Chapter thirty one

902 69 4
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗






IGIYAR RAYUWA😭




🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad gurin

Wattpad:- Gureenjo

'Yar mutan Adamawa

*This page is dedicated to yhu mama on this your special day, Ina rokon Allah ya karo miki shekaru masu albarka, ya biya miki dukkanin bukatunki na duniya da lahira, Allah ka bata tsawon kwanan da zamu faranta mata kamar yadda ta faranta mana kuma take kai. Yhu the best woman I've ever met and strong lady I've ever known. I love yhu so very much mama*

Page➡️5️⃣9️⃣▶️6️⃣0️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Musharraf ne ya kula da ni a ranan, dukkanmu da ni dashi tea muka yini sha sbd be iya girki ba ni kuma bazan iya ba, da dare mahmoud ya dawo ganin ba abinci a dining yasa ya nufi d'akina da belt a hannu Ina kwance cikin burgo ya yaye blanket d'in ya fara dukana, bai hankara ba kawai yaji saukan kwalba a keyanshi a matukar razane ya juya da tsantsar mamaki yana kallon d'anshi d'an shekara tara wai yana dukanshi..........................

Kwalban pepsin dake hannunshi ya bi da ido, belt mahmoud ya zuba mishi shi kuma ya d'aga kwalban da niyyar sake kwad'a mishi a firgice nace "innalillahi wainna ilaihi rajiun Abubakar!! Me zan gani haka? Me kakeyi" na karasa maganar cikin d'aukewar hankali ban kara sanin inda kaina yake ba se na ganni asibiti su hamma Ahmad suna tsatsaye kaina sannu suka dinga min...............

A kasalance na amsa Ina dudduba inda zanga musharraf baya d'akin, yaya Ahmad yace "sannu fatima, dukanki ya sakeyi ne? Musharraf ya kira mu da gaggawa wai yazo ya ajiyeku a asibiti yayi tafiyarshi" girgiza kai nayi nace "a'a hamma be dakeni ba ban da lafiya ne, Ina musharraf d'in?" Yaya Nasir yace "yana waje yaki ce mana komai" ajiyar zuciya ta sauke tana runtse ido, doctor Aslam ne ya shigo yana kallon su hamma Nasir yace "congrats tana d'auke da cikin wata biyu" cikin jin daad'i sukayiwa Allah godiya...................

Nan suka tambayeshi yaushe ne sallama, yace za'a iya sallamanta zuwa gobe da safe, godiya suka mishi ya fice a take suka kira su dadda suka fad'a musu suma sunyi farin ciki sossai da sukaji da laulayi kuwa suka ce zasu bani dattijuwar me aikinsu ta kwana mini biyu, Ai ko washegari aka sallameni na samu ma mai aikin ta iso na bata d'aki cikin part d'ina tunda aka kaini asibiti musharraf be yarda mun had'a ido ba har aka sallamoni..............

Bayan mun dawo ne na samu ganinshi sossai na mishi fad'a da nasiha yace baze sake ba, a haka a haka na yi renon cikin nuriyyah har na haifeta tun daga sanda musharraf ya d'aga ma mahaifinshi hannun kaina be sake dukana a gabanshi ba sede yayi min hukunci a lokacin kwanciyar aure, abinda ya matukar bani mamaki kuwa shine ganin sa'banin yadda na gani a lokacin haihuwan musharraf.......................

Allah ya d'auramishi son nuriyyah tun daga randa ya d'aura ido a kanta hakan yasa ta samu gatan suna sossai daga wurinshi har su yaya nasir suka zata ya sauya haline amma hausawa suka ce hali zanen dutse yana nan da kayanshi, seda nuriyyah ta shekara biyu tukun muka koma Abuja inda ya ci gaba da shaye shayenshi wadda da bayayi a gombe, ko da yanayin kuwa be ta'ba shigowa gida a buge ba....................

Sam jituwa be ta'ba shiga tsakaninsu da musharraf ba nayi iya yina da kokarina don ganin musharraf be tsani mahaifinshi ba amma ban ci nasara ba ganin abun na shirin kwa'bewa yasa na yi enrolling musharraf a boarding school don tun kafin mu dawo mahaifinshi ya dena biya mishi kud'in makaranta wai ba yadda za'ayi yana wahala da yaro bayan ci da sha ya kuma biya mishi kud'in makaranta amma yazo yana mishi rashin kunya ba....................

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now