Chapter fifthy two

1.7K 90 16
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗




              IGIYAR RAYUWA😭


                                            🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

       'Yar mutan Adamawa

Las Las

Page➡️1️⃣0️⃣0️⃣▶️🔚🔚🔚
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Gabad'aya parlorn mikewa sukayi ganin yadda yake 'bari kamar mazari dama ranshi a 'bace yake ga maganganun hajiya zulai da Anty Rabi'ah yau ba don matar uncle Ahmad bace, ba don yana ganin girman uncle Ahmad fiye da sauran uncles dinshi ba, ba don ba tarbiyar momma ba kenan da ba abinda ze hanashi yiwa matar dukan mutuwa, shiyasa ya sauke hannunshin akan d'anta da dama shine silar 'bacin ranshi tun farko, uncle nasir ne yace "musharraf wai lafiyanka kuwa?" Momma tace "me ya maka haka?" Hararan da sufyan ke mishi ne yake kara tunzura shi hakan yasa shi had'ashi da gini ya shakeshi da sauri khairi ta dafa hannunshi ganin yadda hajiya zulai ke ihun ze kashe mata d'a.

Momma ta karaso ta d'aga hannu da niyyar sauke mishi mari da hanzari khairi ta shiga marin ya sauka a fuskanta har seda ta zube a kasa tsabar karfin marin, ido ta runtse yanzu da haka marin ze sauka a fuskanshi inaa ta san komai musharraf yayi akwai dalili tana kyautata zaton ba Haka kawai ze hau dukan shi ba, da azama musharraf ya sake Sufyan yana d'agota kallon cikin idanunshi da yayi ja tayi ta runtse ido se hawaye da kirjinshi ya had'ata yana kallon momma da ta tsaya kaman mutum mutumi haka su uncle nasir ma karfin halin khairi suke jinjinawa.

A hankali ya fara magana cikin rawar murya ya bada labarin abunda aka turamishi ran aurenshi wadda yayi sanadiyar kwanciyanshi asibiti ya kara da irin zaman da yayi da khairi kan ya zo ya gane karya ne da alqawarin da ya mata ya d'aura da "na shafe wata shidda chur Ina neman me wannan numbern, har experts a harkan tracking fiye da mutum hud'u na biya amma ba'ayi nasara ba se yau a d'azu d'aya ya kira ni ya bani full details na wadda ya had'a hoton kuma sunje sun sameshi da police inda ya amsa fault d'inshi ya kuma bada details na waenda suka sa shi, and that turns out that sufyan ne ya biyashi don aikata hakan and wanchan munafukan ya nuna Afreen ita ta zo har cikin gidan nan ta d'ad'auki qalbee hotuna daban daban" yana shafa bayan khairi yace "am sorry qalbee na kasa cika alkawarinki sbd munanan kalaman da iyayensu suke jefanki dashi" kallon su Hajiya zulai yayi yace "and yhu this is my first and last warning Wallahi wallahi mata ta kara zagarmin mata se nayi mata abunda bata ta'ba tsamanni ba, ku kuka hallici juyan? Ko ku kuka h......" "musharraf" momma ta kira shi In a whisper.

Shiru yayi tare da jan hannun matarshi suka fice daga parlorn, basu karasa fita ba suka ji saukar mari har kusan kala hud'u, uncle nasir ne yake saukewa sufyan duk sanyinshi seda ranshi ya 'baci yau haka ya rufe Afreen da duka wasu irin yara ne su, seda uncle Ahmad ya gama dawowa daga suman tsayen da yayi kan ya kalli Hajiya zulai yace "ki tafi gidanku se na neme ki" waro ido sufyan yayi tare da zubewa a wurin yace "kayi hakuri dad wallahi bazan kara ba, karka hukunta mom akan abinda ba ita ta aikata ba na tuba" hararanshi uncle Ahmad yayi kan ya juya ya fice momma de bata ce komai ba amma kallo d'aya ka mata zaka san ranta a 'bace yake haka su Amrah da mai jego ma se harara suke sakewa su afreen din, wato uncle Ahmad ya san hukunta mahaifiyar sufyan ne kad'ai ze sa shi ladabta yayi nadamar gaskiya sanin yadda yake kaunar mahaifiyar tashi, ita kuwa cikin kuka da ihu ta fice daga gidan, hajiya rabi'ah ta rufa mata baya Afreen kuwa Uncle nasir yace da ita ze tafi zata ci me unguwan garinsu a gidanshi cikin sacewar gwiwa sufyan ya mike ya fice, nan momma ta kira bappa ta fad'a mishi duk abunda ya faru ta kuma tabbatar mata da hakan, inda bappa yayi alkawarin sa taheer yaje har gidanta ya ci mata mutunci kuma shima ze kirata haka diddinsu ma, hakuri ya dinga bata har taji kunya.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now