✨Najmah✨25 ( Daurin Aure)

90 8 0
                                    

Najmah
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Daurin Aure
💃💃💃💃

**************

Misalin karfe 12:40
Jama'a yan daurin aure, Yan uwa da abokan arziki sun cika makil a masallacin Almannar dake Unguwan rimi cikin garin kaduna
Don Anan xa'a daura auren
Xasu gabatar da sallan azahar sannan a daura aure

Adaidai wannan lokacin Minal,Najmah dakuma Amarya na zaune a wani daki Wanda bangaren dakin ya fita daga cikin gidan Yana bayan garden din gidan.

Mai hoto ne yake ta Mata hoto tun safe da suka shirya ta cikin wani purple color din gown da karfe Sha biyu Kuma ta cire ta Sanya lifaya red color
Itakam tarasa wani irin farin ciki xatayi.....babu abinda takeyi sai godiya ma ubangiji day nuna mata wannan rana....ilham kenan

Mahaifiyarta ta dafa ta
Ya'ta

Juyowa tayi mezai faru zazzafan hawayen da take boyewa sune suka fara diga ahankali

Ammie Tai saurin goge Mata tare dace wa
Kul Ilham karki soma
Naxo ne ki fadin min in kina da wata matsala da wannan auran saura minti Ashirin kacal a daura auran ku........Ina nufin idan da akwai wata mgn da kike son fadamin amatsayina na mahaifiyar ki toh ki Fadi min ilham...idan Kuma babu to Ni Ina da mgn

Ilham ta kalli idanun mahaifiyarta....tace Ammie nagode sosai da tarbiyar da kika bani amatsayinki ta mahaifiyata
Ammie kin dau cikina na tsahon wata Tara sannan kikayi raino na Wanda har izuwa yau Ammie da aure xai rabamu , kina cikin rainona ne....Ammie ki yafe min Dukkan laifukan da nai maki da Wanda na sani da Kuma Wanda ban sani ba.....

Ammie Ina so ki cigaba da min addu'a kaman yadda kike min har na kawo matsayin aure yanxu........Ammie bani son rabuwa daku Ina matukar sonku Ammie......zuwa wannan lokacin kuka ne ya kwace wa idanuwanta sosai takeyin shi

Wanda itama Ammie tuni ta fara kuka....toh fah su Naj da Minal tuni Suma suka fara kukan tare da rungume Ammie wacce itama ta rungume yarta.......suna ta kuka wi wi wi wi wi wiiiiiiiii
Babu Mai lallashin wani acikin su.

****

Hajiya Wanda aka ba mawa order papper Chicken sun iso, masu abinci ma sun iso sannan masu decorations da DJ Duk sun iso dama karfe Shabiyu akayi dasu duka

Ohk tooh Ina ta neman Ammie nee na rasa inda ta shiga....Bari ki gani tunda Ina da key din store din muje a saka komai a ciki........
Suka je suka aje komai yanda ya kamata.....
Yauwa Rabi yanxu kice da masu decorations din su fara aikinsu da DJ din duka masu raban abinci Kuma kikai su babban kitchen su jira acen xuwa karfe biyu idan Yan daurin aure sun dawo.....Ni Kuma xanje in nemo Ammie
Toh Hajiya

.........

Wai nikam Minal ko................Kasa karasa maganar tayi ta tokare a bakin kofa ganin daga yayan har ita uwar kuka suke yi

Salati ta kamayi tana tafa hannuwa.......Nan Ammie Tai saurin juyawa tana share hawayenta

Haba Ammieyn yara keda xaki na tausansu....sai Kuma ya kasance ke ce kike Taya su kukan
Toh sai ki xo muje Koh.

Simi Simi Ammie ta biyo bayan Mamie........Mamie ta jata har dakin sama suka kulle inda ba mutane

Haba Ammie Zaki sa yarinya ta karaya da auran da xatayi......Nasani akwai xafin rabuwa duba da yanda shakuwa tsakanin uwa da diya ......Amma
Don Allah ki tausasa zuciyarki kinji
Kinsani aure zatayi fa bawai rabuwarku tazo karshe bane.

Tohh Mamie na Bari inshallah

Muje ga masu aikin nan Koh...

***********

Karfe Daya da Rabi (1:30) aka daura auran Ilham da Ahmad
Da Kuma
Sadeeq da Yusrah
Kowa Yana murna aka dawo gida

Hakika tsayawa in rubuta zallan farin cikin da Sadeeq yake ciki to na Bata Alkalami na ne
A baiyane xaka hango farin cikin da yake ciki sai gaisawa yake da mutane
Shida Shariff Kam baxaka iya tantan murnan su ba.

Daga masallacin wajan reception aka wuce na maza anan aka ci aka Sha sanna kowa ya Kama gaban sa

Xuwa karfe uku na rana Angwaye biyu suka iso kofar gidan Alh.Salis......
Baka Jin komai alayin sai zallan kida dayake tashi.....

Sannan suka kutsa Kai zuwa cikin gidan.

MC kuwa Fadi yake ga Anguna Nan biyu xasu shigo asuburbuda masu sauti

Kasancewarshi filin gidan Babba nee decorations din da Akayi na yinin biki xaka dauka wani gagarumin event nee aka shirya tabbas wajan ya tsaru....Amarya ce sanye cikin White Gown an lullube ta da net tayi kyau kaman wata balarabiya

Kawayenta ne agefenta Suma sunyi kyau kaman sune Amaren barin Minal wacce take sanye cikin wani Gown golden color shigen ta Ilham banbancinsu kadan ne.

Hangota kawai yayi yaji wani sanyi a zuciyarshi,yaji rahama na Dade shiga cikin jikinshi
Yaji tunda yake Bai taba yin farin ciki ba irin na yau

*******
Mamie da Ammie sai Kai da kawo ake yi MashaAllah uwayen Amarya sunyi kyau matukar gaske

Mamie na tsaye a wani corridor tana jiran Ammie ta fito
Don Daddyn Ilham ne ya Kira ta yanxunnan
Karan wayar Mamie ne ya katse mata tunani
Mijin ta ne ya Kira
Murmushi tayi sannan ta daga adaidai lokacin da Ammie ta fito dauke da kyakkyawan murmushi a fuskan ta
Da saurin ta ta nufo Mamie sai ta iske ta tana waya don Haka ta jira ta gama

Na'am Alh. Nace Goro yafi so a kirga
Nikam kawai ka fadimin ko nayi fushi Allah☹️

Bude Baki tayi da mamaki hade da zare idanu
Don Allah Abba da gaske kake wannan mgn

Alhamdulillah Allah na gode maka 🙏 ALLAH ABIN GODIYA

Sannan ta kashe wayar rungume juna sukayi da Ammie suna murna

Alhamdulillah Mamie Burinmu ya cika...

************

DielaIbrahim ✍️
Vote And Share
Pls 🙏







BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now