Chapter fourty six

934 82 6
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗




              IGIYAR RAYUWA😭


                                               🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

                   'Yar mutan Adamawa

Page➡️8️⃣8️⃣▶️8️⃣9️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Babban parlorn dake saman ta fara cin karo dashi had'adden parlorn da ya tafi da imaninta komai na ciki sky blue se ratsin fari fari a abubuwa dayawa wani katon wall sticker ne zagaye da parlorn da In baka sani ba zaka ce carpet ne aka manna tsabar had'uwanshi, bata tsaya kalle kalle ba ta bud'e d'akin farko dake parlorn babba ne sossai ba komai cikinshi se abubuwan gym dinshi dumbbell, treadmills da dai sauransu, janyo kofan tayi ta koma na karshe ta bud'e nan kuma ba komai se shimfid'add'an tiles fari da wani carb ward na littatafai kaman library sede litattafan basu dayawa har chan hakan yasa carb ward dinma ya zama daga jikin gini d'aya.

Jikin windown room din kuma study table ne me had'e da kujerunshi guda biyu se kofan toilet dake gefen kofa wurin ya mata kyau sossai musamman da ya kasance d'akin corner room ne, kallon white door din tsakiyan tayi kenan tabbas shine nashi zuciyarta dake ta tsalle ya kasa zama wuri d'aya ta dafe tsoro ne fal ranta amma ya ta iya hakan shine solution.

Seda tayi adu'o'inta kan ta tura kofan da sallama duhu dulum d'akin kaman ba wuta a gabad'aya gidan ko tafin hannunka baza ka iya gani ba sbd an kashe duk wani abu me supplying haske a d'akin, sake sallama tayi a hankali, jin ba'a amsa ba yasa ta juyawa don ficewa se taji an kunna wutan d'akin, a tsorace ta juyo se ta hangeshi zaune chan karshen gado a takure kaman ba gidanshi ba kallon seconds biyu yayi mata kan ya maida kanshi tsakanin cinyoyinshi.

A rud'e take kallonshi sbd hawayen da ta gani ke zuba a idonshi da kyar ta samu ta seta kanta kan ta karasa bakin gadon cikin natsuwa ta zauna a hankali tace "Hamma na zo mu yi maganar fahimta ne dakai, na gaji da irin wannan zama da mukeyi Ina rokon ka don alfarman annabi da alqur'ani ka fad'amin laifin da na aikata a gareka ko zan samu sa'idar azabtar danin da kakeyi".

Shiru yayi kaman baze ce komai ba kan ya d'ago kai yasa hannu ya share fuskanshi cikin dashewar murya alamun ya jima yana kukan yace "me yasa zaki min haka ummulkhairi? Me yasa kika dasa min bishiyar soyayyarki a zuciyata wadda har root din ya mamaye ko Ina bayan kin san you are not pure? Me yasa baki gayamin komai akan hakan ba se kawai inji daga wani wuri kuma a ranar d'aurin aurenmu? Khair me na miki da zafi haka? Am really heartbroken am hurting down there" ya sa hannu a kirjinshi yana mata alama.

Hawaye ta fara yi me tayi ne haka da bata sani ba? Kukanshi ba karamin d'aga mata hankali yayi ba ita kanta ta san abun ba karami bane tunda har yasa jaruminta kuka amma bata da masaniya akan abinda yake cewa hakan yasa tace "I think am confused, Sam ban fahimci inda zantukan ka suka dosa ba" wayanshi ya jawo tare da kunna hasken har hannunshi na 'bari wurin hawan WhatsApp din da kyar ya kai kan numbern ya lumshe ido kan ya mika mata wayan.

Kar'ba tayi tare da kallon fuskan wayan Ai bata san sadda tayi wani irin mikewa ba tana ambaton "innalillahi wainna ilaihi rajiun" jikinta ne ya d'auki rawa har tana kasa tsayuwa a rud'e ta fara scrolling din fuskan wayan Ai bata san sadda tayi wani irin kara ba tare da sulalewa kasa ta fad'i sumammiya da gudu ya sauka zuwa kanta ya d'ago kanta zuwa kan kafanshi tare da sa hannunshi a hancinta ya zata mutanenta ne suka zo se yaga akasin haka don suma tayi chak ya d'agata ya d'aura kan gado tare da zare mata hijab din jikinta da sauri ya shig bayangida ya d'ibo ruwa yazo ya fara shafa mata a fuska zuwa wuyanta.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now