✨Najmah✨ 17

75 8 0
                                    


✨✨✨✨✨✨

Suna Isa KD Marafa estate suka nufa
Suka fara sauke su Ilham
Amma sai da suka jira doctor ya xo ya duba Sadiq
Kafin suka wuce

Shariff ma aka sauke shi a gida sannan Suma suka nufi gda

Mamie tayi murnan dawowansu
Amma yanayin fuskokinsu tasan
Ba lafia
Don Haka Bata tsananta bincike ba tasan xasu fadi Mata
Tai hakuri har lokacin shanruwa yayi

................

Zancen banxa ne wannan shi Alh.Salis din ya ce maki Sadiq baya son Yusrah

Aa Abban Yusrah.....munyi mgn ne da Ammie

Ni agani na karmu takura yarannan ayi abinnan azo Kuma daga baya ana Dana sani

Tohh Amma kinsan da cewa Yusrah na matukar sonsa koh

Duk da Haka Abban Yusrah xan
Shawo kanta ta hakura

Wannan ba mgn daga jijiyoyin wuya bane

Shikenan tunda kince Haka....

Mom ta samu Yusrah a daki....tace Mata
Yusrah Ina so ki hakura da maganan Sadiq...Munyi mgn da Ammie tace kaman da akwai wacce yake so

Ta fada maki ko wacece ita mom?

Aa Bata fada min ba don a iya saninta ma batasan a Ina yarinyar take ba

To shikenan mom na hakura

Datz my girl ta rungumeta...sannan ta bar dakin

Hmmmmmmm wlhy Ina nan xuwa gare ki....ko ke wacece
Xakiyi regretting shiga gonata

Yusrah ta fada tana daure fuska
Tare da kulla wani mummunan
Kudiri acikin ranta

..........................

Naj nee ta gama ba mamie lbr abinda ya faru

Mamie ta tausaya ma sadiq kwarai...Kuma taji dadin hadin
Amma bazata iya tilasta ma Minal dole sai ta so shi ba

Ahankali xata fada tarkonshi tasani...don ita Minal tana so kawai mutum ya bita yanda take so ne.

Shikenan Naj xanyi mgn da Sadiq Kira min yayanku
To Mamie

Mamie tayi wa Sadiq bayanan Duk yanda xai shawo kan Minal
awaya sukai mgn
Kuma ta bashi goyon baya akan ya cigaba da sonta inshaAllah
Bashi da Mata sai Minal

Sadiq ya ji dadin hakan sosai tare da godiya wa Mamie

Acikin Yan kwanakinnan da suka dawo ya fara samun sauki sosai
Alokacin anyi Rabin axumi ....ana ta shirye Shirye sallah

Yau Monday kwanan su biyar da dawowa ya  shirya don xuwa wajan aiki

Ammie ce ta shigo don ita batasan meke faruwa ba tace
Sadiq meke damunkane
Kaki ka Fadi min

Ammie ba wata matsala kawai fever ne ya Dan Kama Ni
Kuma alhamdulillah ya sake Ni

Toh Allah ya kara sauki
Ameen ya fada

Ammie na tafi wajan aiki
Toh Allah ya tsare

Ameen Ammie
Ammie na matukar son danta Sadiq
...............

Yana Isa wajan aiki direct office dinsa ya wuce...ya xauna
Da zafi zafi ya fara aiki daya chakude mashi na tsahon sati daya da Bai xoba

Bashi ya gama ba sai karfe 12 dai dai .....

Ya tashi don komawa gida ma'ana ya gama da na yau kenan
Duk da lokacin tashin shi baiyi ba..yadau excuse

Ahan yarsa ta komawa gida...yayi branched a wajan Mai fruit don siya ma Ammie

Yana Nan tsaye ne.......yaga gittawan ta tacen tsallaken titi da sauri yai saurin Kara kallon ta tabbas wannan Yusrah ce

Toh me takeyi anan daga Kai yayi yaga daga Ina ta fito Hotel ne

Kuma ita da wani mutumi sai dai shi ya rigada ya shiga motan
Bai ganshi ba.

Bai bi ta kanta ba.....Binciken mutumin yafarayi.......ta hanyar daukan lambar motanshi

Sannan ya shiga mota ya nufi gida.

A bakin kofan dakin Ammie kawai yaci karo da ita....tana niyar fita

Tsayawa yayi cak Yana kallonta
Kasa kasa tayi dakai kaman wacce Tai mashi laifi

Da kyar ta iya kakalo murmushi hade da fadan kalma uku

Ina yini Yaya

Kauda kanshi yayi daga kallon nata Yana kutsa Kai cikin dakin
Tare da cewa
Ah lafia lau

Ya wuce abinshi kaman Bai damu ba

Mamaki ne ya kamata
Toh dama ba so na yake yi ba
Ji ko kallo na baiyyi ba
Ta tafi tana kun kuni a cikin ranta

Murmushi Sadiq yayi don Yana jinta...sannan ya girgiza Kai ya wuce ciki .

Shiga dakin ilham tayi tana turo baki....ke Kuma me ya sameki ne kike turo baki, Naj ke tambayan ta

Babu komai ta Bata ansa

Uhmmmmm..... Kyaji dashi karki fada din.

Basu wani dade ba suka koma gda...don magriba na gaba towa

............
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

DielaIbrahim
Vote nd Share
Pls 🙏

BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now