Chapter twenty seven

928 83 6
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





                IGIYAR RAYUWA😭





                                             🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

                   'Yar mutan Adamawa

Page➡️5️⃣2️⃣▶️5️⃣3️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Musharraf ba shi ya farka ba se bayan magrib, a hankali ya bud'e ido yana kallon momma dake zaune kan sallaya tana karatun Qur'an a wayanta, mayar da idon yayi ya lumshe yana tunanin marin da momma ta mishi sbd mutumin Chan, duk tunaninshi yayi ya rasa me yasa momma ta mareshi don ya gayamishi abinda y dace dashi da rayuwanshi....................

A hankali ya mike ya zauna tare da gyara pillown da yake kai zuwa bayanshi ya jingina yana taune lips sbd kanshi da ke Sara mishi da jirin da yake ji, motsin shi ne ya sanar da momma farkawanshi tsayar da karatun tayi tana kallon gadon, ganin da gaske ya farka ne yasa ta mikewa tana cewa "sannu musharraf"....................

Kai ya gyad'a ba tare da ya kalleta ba, a hankali tace "wai kai se yaushe zaka girma ne ka san abinda yake daidai da wadda ba daidai ba?" Tura lips dinshi yayi ba tare da yace komai ba, seda ta kuma cewa "ba da kai nake ba musharraf?" Yace "Toh ni momma me kuma nayi bayan ba nine da lefi ba kika mare ni gaban kannena da masu aiki" murmushi momma tayi tana girgiza kai tace "Toh yanzu fushi kake da ni kenan?" Kara tura bakin yayi ita kuma ta saki murmushi tana cewa "Toh kayi hakuri, na san ba lefinka da be maka abinda ya maka ba da baka fad'amishi ko wacce kalma ta fito daga bakin ka ba"........................

Ajiyar zuciya ta sauke kan ta ci gaba "Ina kwa'bar ka ne don bana son Allah ya kama ka da laifi, sbd uba de uba ne ko min lalacewarshi adu'a ne kawai tsakaninku ba wai zagi ba, yanzu In ni ce nayi maka haka haka zaka dinga zagi na?" Had'e rai yace "subhanallah ki dena kwatanta kanki dashi plz momma, baza ki ta'ba ko da kwatanta abinda ya aikata ba" girgiza kai tayi tace "In yana cikin kaddara na dole hakan ya kasance ko da kuwa bana so, shi yasa nake so ka yarda kaddaranshi kenan, ku yafemishi tabbas ya tuba, don naga hakan" Shiru yayi be ce komai ba....................

Kanshi ta ta'ba jin jikinshi har yanzu da zafi yasa ta mikewa tace "bari na kira doctor zazza'bin nan be sauka ba" hannunta ya rike yace "a'a momma zanyi sallah tukuna ko la'asar banyi ba" duk maganganun da yake yin nan muryanshi ba wani fita yakeyi ba sbd mura da ciwon kai, bowl ta samo mishi a toilet da ruwan gora ta rike mishi yayi alwala don ba ze iya mikewa ba sbd jiri haka yake mishi In har jininshi ya hau...............

A zaunen yayi sallah yana idarwa ta sa mishi pepper soup da Amrah tayi, da kanta ta dinga bashi har ya ce ya koshi, magunguna ta 'balla mishi wadda bata jima da sayowa ba, yana 'bata fuska yana komai haka ta sashi sha dole, yana gama sha doctor na shigowa da fara'a ya mishi sannu da jiki amsawa musharraf yayi yana d'an murmushi....................

Dube dubenshi yayi kan yace "masha Allah, Dan Allah ka kwantar da hankalinka samun jinin da ya hauran nan ya sauka" murmushi kawai musharraf yayi ba tare da ya ce komai ba, fita doctor Aslam yayi don ba yau ya san halin musharraf ba, momma tace "ga jallabiya nan ko zaka chanza" kar'ba yayi ta fice daga d'akin bayan wasu mintuna ta dawo da waya sakale a kunnenta tana kallonshi ya chanza zuwa jallabiyan brown color sossai ya mishi kyau kaman ba shine mara lafiya ba........................

"Eh yaya, amma da sauki sossai a'a hawan jinin ne de, toh mun gode se da safe" tana kashe wayan ta kara danna wani layin bayan an d'auka suka gaisa tace "Rabi'ah ya kk ya su afreen?" Be ji me aka ce daga d'ayan bangaren ba se momma da tace "Toh gashinan de musharraf ne Wlh ba lafiya muna asibiti" Shiru tayi kan tace "Eh amma da sauki sossai, Ohk toh se kinzo"...............

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Donde viven las historias. Descúbrelo ahora