🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Page➡️3️⃣▶️4️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗"Thulaimi(sulaimi) ba dukan hauwan da akayi nake tsoro ba thasoba (sbd) ko nima kusa nake da Chatha(chasa) ta thulaimi fad'an Abba ne ban shirya mishi ba Wlh kin than(san) ba son tashin hankali yake ba na tabbatar kuma se Maman hauwa ta kawo kara" khairi tayiwa sulaimi maganan cikin sanyin murya ganin yadda sulaimin ke dariyar rud'ewantan daga farko shiru kawai sulaimin tayi don bata san me zata ce ba hakan yasa khairi ma tayi shiru da bakinta har suka isa kasuwa ta gate d'in baya suka shiga hakan yasa sukayi saurin isa layin 'yan kayan miya daga nesa take hangan malam umaru wato mahaifinsu da suke kira Abba zaune a gaban kayan miyanshi da ba wani yawan kirki ne da su ba, har suka karasa kusa be lura dasu ba seda khairi tace "Salamu alaikum Abba" juyowa yayi yana sakar mata murmushi yace "wa'alaikissalam na'am 'yar Abba kun karasu kenan?" Har kasa suka duka suka gaisheshi tare da mishi sannu da kasuwa d'an ledan dake ganganshi ya d'auka ya mikawa khairi hannu biyu ta sa ta kar'ba tana mishi godiya sallama suka mishi shi kuma yayi musu Allah tsare suka wuce seda suka sayi sakon sulaimi tukun suka juya gida..
Suna isa khairi ta hura murhu ta d'aura musu abincin daren tanayi suna hira da Dada har Abul ya dawo kusan lokaci d'aya suka shigo da Abba khairi ta kawo musu ruwa suna had'a baki da Dada wajen musu sannu da dawowa, abinda na fahimta shine akwai tsantsar kauna da shakuwa a cikin wannan gida suna tattali da kula da juna ba kad'an ba, dab magrib khairi ta gama girki ta fito daga kitchen din tana sharce gumi don duk tayi zufa sbd hayaki sannu sukayi mata Abul da take kira d'an uwa har da mata dariya bata kula shi ba ta d'ibi ruwa ta shige bayi tare da watsawa sauri sauri tana fitowa ana kiran magrib, ta samu ma Abul ya nemo nabeel duk sunyi alwala zasu fice massallaci itama alwalar ta d'aura tare da shigewa d'akinsu ta tada sallah tana idarwa ta fito ta d'auko katuwar taburmansu da ta ji jiki ta shimfid'a a tsakar gidan tare da shiga d'akin Dada ta tada nabeela tana fitowa ta kunna wani fitila me haske da ake makalawa a sama yana anfani da manyan batir a kan taburman ta ajiye tare da kara komawa d'akin Dada ta kwaso qur'anai dasu hadith, zadulmuslim, riyadussaliheen, Arrijalu wannisa'u fil jannah da dai sauransu ta ajiye akan taburman a daidai lokacin su Abba suka shigo akan taburman suka yada zango har nabeela da yanzu ta idar da sallah irin tasu ta yara karatu suka fara Abba ke koya musu dukkansu Dada ya fara yiwa tukun ummulkhairi da Abulkhairi su kuma suka karawa nabeel da nabeela suna gama hadith da sauran littatafan suka bud'e qur'ani me tsarki kowa ya fara inda yake so Dada na zaune tanayi da kai basu suka rufe alqur'anin ba se da sukaji ana kwala kiran sallahn isha adu'a Abul ya musu suka shafa mazan suka nufi massalaci yayin da matan suka yi a kan taburman suna idarwa Khairi ta shiga kitchen ta fiffito musu da abinci da plates, ruwan sha har dana wanke hannu ta Ajiye, su Abba na shigowa suka nufi taburman a natse suka zazzauna tare da wanke hannu suka fara cin abinci wadda ya kasance tuwon masara da aka d'aure da garin alabo se miyan kuka da akayishi da kifi banda, mazan su uku kwanonsu daban haka matan su uku nasu daban gidan Shiru kaman ba mutane har suka gama suka wanke hannu nabeela ta taya khairi tattare kwanukan zuwa kitchen, wai kafin su fito gidan ya kaure da hira nabeel se zubawa Abba surutu yakeyi yayinda Abul ke magana da Dada su khairi ma jona su sukayi yayinda Abul ke tsokanan khairi tana ta shagwa'ba Abba na kar'ba mata (kai readers gaskiya rayuwan gidannan ya burgeni) tsintar muryan Abul nayi yana cewa "In ba tsoro ba er uwa kice Asiya" Da karfi tace "Athiya" dariya suka face dashi kasancewar bata da "sa" duk yadda tayi sede ya fita a "tha" (ba lallaine duk maganan da khairi tayi in rubutashi da 'th' ba, sbd ba kowa ne ze fahimta ba kuma bazan iya dinga rubutawa sau biyu ba)..
