✨Najmah✨ 34

73 8 0
                                    

Najmah
Story written by
DielaIbrahim ✍️

(34)

*****************

Shekarun baya
Xan iya cewa 22 years back
Khadeeja was mi junior
Shakuwan mu ta fara nee sbd we re room mate

Na fita sanin gari sbd na zauna a kasar Nijar sosai
Am staying with my uncle daga baya Kuma na Kama off campus

Mun shaku da khadeeja matuka har takai ga Duk inda zani ita ke raka Ni...ita Bata zuwa ko'ina

Wata Rana mun fita bikin wata kawata sai ga Major A.A wato (Abdullah Abdullah)
Yaro Mai tashe don ni ban taba ganin kyakkyawan saurayi Wanda ya amsa sunan kyau ba sai shi
Mata dayawa suna rushing dinshi Amma shi babu ruwanshi da mace , mace ma Bata gabanshi
Nasanshi tunda dadewa
Major AA haifanfan Saudi nee cikin Riyadh....a iya Binciken mu shikadai nee  iyayen shi suka haifa......iyayen shi suka turashi kasar Russian don zama soja Kuma ya cika masu Alkawari

Awannan lokacin da suka hadu da khadeeja aiki nee ya qawo shi Nijar republic tsahon shekara biyu suna wannan aikin

Kwatsam yaga khadeeja
Daga Nan ya fada tarkon sonta

Tsahon shekara daya ya Kuma dauka yanafama da khadeeja ta amince da soyayyar shi Amma ta ki bashi Hadin Kai
Har takai ga ya kusan rasa rayuwarshi Yana gadon asibiti
Khadeeja ta amince dashi
Kuma atake aka daura masu aure batare da sanin iyayen su ba
Da sanina Kuma agabana akai komai Nina dinga tursasawa khadeeja harta yadda ta aure shi

Major AA Yana matukar son khadeeja shiyasa yake ta avoiding wasu transfer din da ake masa da Kuma wasu yakin da ake turasu.... Unfortunately kasar su ta cen Russian ta neme su da su zo wani babban aiki

Tunda ya tafi kimanin watanni uku babu shi babu labarinshi
Sai kawai muka ga sako
Daga wani soja
Cewa Allah yayi wa Major Rasuwa

Daga lokacin khadeeja ta Shiga wani mayuyacin Hali Mai ban tausayi don sai da ta farfado daga ciwon da tayi nee
Tace xata gida kawai baby anfanin xaman ta Nijar
Tunda dama ta gama sch

Tundaga lokacin ban sake Jin duriyar khadeeja ba
Sai yau Dana ganku

Ta Dan share hawayenta kadan
Tace shin khadeeja na Raye nee

Shariff nee ya samu kwarin gwiwar Bata ansa
Allah ya Mata Rasuwa ranar data haifi cikin da ta tafi dashi

Allah sarki khadeeja Allah ya jikanki.......

Sadeeq yace yanxu babu yanda xa'ayi musamu family din Major

Dasaurinta ta kalle su
Sannan tace ai ban gama Baku lbrn ba

Ohk sorry muna jinki

Bayan shekara da tafiyan khadeeja unfortunately wata Rana naji ana min sallama tare da jiniyan force

Ina fita naga
Major
Abin ya daure min Kai matuka
Bayan mun zauna dashi nee ya ke bani labr abinda ya faru dashi
Wanna asatinnan ma ya dawo shiyasa yaxo Nijar aranar don ganin khadeeja
Amma poor major tunda na bashi lbr tafiyan khadeeja ya Shiga mayuyacin Hali
Mai wuyan fassarawa

Yayi nema sosai har ya gaji
Tace a KD take har kaduna yaje Amma Bai same ta ba

Minal Tai saurin cewa Yana Raye har yanxu nee

Kwarai kuwa Yana Raye ayanxu Kam ai ba Major bane field Marshal nee Wanda bakaramin mukami aka daura Shiba
Kafin kusamu damar ganin shi zaku Sha wahala kam

Nataba ganin shi sai dai zai yi wuya in gane shi ayanxu Kam

Duk suka juya ga kallon su ga Fayrouz da yayi mgn

Kwarai kuwa i saw him once nd cikin taron da akayi akasar Saudiya na Karin girma was sojoji kasar ya hallaci taron
Abin ya wakana nane kaman Haka

Ina tsaye da abokanai na alokacin muna sch
Ta Bayan mu Motocin su suka tsaya
Sannan suka bi ta gaban mu mutane dayawa suna ta gaisawa dashi sai na tambaya shin wanene wannan da mutane suke so haka?
Wani daga cikin aboki na nee yace min Major A.A kenan
Mutane suna sonshi sbd kyakkyawan halayenshi da Kuma jajircewa akan kishin kasar sa
Tabbas A.A Yana da masoya  can iya cewa a duniya gaba da baya sbd ya taba ansan mukamin sojan kasa da kasa

Lallai ban samu na ga fuskan shi ba Amma ayanda naji lbr baida Yaya saidai ya taba aure Kuma matar sa ta rasu
Wanda awannan lokacin ma da Naga ganshi bashida Mata sai dai ban sani ba ko yanxu

Hawaye suka sauka a idanuwan Najmah.....tace ya Fayrouz muje Saudiya ko zamu same shi yanxu

Ba lallai bane Naj sbd kasashe da dama yake ma aiki ahalin yanxu sai dai muyi ta yawo Amma sabani xamu samo dashi
Kasancewarshi babban soja babu Wanda yasan movement dinshi
Kinsan irin rayuwan force ba kasafai suka fiye fadin inda xasu ba.....so I want you to keep calm
A hankali zamu bi komai
Da yardar Allah xamu same shi.

Matar ta katse su day cewa
Kardai kuce min diyar Major ce wannan don tabbas
Shiyasa nace tamin Kama da mutane biyu tun farkon

Wato Khadeeja da Kuma Major

Zo yata

Naj ta taso ta Zo wajan matar
Matar ta rungumeta tsam ajikin ta.... Tace Ashe akwai ranar da zanga jinin khadeeja MashaAllah
Yarinya daga gani halin mahaifiyar ki kika dauko
Allah ya baki sa'an ganin mahaifin ki

Ameen Duk suka ansa
Xan Taya ku nema inshallah da zaran na samu information can Kira ku

To Mommy mun gode mu xamu koma

To saduwan Alkhairi

Sukai Mata sallama suka Kama hanyar masaukin su

Kowannansu da tunani acikin ransu na (3rd) third plan

*******************

DielaIbrahim ✍️
Vote and Share
Pls 🙏

BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now