Chapter thirty six

941 94 16
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





               IGIYAR RAYUWA😭





                                              🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

                  'Yar mutan Admawa

Page➡️6️⃣9️⃣▶️7️⃣0️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Wani irin sharp idea ne ya fad'o mata dukda ta san it is not right a matsayinta na er talaka amma tana tsoron zargi ya shigo tsakaninta da musharraf In har ta aureshi kai ko bata auri musharraf ba ta san mutuncinta na 'ya mace, cikin abinda be wuce kyaftawar ido ba ta d'aukeshi da wani wawan mari tare da fisge hannunta had'e gabas da yamma tayi, shi kuwa abun ya zo mishi out of blue, dayake bayanshi ne ke facing kofa se be ga musharraf ba, ganin tana kokarin wucewa bayan ta mareshi, shi da kowacce mace ke burin samu sbd kyaunshi irin na shuwa arab da kuma kud'in da yake dashi, don ma ya nuna yana sonta ba wai asalin so yake mata ba kawai de akwai abinda ya gani jikinta ne da ya kula ba wadda ya lura da hakan..................

Duk Laifin kanshi yake gani na kulata da yayi be danneta ta karfi ya biyawa kanshi bukata ba, cikin zafin nama ya damko hannunta tare da murd'e shi a bayanta wani d'an kara ta sake tana juyowa taji saukar hannunshi a fuskanta wadda har seda ta dena gani da ji na wucin gadi, d'ago hannun yayi da niyyar sake kaimata mari yaji an damke hannun, a zafafe ya juyo yana kallon musharraf dake tafasa har fuskanshi yayi ja tsabar 'bacin rai, shi karan kanshi ya manta last da yaji irin wannan ciwo da 'bacin ran da yakeji daga kirjinshi har kan harshenshi.

Mamaki ne ya kama sufyan a saninshi musharraf baya shiga abinda be shafeshi ba amma gashi akan wannan banzar yarinyar ya hango abinda be ta'ba hangowa ba a idon musharraf tsantsar kishi da 'bacin rai har rufe mishi ido yake, naushin da musharraf ya sake mishi a fuska ne ya dawo dashi daga tunaninshi zaro ido yayi yana kokarin fusge d'ayan hannunshi dake cikin na musharraf amma ya kasa.................

Naushinshi musharraf ya dinga yi da hannunshi na dama shi kuma yana tarewa da na hagu ganin In be yi wani yunkuri ba fa musharraf ze iya illatashi hakan ya sa shi saka iya karfinshi ya fusge hannun tare da kaiwa musharraf naushi a fuska shima, Ai ko nan ran 'yan maza ya 'baci suka fara kaiwa juna naushi sede ba'a d'au lokaci ba sufyan ya galabaita abinka da wadda yayi zaman prison har ya zama kwaro a cikinsu.............

Khairi kuwa ganin musharraf ze iya yin kisa yasa ta Kwasa a guje zuwa part d'in dadda ta san ko ta hanashi ba hanuwa ze yi ba balle ma baza ta iya ba sbd tsoronshi da ya shigeta lokaci d'aya, da karfi ta tura kofan parlorn tana cewa "momma ki zo, momma!! Hamma musharraf" tana magana tana nuna waje da sauri suka mike momma tayi saurin bin bayanta ganin ta kuma kwasa a guje, suna turo parlorn suka sake salati a tare............

Da sauri momma tayi kanshi tana kamashi a lokaci d'aya tana kiran sunanshi, cikin 'bacin rai ya ture hannun momma yana shirin komawa sufyan da be dena zaginshi ba, uncle Ahmad ne ya tsinka mishi mari yana cewa "baka da hankali ne da girman ku  musharraf? Me ya had'aku haka??" A zuciye musharraf ke kallon uncle Ahmad yana ta aikin sauke numfashi yayinda hannunshi ke a dunkule, wato ubanshi son kai zeyi me yasa be mari d'anshi ba se shi...........

Sufyan ne dake zaune kasa jini na d'iga a fuskanshi yace cikin alamun kuka a muryanshi "Abba wai akan wanchan banzar yar......." "dakata!! Wallahi ka kiyaye ni na rantse da girman zatin Allah ka sake cewa abinda zuciyata ke SO banza zan kakkaryaka a gidan nan, In kuma ka Musa ka gwada inga uban da ya tsayamaka"...........

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now