✨✨✨✨✨
Wanake gani ne kamar Alh. Imran Abban Yusrah ya fada yana mamaki......
Abban Fayrouz yace Ahhh kasanshi ne ?
Kwarai ma kuwa
Bissimallah ku zaunaIlham Tai saurin tashi ganin Dr.Zainab Imran....tace zainab dama ke kanwar ya Shariff ce
Yh...ta amsa Mata tana murmushi
Sannan ilham ta kara Kai dubanta ga Mama tace Mama Ashe kece mahaifiyar zainab da ya Shariff
Mama Tai Mata murmushi kwatankwacin yanda ya Dace tace hakane ya ta Nima naji lbr ki da dadewa Amma bansanki ba har muka hadu
Gashi yau na ganki a lokacin daya kamata Kuma gdanku.Murmushi ilham tayi Bata dago xanjen mama ba don Haka Tai watsi dashi...su Ammie sukai masu maraba sannan
Suka samu waje suka zauna kowa da angle dinsaBayan sun gama cin abinci ne Alh.Salis ya nemi dasu koma waje don tattaunawa
Wani bangare suka nufa acikin katafaren gidan....Wanda akewaye yake ma'ana karamin garden ne don shakatawa
Sun xauna tsahon minti biyar.
Abban Sadeeq yayi gyaran murya yace
Hakika naji dadin zaman Nan da akayi Kuma abin farinciki anan shine a gida akayi wannan haduwan babu abinda xance daku sai Allah ya saka da AlkhairiMurmushi Abban Fayrouz yayi yace haba Daddy ai xaman taren kenan yanxu ba gashi mun xama Yan uwa ba.
Tabbas hakane cewan Abban Yusrah....Alh. Imran dama kana raye Ina ka shiga ne
Uhmmmm Alh.Imran ya ja dogon numfashi sannan yace
It's a long story..... abubuwa sun faru da dama...cikin shekarannan ai na dawo Nigeria da zama tare da iyali na gasunanMasha Allah fadar Abban Yusrah yace...Daddy Alh.Imran course mate Dina ne tun bayan NYSC dinmu bamu sake haduwa ba...gashi yau Allah ya hada mu
Haka Allah ya ke lamuranshi cewan Abba
Toh hanzari ba gudu ba Abba dama da akwai maganan dake tafe da mu personal
Toh wace mgn kenan Alh.Imran
Uhmm.....ya danja numfashi kafin ya daura
To ba wata mgn bace illa kawai ince iri mutum muke nema awajankuAbba ya katse shi da cewa Alh.Imran ban katse kaba Amma ko xaka mana gwari gwari inji bahaushe
Alh.Imram yai murmushi sannan yace
Dana Ahmad Imran Wanda kuka fi sani da Shariff yaga yarku Ilham yana sonta da aureYana son kamar yadda shari'ar musulunci ta kaiyyada da abashi izinin zuwa wajan ta don su dai daita
Murmushi Daddy yayi yace to Alh.Imran Azahiri nine mahaifin Ilham Amma ga iyayenta guda biyu...xan so ka nemi izini a wajan su idan sun amince to falillahil hamd
Murmushi Abba yayi yace nidai awaje na babu wata matsala
Munbashi indai akwai rabo to Ilham Bata da miji sai Ahmad
Kamar yadda Shima Ahmad baida Mata sai ilhamAbban Yusrah ya daura da To Allah ya tabbatar Mana da abinda yafi Alkhairi....
Ameen Duk suka amsa
Sannan suka cigaba da wata hirar.................
Bangaren samarin kuwa suna zaune a part din Sadeeq yake shaida masu abinda iyayensu suka yanke ta hanyar Jin mgn ta Bluetooth....yaji komai
YOU ARE READING
BETWEEN US ✔
Non-FictionStory of three sisters that made alot of painful sacrifices to each other Najmah who happens to be the star of the story, Minal ( Najmah's partner) And Ilham the honest friend