✨Najmah✨20

83 8 0
                                    

✨✨✨✨✨

Daki ta tashi ta nufa cike da tunani kala kala
Wata zuciyar tace mata keda baki son shi me xai dame ki dashi
Nan take tai watsi da xancen Sadeeq ta koma Danna wayarta
Tana zaune har ilham ta shigo
Mrs Sadeeq lafia ki ka shigo kika barni nikadai a falo

Uhmmmm babu komai ilham
Azumin yau ne ya gajiyar Dani
Meyasa baxaki Dena kirana da sunan Nan ba?

Ohhhhhh i see ilham ta fada tana mata kallon wannan ta raina min wayooo😏 are sunan a rubuce yake
Kallon ta Minal tayi ayayin da take mgn daga bisani ta dauke kanta.

Bangaren sadeeq kuwa Yana fita gidan su Fayrouz ya nufa
Bashi ya koma gda ba sae karfe Sha daya
Kai tsaye part dinsa ya nufa
Don bacci ne a idonsa sosai.

,...............

Yau saura kwana  biyar sallah kamar yadda kwanan Minal biyar a gidan.....
Kullin tana kunshe a daka.....bakijin doriyar ta sai idan Ammie ce ta kirata......Ilham Kuma takan tafi asibiti sai bayan azahar take dawowa
Minal ta Saba xama Shuru abinta

Shirye shiryen sallah gaba daya family din sukeyi ka'in da na'in
Wanda Duk sun gama anso kayan sallan su wajan telor
Babu abinda Yan matan Basu siya ba...kawai sallan suke jira
Granny ta iso gidan su ilham wannan karan tace ita yakamata taxo, ga Naj gaba daya wannan lokacin sunyima Mamie kaura anbarta da yara

Ana sallah saura kwana biyu.....Ilham na zaune suna hira da Minal da Naj
Taga Faruk yashigo ya nufota da leda ya mika mata
Ya ilham gashi ya Shariff ne yace na kawo maki

Minal ce tai saurin anshe wa hade da bude wa sabuwar wayace acikin kwalinta iPhone 11pmax....wow🤭 suka fada dukkansu suna kokarin bude wayar
Ita Kam ilham abin ya Bata mamaki tace kada ku bude pls mayar mashi xanyi wannan wayar ai tafi karfi na wlhy

Gaskia Kam na goyi bayanki Cewan Naj.....Minal ta tabe baki nikam Banga abin mayarwa ba anan
Ina shi yayi sanadiyar fashewar wayarki Kuma yanxu ya siya maki sabuwa to bashi kenan ba

Baki gane nufi na ba Minal....akan me xai siya min waya Mai tsada haka ba wani abu ke tsakanin mu ba Kuma inma Yana son siya minne ai sai ya siya irin wacce ta fashe koh

Ni atunanina ya dauke ki kamar kanwarsa ce ai shiyasa ya siya maki cewan Naj...amma Duk da Haka wayar babbace Kuma ayanxu ma wayar sai ya'yan wane da want suke rike ta..

Yauwa Yar gari abinda nake nufi kenan cewan ilham

Ansan wayar tayi ta maida cikin kwalinta sannan tasa cikin leda ta fita......Minal tayi murmushi tace da Naj mayar Masa fa xatayi

Ehhhh ae tana da right din hakan....Kuma yin hakan shi xai sa mutuncinta baxai xube ba

Ilham na fita tayi dakin ya Sadeeq da sallama ta shiga
Jim kadan aka amsa Mata ta shiga
Tayi sa'an ganinshi a dakin....sai dai su uku  zaune suke suna Hira

Tunda ya daga Kai ya kalle ta...ya sauke har ta karaso ta gaishe su Bai Kara kallonta ba

Ya Shariff Ina kwana
Bata jira amsawarshi ba ta cigaba da mgn
Yanxu Faruk ya kawo min waya yace inji ka.....
Kayi hakuri ya Shariff ga wayar na dawo da ita bawai na Rai na wayar bane...illa wayar tafi karfi na wlhy am so sorry bai kamata in rike babban waya irin wannan ba..
Ta ajiye sannan ta juya ta wuce abinta

BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now