Tura baki gaba khairi tayi tana bubbuga kafa tace "Abbana ba ka ganshi ba" wani dariyan suka sa Abba kam murmushi yayi yana cewa "Zo nan 'yar Abba kyaleshi zan rama miki ne" gwalo ta mishi tare da komawa kusa da Abba tana d'aura kanta kan kafanshi, Baammm suka ji an buga kofan gidan a tare suka maida hankali kan kofan lokaci d'aya khairi ta lumshe ido zuciyarta na bugawa alamun mutanenta suna kusa, hauwa ce da mamanta suka shigo a masifance har kan tsakiyar taburman da suke Maman na zuba masifa kaman zata ari baki "matsiyata en iska, en gudun hijira ko kuma ince korarru wai ku har kun isa? Nace kun isa? Kusa d'an isakan saurayin d'anku yima 'yata duka?" Shiru Abba yayi yana kallon khairiyya har ga Allah shi ba mutum ne me son tashin hankali ba haka matarshi be san inda ummul ta d'auko zafin zuciya ba a sanyaye yace "ummulkhairi bata hakuri, Dan Allah Maman hauwa kiyi hakuri hakan baze sake faruwa ba" Abba ya furta Kan ya rufe baki Maman hauwa ta kar'be "baza'ayi ba, baza ayi hakurin ba Wlh se na rama mata ko akan wannan makauniyar nakasashiyar matan nan taka ko kuma kan gantalalliyar 'yarkan....." Abul yayi saurin cewa "dakata Malama ya za'ayi kizo har cikin gidanmu kina zagar mana iyaye toh ya isheki shiru shiru fah ba tsoro bane, wall......." Dada ce tace "Abulkhairi" Da kausasshen murya shiru yayi yana cije le'be duk da ya kasance marar fad'a ga hakuri amma In an kaishi makura shima ba baya ba wurin masifa, wani irin gud'a Maman hauwa ta sauke tana girgiza jiki tace "Ayyyirrriirii yaro man kaza kai baka kai inyi da kai ba haka uwarka sede inyi da uban ka" Abba yayi saurin cewa "dakata dakata talatu shiru shiru fah ba tsoro bane Wlh gudun magana ne ki kiyayi randa zaki kaini bango" be karasa ba ta sa hannu ta bankad'a shi zuwa jikin gini tace "an kaika umaru nace an kaika me zakayi" shiru gidan yayi na mintuna kan naji wani bala'e'en kara da ya sa hanjin cikina motsawa kaman kiftawar ido naga khairi dake kwance a taburma ta lumshe ido da farko kaman bata san abunda ke faruwa ba, ta isa gaban maman hauwa hannun da ta sa ta hankad'e Abba hannun khairi ta rike tare da kafe Maman hauwan da idanunta da suka koma ja tana mata wani irin deadly look wani irin ihu Maman hauwa tayi na azaba tana kiran hannunta hannunta, khairi ta kara murd'awa tana danne hakwaranta da gudu Abul da Abba sukayi kan khairi suna kokarin cire hannun khairi amma ko motsa hannun sun kasa hauwa ma ta karaso da d'ingishi tana ture khairi wani wawan mari me kurmantarwa khairi ta sakewa hauwa da hannun hagunta inda ta ci gaba da murd'a hannun uwar da na damanta, zuwa lokacin duk makwabta na kusa sun shigo mazan suka taru suna kokarin cire hannun Maman hauwa a cikin na khairi amma abun ya ci tura da sauri Abba ya nufi kitchen ya d'auki