Najmah
(45)
_____________(Garkuwa Hospital)__
Likitan ya daura Bayan ilham tayi shuru
Congratulations Mr.Fayrouz Muhammad you're going to be a father
Gwaje gwajen mu ya nuna mana tana dauke da 4weeks pregnant
Don saura kwana biyu kacal ya cika 4weeks din........
Fayrouz ya rasa me xaiyi suman zaune kawai yayi Yana murmushi harsai da ilham ta Dan taba shi kafin ya dawo hayyacinsa......................tashi yayi
Ya durkusa yayi sujudur shukur
Ya godewa Allah da kyautan da yayi Masa........ya tashi ya zauna
Ya Mika ma Dr hannu suka sake gaisawa ilham babu abinda take sai dariya..............saboda farin ciki Yama rasa me xaiyi awajan.......
Likitan ya cigaba da cewa sai dai Kuma akwai wata matsala kadan
Matar ka mahaifanta baya da karfi sosai don Haka idan ana so cikin ya xauna sai dai ta Dena Duk wani aiki na wahala
Ta samu bed rest sosai saboda babyn dake cikinta yayi kwari tukunna...................akwai medicines da xamu Bata Wanda xai taimake ta sosaai yanxu cikin karami nee so she have to be very careful and always take good care of her kada kusha want magani sai wanda doctor yayi maku prescription akai pls take note............
Fayrouz yace inshallah Dr zamu kiyaye Zan iya ganinta yanxu
Eh ba matsala you can
Dr. Ilham will show you the way
Ilham ta raka shi izuwa dakin da aka kwantar da Naj
Kwance ya sameta ta farka
Tuni ya rungumeta sannan ya sumbaceta a kumatunta da goshi
da Ido daga bisani ya Kara rungumarta kamar za'a kwace mashi ita.......lol
Itakam ta rasa meya faru
Ta kalli ilham ta daga Mata gira
Ilham ta ware Mata hannu Alamar babu komai 🤷
Sannan ta juya ta barsu don da alama Fayrouz ya manta tana wajan..........
Tace Yaya na what's happening
Me likita yace Yana damuna
Yanxu akaxo aka tsira min Allura
Wlhy ban yafe ba.....Ni da lafiyata kalau duka duka ba daxu bane na fara rashin lafiyar
Sakin Baki yayi Yana kallon ta Wanda ita fah Wai da gaske take Bata yafe ba..........dariya Kuma ta subuce mashi sai da yayi Mai isarshi kafin ya Kama hannunta yace look Mrs Fayrouz yanxu hakuri zakiyi da duk wani abinda za'ai maki a hospital saboda lalurar da kike dauke dashi...... ..
Lalura wata irin lalura Kuma Yaya? Ta tambaya
Ya kalle ta Yana smiling yace
You re pregnant little
Kina dauke da cikina
Mun kusa xama iyaye muma in future time..... ..
Mamaki yasa ta sandare ta zuba mashi idanuwa kawai tana kallon shi
Yadan tsakure ta kadan ta dawo hayyacinsa
Yace Mrs Fayrouz are you there? Yana yi Yana Mata waving da hannu.........
Wani kalan murmushi nee ya xo Mata harda guntun hawaye ta rungume Fayrouz tana cewa
You mean am....am ......an pre.....maganan ta kakare Mata saboda murna
Yace yes you are mi wife
Allah ya bar Miki
Kuma Allah yasa ki haihu lafiya
Ameen summa Ammen ta fada
Nan dai sukaita murna
Washegari su Mamie harda su Ammie suka xo dubata
Kowa saida yaxo Yana Taya su murna ita ko Naj kunya ce ta kamata har da yima Fayrouz fada Wai meyasa duk ya fada masu yanxu xa'a ace ai dama abinda sukeyi kenan.............
Fayrouz idan ya tuna maganan babu abinda yake Banda dariya
Kwanan su uku akayi discharging dinsu daga hospital din.............
...................
