NAJMAH
MALLAKIN DIELAIBRAHIM ✍️___________________________________
DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Da shigar su babban super market din wanda ya kunshi bangarori daban daban, da àlama tasan kan super market din don haka kai tsaye hanyan daxai kaita layin cosmetics💄ta nufa, ba tare da bata lokaci ba ta fara zaban duk abinda take bukata, tana gamawa ta fara jan trolly din har inda yan uwanta suke.
Dariya Minal takeyi ciki ciki tare dacewa wai ke Najmah duk sanda za'a zo super market baki da abin zaba sai cosmetics💄😏?
Sakon harara kawai ta aika ma minal batareda ta tanka mata ba.In banda abinki minal ai tafi ki tunda ita abin anfani ta dauka ke kuma fah, baki da aiki sai zaban chocolates,sweet, cookies d.s kodayaushe cinkin shan kayan xaki kike kaman wata baby Mamie ta karasa maganar tana hararar minal tace chop chop kawai"
Zumbura baki tayi kaman mai shirin yin kuka sannan tayi hanyan waje abinta
Murmushi Abba yayi tare da cewa mamie kenan da twins dinta.
Abban yara ai gaskiyace chocolates ai cimar yara ce ta karasa mgn tana niyar fita daga super market din....Fahad wanda babu abinda yake sai dariya ya bi bayan Najmah yana cewa sis Najmah dan Allah zan kawo gf dina kima ta make-up,
Uhmmm... sannan tace kai karami da kai dinnan sai faman rigima wai sai girlfriend to sai ka kawota tana niyar bude mota ne......
Najmah Muhammad....
Taji an kira sunanta atare suka waiga daga ita har fahad , khaleel da suhaila sai da suka juya don ganin mai kiran sis najmah... Ilham Salis ......ta fada tana zare idanu tare da daura hannuwa a kirjinta alamun surprised
Rungume juna sukayi tare da murnan sake ganin juna yaushe a gari ilham?
Wlhy jiya muka dawo najmah......Najmah ya akayi ne meke faruwa ne? Mamie wacce tuni har ta zagayo daga dayan bangaran take tambaya,
aa Mamie ilham ce nagani,Ilham tayi sauri ta rungume Mamie tana murna."
Ahhhhh ilham yauce a gari,ina su Daddy da Ammi?
Suna lafia Mamie suna gida inna koma yau xan fada masu na hadu daku, muma mun dawo Nigerian da xama yanxu ta karashe mgn tana kallan Najmah
Dagaske to Alhamdulullah najmah ki anshi number ta in yaso sai muyi waya koh ki gaida min Ammi sosai.
To Mamie.
Muje ko najmah
Toh... Bye sai munyi waya
Suka kara rungume juna sannan ta shiga motan da duk yan uwanta sun shiga ita kadai ake jira......
So ilham ta dawo minal ke tambayan najmah fuskanta babu yabo babu fallasa.
Yes ta bata amsa batare da ta kalli gefen da minal din take ba.
Shuru ne ya biyo baya a tsakaninsu ba wanda ya kara tanka ma wani..bakajin hayaniyan komai a motan sai nasu khaleel da suhaila."Motar tasu bata ako ina ba sai kofar wani katafaren gida, horn sukayi sannan gateman yazo ya bude musu suka shiga mal.audu gateman ya tsaya yana musu barka da dawowa.
Abba ya nufi parking lodge wanda yake bangare guda na filin gidan sannan dukkan yara suka fito kowa yadau ledan kayanshi yayi hanyan part dinsa.khaleel da Fahad suka nufi part din Abba. Wanda dakin nasu yana bangare daban daga cikin part din Abba, Suna da komai a dakinsu mai yalwan fili, gado biyu ne kowa da gadonsa,wordrope,bedside...sai kujeru guda biyu da tv daga dayan bangaran hanyan toilet sai wani step a wajan toilet din wanda bakomai bane a wajan sai desktop, laptop d.s,dakin yaran mazan gwanin ban sha'awa agyare stab kaman dakin mace.
Mamie, suhaila da twins din mamie part dinsu daya,part ne falo babba mai kunshe da kaya masu stada sannan sai dinning da kitchen babba daga cikin dinning din sai corridor din da xai kaika dakin Mamie wanda still tana da falonta separately da bayi,Suhaila tare da Mamie take kwana komai nata a dakin yake.
Sai dakin twins daga gefe babban daki ne bangare guda set din kujeru labulaye da carpet orenge nd brown...sai wani gefe,gado ne guda biyu da wordrope a akowani gefen gadon sai karamin carpet dogo a tsakiyan gadon nasu... MashaAllah dakindai yayi kyau matuka fiye da tunanin mai karatu.Wash Allah bayana minal ta fada tana kokarin kwantawa akan kujera tabi Najmah dake kokarin cire kayan jikinta da kallo tana shirin yin wanka, tace Agwagwa sarkin wanka....tsahon dakika biyar najmah bata kula taba kafin ta dauke kanta daga kallanta tana tunanin wani abu acikin ranta.....
