🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gureen
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
*my first dedication in this book will goes to kindhearted woman, with a unique name and a very kind full habit- Sawdah-edress, Allah yasa ki fi haka, ya rabaki da sharrin makiya, ya kuma bar zumunci🥰🥰*
Page➡️1️⃣7️⃣▶️1️⃣8️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗Bayan kwana uku
Yau Abba ya cika kwana uku cir da rasuwa yayinda family d'inshi suke cikin tsanani da matsin rayuwa, da ba don Allah ya basu makwabci me halin sahabbai ba da basu san inda zasu jefa kansu da rayuwansu ba............
Tunda aka watse a bayan an kai Abba an dawo, baba da kanshi ya dinga d'iban akwatunansu yana kaiwa d'akin sulaimi na Abul ne kawai ya shigar d'akinshi inda ya fitar wa Maman sulaimi da akwatin da ta had'a na kayanta zuwa d'akin sulaimi...........
Duk da shi talaka ne futuk amma yana da wadatar zuciya bade a rasa abinda za'a sa a baki a gidan na kwana ukun nan kam safe,rana, dare. Abunda ke d'aga mishi hankali shine In aka wuce haka be san ta inda ze ciyar dasu ba, Ya nemi jin me ya faru gidan Malam umar ya kasance a kulle Maman sulaimi tace bata sani ba Wlh taji de kukan dada se ta fita ta samu yayan babansu khairi na ta watsar da kayakinsu shine na nemi yara suka tattaro zuwa nan, muna shigowa kenan kuma kuka shigo..............
Sauke ajiyar zuciya yayi inda ya kudurta a ranshi ana sadakar uku ze zaunar da Dada ta fad'a me ya faru me kuma yasa hamma habu ze koresu a gidan da yake na mijinta?............
Yauma Alkali ne ya kawo masa/waina da kunu ba'a wani 'bata lokaci ba akayi ma mamaci adu'o'i aka ci aka sha kowa ya watse yana me bin Abba da adua, har cikin gida baba yayiwa alkali iso inda ya kara yiwa su dada ta'aziyya su kuma suka mishi godiya sossai akan hidiman da yayi dasu..............
Bayan tafiyanshi ne baba ya kira Maman sulaimi, Abul, se khairi suka zauna daga tsakiyar gida, inda baba ya kalli dada dake sanye da khimar dogo har kasa, a natse yace "Maman nabeel ya kamata mu san me ya faru bayan tafiyar mu koto, me yasa hamma habu ya watso muku da kaya waje bayan gidan ya kasance mallakinku?"...........
Runtse ido dada tayi, idon da In ka gani zaka rantse ba makauniya bace In har ba fad'a maka akayi ba, a sanyaye tace "hmmm ban san me kaddara ta tanadar mana a gaba ba amma Ina matukar tsoro da shakkar abinda ze biyo baya muddin burin Hamma habu ya tabbata, mawiyacin hali da suka sa mu, da kuma tagayyar da rayuwanmu da sukayi be ishe su ba har se sunzo neman wani abin kuma a garemu a daidai lokacin da d'an uwansu ke halin mutuwa ko rayuwa.....".......
Hawayen idonta ne suka zubo a kan kuncinta, khairi ce ta sa hannu ta goge mata, da dishashiyar muryarta da sam baya fita sossai tsaban kara da takeyi idan aljanunta sun tashi da kuma kukan da take sha bayan sun tafi, a kwanakin nan baza ta iya lissafa sau nawa sukazo ba duk ta rame se ido da tsiririn hancinta ake gani............
Tace "Dada ba tun yau ba muke rokon ku ku fad'a mana tarihin rayuwanku da abinda yasa 'yan uwanku gabad'aya basa sonku, sau d'aya kachal muka je 'baba gaasa' amma mun fuskanci wulakancin da bamu kara marmarin zuwa koda ta arean ba, me kukayi musu da zafi haka da har d'an uwansu na jini ze fad'i ya rasu ba wadda yazo ta'aziyya ko zaman makoki? Dan Allah ki daure ki fad'a mana su wanene ku"...........