Najmah
(44)
______________________Marafa Estate,11:30am
After 1 month da auransu Naj
...............
Najmah zaune a katafaren falonta tana lissafin kayan shop dinta tana son ta Kara ma'aikata besides Abhi dinta ya ce xai Zo Nan ba da dadewa ba
Za'a gina Mata babban shopping mall,ciki harda bangaren make-up,saloon,da Kaya designers (Arabian perfumes Suma designers...tana ta lissafin yanda xata kawata mall din nata.........
marar ta nee ya fara murda mata
Kaman yadda yakeyi Mata cikin kwanakinnan
Bata iya gane ma kanta
Kuma babu Wanda ta sanar mawa
Kashe laptop din tayi
Ta kishingida a saman 3seater
Bada jimawa ba bacci ya dauke ta............tsahon dakika Ashirin
Wayarta kirar Samsung ta soma ringing
Tuni ta farka daga baccin ta dauka Minal ce ke Kira
Hello ta fada cikin muryan bacci
Sannan ta numfasa da cewa
Minal bacci nakeyi Kika tada Ni
Ya akayine sister?
Minal da tunda ta dau wayar ta kosa ta zayyanawa Naj labarin da take tafe dashi
Cikin zakwadi ta furta
Naj am pregnant
Naj da tuni ta tashi daga kwancen da tayi tana murna bakinta a bude tace
Are you serious sis
Ofcux i amNaj
I'm having 4weeks pregnant in mi womb
Alhamdulillah Naj ta furta Congratulations to you mi sis
Allah ya barmiki Kuma Allah yasa ki haihu lafiya
Ameen summa Ameen
Thank you Naj
I'll hang up the phone now
We'll talk later darling
Naj Tai dariya tana son jin irin farin cikin da Yar uwarta ta take ciki, ta shafa cikinta itama
Tace Allah Nima kabani
Mai Albarka
Ameen taji an fada hade da rungumeta tsam ta Bayan ta
Yana shafa cikin nata Wanda ta daga rigan ya Sanya hannunsa saman nata yace
Xanyi matukar farin ciki idan Kika min wannan surprised din
Naj Tai murmushi tace
Toh addu'a xakayi tayi Allah ya bamu mai Albarka
Ameen ya fada Yana mai zagayowa inda take yace tashi mu shirya muje gidan su Sadeeq
Mu Taya su murna Koh
Daga Nan xamuje gidan Mamie da Ammie
Suna ta korafi Wai su kewarki sukeyi
Naj Tai murmushin karfin Hali saboda wani jiri da taji ya bugi kanta ayayin da take kokarin tashi tsaye......komawa tayi ta zauna tana mutssuke idanuwa
Arazane yayo kanta Yana tambayan me ya faru
Daurewa tayi tace dashi
Dil❤️
Babu komai tashina da Minal tayi shine kaina ke min ciwo saboda ban Dade da kwantawa ba ta Kira Ni
Ajiyan zuciya ya saki ahankali
Hade da danne kirjin shi
Yana Fadin
Alhamdulillah to Bari na kamaki Koh sai na kaiki daki idan kin huta sai kiyi wankan muje
Toh ta bishi dashi ta tashi ya dauke ta cak
Bai aje ta ako Ina ba sai saman milk color din gadon ta mai Kama da gadon sarakuna
Royal furnitures ne a dakin
Komai milk color har cottons dinta sai carpet da ya kasance golden color sai shinning yakeyi
Naj ta kalli mijinta wanda
Yake ta Danna Mata kafafunta da tafin kafanta
Ko headache din xai saketa
baya gajiya da dawainiya da ita tace
Naji Kan ya dena ciwo Bari kawai nayi wanka muje
YOU ARE READING
BETWEEN US ✔
No FicciónStory of three sisters that made alot of painful sacrifices to each other Najmah who happens to be the star of the story, Minal ( Najmah's partner) And Ilham the honest friend
