✨Najmah✨11 What is meant to be_ will surely be👇

130 10 0
                                        


Gaba dayansu gida suka wuce
Kowa da irin tunanin da yake a xuciyarshi
.................................

Naj gift dinki yafi nawa yawa so xamu had a duka sai muyi raba daidai

Allah ya sauwake min...sai dai na baki duka

Aa Ni wlhy bana son duka sunmin yawa..

Toh sai ki hakura da nawa gift din

Lallai ma naki yafi nawa yawa

Ohhhh too shikenan baki shirya Kar ba ba ......ta juya Mata baya ta kwanta abinta tare da cewa
Gudnyt nd Don't 4get
Gobe xa'a tashi da azumin
Ramadan

Pillow Minal ta dauka ta jefa mata......sannan ita ma ta juya baya ....tana fadin ai kowa ma da ranar sa ehee

Naj ta make a bargo tana dariya kasa kasa

..............................

Yau Asabar kuma ayau Al'umman garin kd suka tashi da azumin Ramadan
Gashi ruwa ake ta zubawa agarin kamar da bakin kwarya

Misalin karfe Takwas da Rabi na safe ........Mamie ce a kitchen tana ta aikin ta ita da mairo Mai Taya ta aiki.

Abba ya shigo yace Mamie xo

Toh Abba lafia?
Lafia muje Mana

Parlor suka nufa suka xauna

Tsahon dakika Biyar kafin Abba ya fara mgn

Ina ganin lokaci yayi da yarannan xasu fito da maxajen aure koya kika gani....don Naj ta jima da gama sch...Minal Kuma this year xata gama

Ga Fayrouz Shima akalla Yana shekara 35 kenan...

Gaskia Abba mgn abin dubawa ne
Na dade Ina sonyin mgn
Amma wani xubin sai in kyale su
Sbd a tunani na idan sun dai daita da mane mansu xasu
turo su....Amma Shuru kake ji
Kaman ba auren agaban su

Toh shawaran Dana yanke ki fara masu mgn
Inyaso Ni idan bamuji feedback ba sai nai masu da Kai na

Toh Abba ba matsala Allah ya shige mana gaba

Ameen
Bari naje na karasa kammala aikin

Yau ba breakfast kaji yaranka Shuru dayake Fahad yakai su Suhaila makaranta Bai ma dawo ba...sukuma manyan suna ta sharara bacci abinsu
Kasan haka sukeyi Duk axumin Ramadan indai suna gda......

Hahhhhh ai wannan Yan biyun naki Mamie sai ke....ke kadai kika iya dasu
Ta wuce tana dariya .....

........................

Najmah ce ta fito daga wanka tana tsane gashin kanta
mai santsi,cika da kuma tsayi
Abinda ya banbanta gaahinsu da Minal kenan

Ita Minal gashin ta santsi da tsayi Amma ba cika.

Zaune take agaban dressing mirror tana shafa mai........sauri takeyi tagama
Sbd ana jiranta a shago....gashi ta dade Bata je shagon ba

Minal ....Najmah ta Kira sunanta....

Cikin bacci tace uhmmmm

BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now