6

106 6 0
                                    

NAJMAH

ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________

Tsahon awa daya suka dauka kafin suka gama siyan duk abinda suke bukata..
Sun fito daga kasuwar direct wajn mai napep suka wuce....
Naj ta ga mai agwaluma...Minal karasa da kayan bari na sai agwaluma juice dinshi xanyi yau
Inshallah
Ohk toh ko in jiraki ne mu tafi tare" aa kaya sun maki yawa fah tunda bamu da nisa da napep din ki je mana...To kawo sauran ledan, okay to gasu.

Ta gama jera kayan kenan tana Shirin shiga napep taji kaman an Kira sunanta
Waigawa tayi taga ba kowa Amma sak muryan Naj ne wannan

Tai saurin kallon angle din da Naj take ba mai agwaluma kuma ba alamar Najmah
Bata gama dawowa daidai ba ta sakejin an kwala mata kira
Wannan karan ta gabanta ne ,don haka tayi sa'ar ganin masu kiranta....Najmah ta hango acikin wata bakar mota an rufe Mata baki da hanci..
Sae faman daga hannu take tana neman taimako
Amma Ina kafin nai napep ya kunna ya bi bayansu har sun masu nisa sosai.

Minal kuka take yi shabe shabe 😭
Abinda yake kara ta yar mata da hankali shine in ta tuna cewa dauke Najmah akayi, kidnapping fah sai hankalinta ya tashi matuka.

To Amma su waye suka dauke ta
Kuma Ina suka kaita
Sannan ita me xata ce ma iyayensu....
Tana cikin wannan tuna nin ne suka iso gda.
Mal.Audu ne ya taimaka ya shigo da kayayyakin
It's Kuma straight part din Mamie ta nufa tayi sa'an ganin duka iyalan gdan

Sai dae sunyi matukar mamakin ganin Minal na kuka
Lallai ba karamin abubane ya sameta...

Mamie ce ta taso da saurinta...meyasa me ki Minal
Ina Najmah
Shuru ba ansa

Ke Minal baki ji ne Wai ki ma na mgn mana.....cewan Abba

Sis Minal mgn ake maki Ina sis Najmah...Yana tambaya Yana jijjigata...cewan Fahad.

Wasu sabbin hawayen ne suka kara gangarowa a saman kumatun ta Wanda tuni fuskan nata ya kumbura tsabagen kukan da ta ci

Da kyar ta samu ta zayyana masu abinda ya faru
Kowa sallallami yakeyi Amma banda Mamie
Da taji abin kaman almara...Wai an dauke Naj din ta

Abba namijin kokari yayi Yana ta lallashin yaran da suke ta faman kuka

Ranar anan dakin Mamie suka kwana gaba dayansu

Karfe biyu 2 nayi Mamie ta tada kowa
Mamie yadai
Abban yara bacci Bai ganmu ba sallah xamuyi mu nema ma kanmu mafita tare da neman tsarin azzalumai.

Toh Mamie tado yaran,

Duk suka tashi don inda sabo sun Saba da halin Mamie tun suna yara basu manta wa....Duk abinda xasuyi takan hada su duka suyi sallah su roki Allah da izinin ubanhiji saiki ga komai ya wuce...

Toh awannan lokacin sai da su Mamie sukai kwana biyu chur suna rokon Allah....Amma babu Najmah babu labarinta.

Ilham dasu Ammie Duk sun xo
Don ilham ma barinta akayi Nan take kwana itama ana adduo'in da ita.

A rana ta Hudu 4 da bacewar Naj...Minal na bacci a dakin Mamie don Nan suke kwana it's da ilham da Suhaila acewarsu
Kada Suma a dauke su...

BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now