Kamar daga sama ta sinkayi maganar da Najmah takeyi mata
Yaushe xaki je ki fara registration kinsan dacewa lokaci na kure maki don sun kusa kulle portal koh ?
Kuma Abba ya rigada ya baki kudin dakika tambaya suna wajan Mamie.
Uhmmmm...taja dogon numfashi sannan tace zanje cikin week din daxamu shiga inshallah so kudin suna wajan Mamie
Ohhh shitt😣ta fada tare dayin jifa da pillow.
Hhhh😁 Najmah ta dara..........what's wrong with that idan kudin suna tare da Mamie, kina so ki wasa da kudin ba,?Allah na gode maka🙏Wani pillow din minal ta dauka da niyan jefa mata, Amma tuni tashige toilet hade dayi mata gwalo😛....zan kama kine wlhy fadan minal.
Misalin karfe 10 na safe gabadaya iyalan gidan Alh.Muhammad Adam Misau sun hallarah a dinning din Abba wanda duk kansu anan suke cin abinci always....kasancewar yau weekend kowa yana gida,wannan daman ne iyalan gidan suke samu su tattauna don jin damuwar junansu.
✨Hakika abinci suke ci, idan ka dauke mutun biyar daga cikin su, mutun biyu kawai tsakurar abincin suke,
Abba ya dubi Mamie yace I received a call from Alh. Salis Ibrahim,daxu ya fadamin ya dawo Nigerian shida iyalanshi Kuma xasu shigo anjima Abba ya karashe maganan yana kallon Mamie,Masha Allah amma ka fada masa munga ilham a super market ko?
Abba yace ehh na fadi masa " To Allah ya kaimu anjiman cewar Mamie"
Mamie su wanene zasu zo ne? Khaleel da Suhaila ke tambaya,
Ammi ne da Daddy lokacin dasuka koma America da xama ba'ama haife ku ba don't worry you two zaku gansu anjima ae Mamie ta fada tana musu murmushi.
Actually I can't wait to see Faruk...Fahad ya fada yana washe baki hade da kallon minal wadda tunda aka fara zancan iyalan gidan bata ko dago ta kalli kowa ba, ganin hankalinta baya tare da shi yasa ya tsunguleta a hannu........
A razane ta dago kai tare da sakin kara kadan...sanin Fahad ne yasa ta bishi da harara...sannan tace why do you pinch me?
Sis Minal mgn nakeyi maki but hankalinki baya tare dani...ya bata answer
What do you want me to say?"Fahad ya numfasa yace at least you have to show me that kinji abinda nace......uhmmm
Naki din and don't you dare try to disturb me about such things okay"Ta fada ranta yana mai tsananin baci sannan ta tashi tabar dinning din.Suhaila ta kalli khaleel tace meke damun sis minal?
nima ban sani ba Suhaila....
Ya Fahad sorry kaji sis Minal ta maka ihu maybe bata jin dadi ne na lura da ita tun daxu bata cin abinci kadan kadan take ci....yes khaleel da Suhaila suka fada atare suna karkada kai alamun zancensu gaskia ne.
Mamie da Abba tuni suka bar wajan dan ba kasafai suke shiga shirgin ya'yan nasu ba.
Sosai Fahad ya tsura ma yaran idanu...sannan yace ku wayace maku batada lafia?
Ae a tare suka nuna Najmah alamar ita ta fadi masu.....kallon Najmah Fahad yayi tare da cewa Wai haka sis.........tsahon minti biyu ta dauka kafin ta dago kanta daga danna wayan da takeyi, sai a sannan tace Fahad karka sani cikin wannan maganar bissallam ita ma tayi hanyan fita part dinsu """ fahad ya bita da gudu yace one minute sis wai meyasa sis Minal da anyi mgn su ilham ranta yake baci ne miye dalili? Fahad da yake binta da gudu saboda saurin da takeyi....Fahad me yasa baka ji ne "told you" karkasani cikin maganar...pls leave me alone I don't want to talk right now....infact nima bansan komai ba akai get that. Sannan ta shige daki abinta
Ta barshi nan tsaye yana nazarin reaction din yan uwan nashi....✳️✳️✳️✳️
DielaIbrahim
Comment
Vote
&Lyk........✳️
YOU ARE READING
BETWEEN US ✔
NonfiksiStory of three sisters that made alot of painful sacrifices to each other Najmah who happens to be the star of the story, Minal ( Najmah's partner) And Ilham the honest friend