Chapter twenty four

838 72 4
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗






IGIYAR RAYUWA😭





🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

'Yar mutan Adamawa

*Alhamdulillah Ala kulli haalin, thanks for your prayers🙏*

Page➡️4️⃣6️⃣▶️4️⃣7️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Tunda garin Allah ya waye take jin gabanta na fad'uwa kaman yadda yake mata de in jikinta ze tashi ko kuma mutanenta suna kusa, kaman ta ki zuwa wurin aikin amma In ta tuna momma tace akwai ayyuka dayawa yau sbd dawowan musharraf se jikinta yayi sanyi bata so su sha wahala.............

Dada ta fad'awa bayan sun gama breakfast dada tace "ki yawaita azkar a zuciyarki kuma ki kiyaye duk abinda kika san ze ja miki 'bacin rai, Allah ya tsare de kar suyi miki sanadiyar aikin nan" khairi tace "Ameen" a sanyaye ta gama duk abinda zatayi suka sallami dada suka fito ta ajiye su nabeel makaranta ta wuce GRA............

Yanzu sunyi time table sbd saukaka mata base ta dinga tambaya ba musamman breakfast, yau Irish potato za'aci da kwai se black tea duk me so se ya zuba madara da bournvita, aikinta ta fara cikin natsuwa tunda kitchen din a goge a share ta sameshi, kan lokaci ta gama ayyukanta tare da shiryasu kan dining, ta dawo kitchen ta wanke duk abinda ta 'bata ta kuma share kan gas d'in.................

Bayan ta gama ta koma d'aki taje ta kwanta har wa yau zuciyarta be dena bugawa ba, adu'a kawai takeyi a cikin ranta, ta jima sossai a haka ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba, tana jin muryoyin su momma a parlor amma ta kasa tashi ta fita, tanaji momma ta turo Miemie ta dubo ta ko lafiya, har Miemie ta shigo bata iya ta tashi ba seda ta jijjigata tukun ta bud'e ido Miemie tace "khairi, khairi tashi momma na magana" ta juya ta fita, a hankali ta mike ta sa khimar dinta ta fito..................

Har kasa ta duka tace "Ina kwana momma?" Momma tace "Lafiya klau ya gajiyar aiki? Da su dada?" Khairi tace "duk Lafiya klau Alhamdulillah" gaisawa sukayi da nuri tukun Miemie, Amrah da little kam sun tafi school, salima da maryam kam sun jima da komawa gidajen iyayensu, khairi tace "me dame za'ayi momma?" Momma tace "eh toh zakiyi pepper soup na kifi, se tuwon semonvita da miyan ku'bewa d'anye, se zobo da fruit salad" kai khairi ta gyad'a tace "bari na fara wasu abubuwan yanzu kar lokaci ya kure" da toh momma ta amsa tana cewa "nuri da Miemie ma zasu shigo su tayaki"..................

Tashi sukayi suka rankaya kitchen din gabad'aya ko wacce ta fara aiki, cikin lokaci kankani suka gama, nuri na kallon khairi tace "Ke kuwa khairi lafiyanki kuwa yau? Na ganki duk wani iri" khairi ta d'anyi murmushi tace "lafiya klau Adda kawai kaina ke d'an ciwo amma na san zuwa anjima ze yi sauki" miemie tace "subhanallah sorry bari In kar'bo miki magani wurin momma"....................

Ficewa tayi Ba'a jima ba ta dawo da panadol biyu a hannunta nuri ta miko musu ruwa ba yadda ta iya haka ta kar'ba ta sha, karasa had'a zobon dake gabanta tayi tana jin miemie da bata dad'e da fita parlorn ba na cewa "Adda nuri har sun shigo gombe fah, inaga tafiyar asuba sukayi amma wannan karon sunyi sauri yanzu 12 fah" nuri dake kitchen din bata ce komai ba se had'a fruit salad d'inta da ta ci gaba................

Khairi kuwa jin sun shigo se kawai ta juye zobon a wani plastic robber me d'an girma ta d'auka ta sa a deep freezer wai don ya d'an yi sanyi kan ya karaso, nuri kuma ta zuba fruit salad din a jug ta saka mishi kankara ta had'a akan tray da cups ta fitar zuwa dining, wanke wanke khairi tayi tare da share kitchen din ta goge ya fita kal kaman ba'ayi aiki a ciki ba...................

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now