Chapter eighteen

762 74 2
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





             IGIYAR RAYUWA😭





                                          🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

         'Yar mutan Adamawa

Page➡️3️⃣4️⃣▶️3️⃣5️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Yau kwana biyu kenan khairi na fita tana aikin neman aikatau amma bata samu ba wulakanci kam ba wadda bata gani ba amma da yake ta sawa zuciyarta neman aikin ya zama wajibi a kanta hakan be dameta ba, babban damuwanta ma kayan abincinsu da suke barazanar karewa don be wuce ya musu kwana biyu ba.................

Tare da su nabeel suke fita ta ajiyesu islamiyya ta wuce kasancewar basu shiga boko ba ta roka su dinga zuwa da safe ma ko ran makaranta ne kan su shiga bokon dayake yara ne masu shiga rai har sun saba da islamiyyar kamar sun shekara cikinta, hannun nabeela ya sabe sossai sede be warke ba, daga randa nabeela ta kone kullum kan ta fita se tayi musu abincin rana take fita, tana kuma iyakar kokarinta don ganin batayi magrib a waje ba....................

Yau ma kaman kullum bayan ta gama shiri tayiwa dada sallama suka fito hannunta rike da su nabeel se da suka shiga gidan Maman hamdeeya fishaa kan suka fito suka wuce kasancewar kwana d'aya kenan basu had'u ba, bayan ta ajiye su nabeel ta tari napep ta shige kud'in hannunta saura 300 duk ranta a jagule tana tunanin In bata samu aiki yau ba bata san da wani kud'in zata fita gobe ba, amma bata cire rai ba Allah na nan...............

Cikin mintuna kad'an suka isa low cost cikin d'ari d'ari ta sauka sbd duk cikin unguwannin da take zuwa ba wadda gidajen suka tsoratata kaman waennan ga ko wanni gida da securities, wani gate ta fara knocking gateman din ya fito sanye da uniform yake tambayarta lafiya? Tace "don Allah matar gidan nake son gani" ta san in tace zata dinga fad'awa gate-mans abinda yake tafe da ita zasu dinga mata bukulu ne..................

Kallon sama da kasa ya mata kan ya bata hanya ta shige duk da ya san madam dinshi bata harka da talaka aiko khairi na shiga tana fad'an abinda ya kawo ta matar ta mata korar kare ta had'a harda gateman d'in ta zage tas, a tsorace khairi ta shiga gida na biyu nan ma wulakanci aka mata haka ta dinga yawo duk gidan da ta shiga koranta ake, wasu kam ma har cewa suke ko an aiko ta spying ne, wasu harda barazanar rufe ta a police station sukeyi.......................

A haka har akayi azahar ta samu panpom gefen wani gida tayi alwala tare da komawa gefe ta shimfid'a d'ankwalinta dukda bata san gabas anan ba amma haka tayi sallanta, bayan ta idar ta jima sossai zaune a wurin duk damuwanta na kan rashin samun aikin nan ga kud'in hannunta sun kare ga kayan abincinsu na hanyan karewa, babban damuwanta school tana mugun son su koma makaranta ko shedan gama secondary d'inta ta samu...............

Bayan ta gama sake sakenta ta mike ta ci gaba da tafiya a sad'ad'e har ta samu wani shop sadakarwa tayi ta karasa ta sayi pure bliss da pure water d'aya ta samu wuri ta zauna taci ta sha ruwan kan ta ci gaba da roaming har gab magriba la'asar ma a wani gindin bishiya tayi, ganin magrib ya gabato yasa ta fara neman napep don komawa gida amma ko d'aya bata gani ba ga hadari da ya had'u lokaci d'aya...................

A mugun tsorace take kalle kalle ko gilmawan mutum d'aya babu securities da suke kofan gidaje dayawa ma babu duk sun koma daga ciki tafiya ta fara sauri sauri tana aduar Allah ya sa ta samu ko machine ne, duk hankalinta ya tashi akwai wani gidan da ta wuce d'azu da ko marmarin shiganshi batayi ba sbd yawan securities din da ta gani kofan gidan akwai kaman rumfah haka wurin taje ta tsaya amma ko minti biyu batayi da tsayuwa ba wani katon security ya fito ya koreta..............

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now