✨✨✨✨
Bata ansa mashi ba....ta rufe idanuwanta hade da toshe kunnuwanta....tsahon dakika Biyar..
Sannan ta bude su ahankali
Kayi hakuri ya Sadiq baxan iya auran ka ba ,we re not meant for each other....tana gama fadin haka tabar wajan da gudu
Yana Nan tsugunne awajan Fayrouz ya dafa shi yace tashi ka bita
Da yardar Allah xakaci nasara Bros.
Rungume juna sukayi sannan ya bita Bai ganta a compound din wajan ba don Haka
Motar shi ya dauka ya nufi titi..
Cen nesa dashi ya hangota tana tafiya ga wajan Shuru babu kowa....
Birki yaci a gabanta
Sannan ya fito
Hannun ta ya Kama ya bude mota da niyar shigar da ita
Ina xaka kaini yaya
Bai kula taba yace Mata shiga mota
Ba musu ta shiga
Ba Wanda yace ma Dan uwansa kala har suka Isa gda
Su ilham Sun rigasu dawowa
Don Haka ta iske su duka a parlor harda ya Fayrouz da Shariff
Wuce su tayi kawai ta nufi daki
Granny tace yarona me ya samu Namshi ne
Ba komai granny guys kaina na min ciwo xan shiga na kwanta
Ohk muma xamu shigo yanxunnan
Ohk ya wuce daki abinshi
Tana zaune a daki ta fara tunanin maganganun da sukayi da ya Sadiq jiya
Ashe sonta yake all dis while
Ita gaskia baxata iya auranshi ba
Me yasa kin manta kin dade kina Addu'an Allah ya baki miji irin Yaya Sadiq
To Allah ya amsa addu'ar ki
Sai dai idan xaki butulce mashi
Wata xuckyar ta Bata ansa..
Haka Tai ta tunani har Yan uwanta suka shigo
Tayi kaman tana bacci
Har suka kwanta suna ta hira har bacci ya dauke su.
Itakam ta kasa bacci kamar yadda Shima ya kasa bacci..
Agogon ta duba taga karfe biyu daidai ta tashi ta yi alwala ta fara nafila.
Bata tsaya da sallan da takeyi ba har sai da taji an fara sahoor sannan tashi ta nemi abinci after ta gama ne taji Kiran sallan farko na raka'atanul fijir
Tayi sannan ta fara karatun alkur'ani har aka Kira sallan asubah
Tana idarwa ta cigaba da karuntun ta .....sai karfe bakwai kafin ta smu bacci anan ta kwanta
Najmah da tun cikin dare take lura da Yar uwartata ta tausaya Mata sosai.....
..............
Tun cikin dare ya tashi yau yaji jikinshi baya mashi dadi daure wa kawai yake yi har safiya tayi...
Ahaka ya rarrafa yayi sallan asuba tare da Tai makon Fayrouz da Shariff...
Ranar haka ya yini ba lafia tsohuwa kam taka sa xama hankali Duk ya tashi
Gashi d next day xasuyi tafiya xuwa u.s
YOU ARE READING
BETWEEN US ✔
Документальная прозаStory of three sisters that made alot of painful sacrifices to each other Najmah who happens to be the star of the story, Minal ( Najmah's partner) And Ilham the honest friend
