✨ Najmah✨40

85 8 0
                                    

Najmah
Story written by
DielaIbrahim ✍️

(40)

.............

Minti Arba'in ne ya dauke su zuwa Babban Hospital din

Tawagar motocin Marshal su suka fara Isa asibitin
Kafin su Sadeeq suka biyo su a motan taxi din dayake ta dawainiya dasu tun shigowansu babban birinin Riyadh

Kaitsaye Female ward daki na kusa Dana karshe suka nufa
Dakin da zai sada su da Najmah Muhammad

Najmah Muhammad
zaune take ta kura wa laptop dinta idanuwa
Hoto take kallo idanuwan ta sun cika daf da hawaye
Kallo Daya xakai wa hoton ka tabbatar da alakarsu da wannan pic din
Ba da dadewa ba suka gama waya da Mamie Kuma tasa Mamie ta tura Mata pic din tare da taimakon Fahad
Ji take inama mahaifiyarta na Raye dukda Bata rasa komai ba daga wajan Mamie da Abba
Amma jitakeyi Ina ma tare da mahaifiyar ta girma saboda soyayyar uwa daban nee
Bawai ta ga gazawar Mamie bane
Illah tana so taga wacce ta tsuguna ta haife ta
Hawayen da suka cika a idanuwan ta suka zuba batareda Bata lokaci ba hakan Kuma  yayi daidai da turo kofar dakin da 'akayi
Babu shakka Yan uwan tane gaba dayansu
Fuskokinsu ta kalla Amma ta kasa fahimtar me fuskokin nasu ke nufi saboda irin kallon da kowanin su yake jifanta dashi

Ahankali suka Buda tsakiya
Ba kowa ta gani  a wajan ba
Sai Marshal Wanda zuciyanta take gasgata Mata cewan
Tabbas shine mahaifinta

Saukowa tayi daga saman gadon da karfi Wanda har sai da sautin tile yadanyi Kara kadan
Sai Kuma ta tsaya ta kasa karasawa kafafuwanta sukai Mata nauyi
Zuciyarta na dukan uku uku
Kunnuwanta suka Dena Jin sautin komai
Jijiyoyin jikinta suka koma kamar tsinkakku
Saboda shaukin haduwa da mahaifinta
Dukda ba yau ta taba haduwa dashi ba
Amma haduwansu nabyanxu ya xama daban da saurin ganin da Tai Masa
Wata zuciyar na cemata
Ba mafarki kike ba Naj
Tabbas mutumin da ke tsaye acen sanye da kakin soja
Ba kowa bane
Illah Mahaifinki
Naj
Ki Isa izuwa gareshi domin ki bayyanar da farincikin da kika Dade kina nema tun Bayan sanin ke wacece.......

Zazzakar muryar sa Mai Kama da yanda yai mata magana dazu
nee ta Kara dokan Mata kunne

Yana fadin
Come here mi Angel

Kasa hakura tayi ta ruga aguje suka rungume juna tana zubar da hawaye
Shima Kuma Marshal hawayen yake zubarwa

Tsahon dakika goma suna wannan yanayi
Sannan Marshal ya nuna Mata kakanninta

Zuwa tayi wajansu Suma Duk ta rungume su
Naj ta nuna wa Marshal su Minal

She is mi twin sister
Ya zare idanuwa what ku Yan biyu nee
Ta girgiza Kai tana smiling
What I mean Rana Daya aka haifemu
Nan ta fahimtar dashi yanda zai fahimta tare da nuna masa
Su Sadeeq da Shariff
Najmah tana cikin farinciki shiyasa Bata San sanda ta gama bawa Marshal labarin rayuwar ta
Duk atsaye ba

Hakika shikanshi Marshal abin yabasa mamaki
Ganin irin farin cikin da Najmah take ciki
Ya Dan goge hawayenshi kadan
Ya durkusa yayi sujudur shukur
Domin Mika godiya ga ubangiji daya amsa Masa addu'ansa shekara da shekaru
Kenan Yana rokon Allah Daya nuna Masa jininsa indai abinda matar sa ta haifa Yana Raye
Kuma gashi
Alhamdulillah ya furta ahankali

Marshal ya tafa hannu
Tare dace wa Hakika zanso na gaa Mamie da Abba
Dakuma Daddy da Ammie
Actually they really tried alot

BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now