✨Najmah✨ 18

83 8 0
                                    


✨✨✨✨✨

Sadiq ya zurfafa bincike akan mutumin daya gani da Yusrah

Inda yagano mutumin mazaunin Abuja ne....harkokinsa ne kawai ke kawo shi KD
Inda yake lalata yayan mutane

Toh Amma baisan dalilin hadin Yusrah da wannan mutumin ba
Barin komai yai a ranshi
Bai Fadi wa kowa ba.

......,..

Daddy da Abban Yusrah sun so samun sabani Akan Yusrah da Sadiq.....sai dai sbd soyayyar dake tsakanin su..tare da respecting din junansu..Hakika Basu so xumuncin su ya bace

Wannan dalilinne yasa Daddy ya yanke shawaran dole Sadiq ya auri Yusrah inya so daga baya sai ya auri wacce yake so.

Hankalin Sadiq Bai wani tashi ba dajin mgn Mahaifan nashi
Ya nuna masu babu komai su na iya sa rana kawai Amma kada asashi kusa kusa domin gaggawa baida dadi.

Abban Yusrah ya jinjina mgnr sannan yace to ba komai
Ku daidaita inyaso Nan da 3month sai ayi bikin

Budan baking Sadiq sai cewa yayi Nooo lokacin bana Nigerian Ina course a Germany

Kallonshi kawai sukayi cen Daddy yai gyaran murya yace
Shikenan Sadiq xuwa Duk lokacin daka ga ya maka...

Toh  Daddy nagode sannan ya tashi ya ware.

Haka taron na su ya watse.

.................

Misalin karfe 10 na safe Najmah ta tashi da ciwon cikin da ta Saba Duk karshen wata....

Sosai take ta kwarara amai.....Wanda izuwa wannan lokacin Mamie da Ya Fayrouz sun rikice, Mamie suka dauketa sai hospital

Suna Isa aka nufi A&E sosai aka mata treatment wanda tasha injections sosai... immediately bacci Mai nauyi ya dauke ta

Ba ita ta farka ba sai kusan karfe
Hudu.....Ba laifi taji sauki sosai.

Mamie da Minal na zaune kusa da ita ...Mamie tace sannu Naj
Zaki Sha tea ahada maki..ko Irish xaki ci nd egg

Ta girgixa Kai alamar aa...sannan tace Mamie bani Jin cin komai

Aa ai baxaiyu ki xauna da yunwa ba tun safe fah baki ci komai ba... cewar Minal

Haka sukai ta fama da ita Amma taki sauraran su, Mamie Tai lallabin Amma sai wani shagwaba takeyi,, Shuru tana kallon Naj....tasan Naj Bata Mata gardama Amma Bari ta rabu da ita Maybe xuwa anjima xata iya ci.......kallon fuskan Mamie Naj tayi taga ran Mamie bai so ba amma hakan Bai sata ta canja ra'ayinta ba.

Ya Fayrouz ne ya shigo..yana fadin, Yar gidan Mamie ta tashi ne?

Kada Kai tayi....
Yaya jikin toh

Da sauki Yaya

Allah ya kara sauki.....Bari a hada maki abinci ko tea kisha kinsan yunwa Bata da dadi

Da ikon Allah sai ta kasa Hana shi hadawa

Har ya gama hada mata tea mai kauri.... ya nufo ta da cup din kusa da bakin ta ....bakajin kanshin komai a tea din sai kanshin cinnamon da ginge.....Minal ce Tai saurin cewa Yaya tace Bata jin cin komai

BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now