Toh Bari mu tabo su Minal
Muji
Minal suna zaune da Yusrah lafiya wata rana abokin Sadeeq yaxo gidan yaganta Kuma ta kwanta mashi arai
Yayi wa Sadeeq magana
Bai Musa ba Amma yace
Me zai Hana kayi campaign dinka dakanka kaman hakan zai sa darajarka ya karu a idanuwanta akan ace na tursasa ta.......abokin ya yarda da shawaran donhaka yasamu Yusrah yai Mata bayanin komai
Bata ki ba sai ta bashi lokaci
Saboda taga he is a responsible man Shima
Xuwa Dan wani lukaci suka fara soyayyah Bayan watanni Kuma manya suka Shiga magana sai alokacin akasan Sadeeq ya saki Yusrah
An daura Mata aure Kuma ta tare a garin da mijin yake wato Katsina state
Asalinshi Dan kt nee Kuma acen yake aiki......... MashaAllah Yusrah Bata taba tunanin familyn mijin ta suna da arziki da Kuma yawa ba saida ta Shiga cikinsu......Kuma mutanen kwarai
Ga mutunci sannan suna ta haba Hana da ita Barin ma kishiyoyin sirikarta suna nuna Mata kulawa sosai.........lallai Yusrah tayi darasi a rayuwa
Allah ya so ta da rahama
Yanxu tana mutunta mutane tana masu fara'a.......ga Kuma kyautatawa
Nikam nace toh Yusrah Allah ya baku zaman lafiya keda mijin ki.....da Kuma zuri'a dayyaba
.................
Bari mu gangaro Kan Ilham
Ilham itama ba'a barta abaya ba
Bayan Naj sun koma gida da sati daya nee ilham ta fara suspecting tana dauke da ciki
Toh kunsan abunka da doctors
Ta jira for 5 days bataga period dinta ba
Tuni ta nufi lab dinsu don a dauki sample dinta
Da ikon Allah kuwa result ya fito positive......babu irin murnan da Shariff basuyi ba Shida su Mama
Da zainab kanwarsa
Tuni aka fara shirye shiryen kayan baby...........uhmm nikam nace masu kaji wa inda basa was da kudi kenan don kayan babyn ma daga Germany Shariff yake siyowa idan yaje Riyadh ma Haka zaita kwaso su har su Naj da Minal siya musu yakeyi
Gadajen Yara da kekuna
Da abin Goya yaro
Fan na Yara kujera na Yara ,kayan wasa baby abin da ya Bari komai yaga ya mashi kyau siya yakeyi.............wannan kenan
.................
Ikleemah kanwar Mamie tun ranar da tabar gidan Mamie
Tayi hatsari kafarta guda Daya ya karye Bayan anyi dauri aka gano cewa karaya uku ce biyu a waje Daya.....Daya Kuma daban
Anyi dauri Amma abin ya kasa
Daga baya aka yanke kafar
Tayi kuka sosai
Tundaga lokacin ta koma wata saliha.......idan ba tambayanta Abu akayi ba to baxaka taba Jin maganarta ba............
Awannan lokacin nee ta samu sauki Kuma taxo wajan mamie neman gafara
Da kyar masu gadi suka barta
Amma said suka shanyata awake kusan awa biyu kafin suka shigar da ita
Mamie tayi matukar mamaki ganin ikleemah ba kafa Daya
Sai da suka zauna tabawa Mamie labari Duk yadda abin ya kasance
Dan uwa kenan Mamie ta tausaya Mata matuka Wanda ji tayi kaman Tai Mata kuka
Tai Mata nasiha Mai ratsa jiki
Sannan Tai Mata kyautan kudi masu yawa
Tamusu sallama ta tafi
Wannan kenan
...................
DielaIbrahim ✍️
Vote pls 🙏
.
YOU ARE READING
BETWEEN US ✔
Non-FictionStory of three sisters that made alot of painful sacrifices to each other Najmah who happens to be the star of the story, Minal ( Najmah's partner) And Ilham the honest friend