cup tare da kanfatan ruwa a randar kasarsu wasu adu'o'i yayi da sauri da sauri ya tofa tare da zuwa ya watsawa khairi a fuska wani irin ihu ta sake tare da sulalewa kasa ta sume nan kukan Maman hauwa ya cika gidan ita da 'yarta tana ta fad'in "ta karyani shikenan ta nakastani kaman uwarta" nace(Lallai matan nan wato bakin nan be mutu ba) wasu daga cikin waenda suka shigo ne suka fice da ita, yayinda gidan ya saura daga su Abba se sulaimi da iyayenta, wasu adu'o'in Abba ya karatofawa a same ruwa tare da watsawa khairi a hankali ta motsa tana dafe kanta da take jin kaman ze rabe sheshekar kukan mahaifiyanta da kannenta yasa ta fashe da kuka itama dukda bata san me y faru ba amma tasan abun beyi kyauba, sulaimi ce ta kamata zuwa kan taburma inda Abul ya kama hannun Dada ya zaunar da ita yana share mata hawaye Abba kuma na lallashin su nabeel, seda iyayen sulaimi suka ga gidan ya d'an natsu tukun suka saka 'yarsu a gaba suka fice suna adu'ar Allah ya kiyaye gaba, sossai khairi tayi kuka inda take ta maganganu tana neman yafiyar iyayenta musamman dada da ta sa kuka anan ne take fad'an "wlh Abba ban mata komai ba haka ban saka idi shed'an bugunta ba Wlh banda masaniyar hakan ze faru da data bangajeni ban tanka mata ba da shiru nayi kaichona...." Abba ne ya katse ta "kul uwar alkhairi yi shiru abinki ba laifinki tun kafin a haifeku take nuna mana wannan hali, ta musgunawa mahaifiyarku ba kad'an ba" Abul yace "Abbanmu me kuka mata?" Shiru Abba yayi kaman baze yi magana ba kuma se yace "talatu tazo ta same mu a unguwan nan da farko a mutunce muka kar'beta duk da bamu san inda ta fito ba hakan be hana mu bata kulawa ba ganin babban ciki a jikinta kuma tana halin neman taimako ni nayiwa Bala dillali magana ya bata gidan da taken nan haya da yake da d'an kud'inta ta zo shawarana ta tambaya na sana'an da zatayi inda na bata shawaran yin abincin sayarwa a bakin kasuwa wadda har yanzu shine sana'anta bayan kwana biyu da ta d'an natsu se ta tareni da wani magana wai In ta haihu na yarda na aureta tunda matata makauniya ce, sam na nuna mata bana sonta ta nemi wani namijin tun Ina mata yadda zata fahimta taki har taja na fara wulakantata ana haka ta haifi 'yarta mace har nan ta zo ta roki mamanku wai inje In ma 'yarta hud'uba da sunan da yamin mamanku bata damu ba kasancewar bata san abunda ya faru tsakanina da ita ba, ta tursasani naje nama hauwa hud'uba da suna hauwa, bayan haihuwan hauwa ta ci gaba da bina ni kuma naci gaba da wulakantata har ya kai na kai karanta fadan sarki inda ya ce ta fita harkana don ta matsamin har kasuwa take bina daga lokacinfa ta d'auki tsana ta daura mana da mahaifiyarku ko motsin kirki bamu da daman yi shine har ya gangaro kanku, kun ji fah"..........
#vote
#comment
#share'Yar mutan Adamawa