Chapter fifthy one

963 72 2
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗




                 IGIYAR RAYUWA😭



                                               🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo 6763

              'Yar mutan Adamawa

Second To The last page

Page➡️9️⃣8️⃣▶️9️⃣9️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Bayan kwana biyu da dawowarsu suka je gidan Abba a parlor suka samu familyn gabad'aya zaune ana hira gidan gabad'aya an sake renovating har furnitures din an chanza kuma Abban ne da kanshi yayi yaki sam su Alhj mudassir suyi, da gudu su nasreen suka zo suka rungume khairi suna murnan ganinta bayan sunyi breaking hug din suka je zasu rungumi little da gudu tayi kan cinyar dada tana tura baki.

Dariya suka saka don sun san fushi tayi da suka fara rungume mommynta, sukayi kanta a cewarsu se sun rungume tan, da gudu ta fara zagaya parlorn suna binta, d'an karamin tsaki musharraf ya saki da su Amrah ne ba abinda ze hanashi make yarinya, khairi tace kasa kasa "sorry mu karasa" karasawa sukayi Abba na musu Sannu da zuwa haka dada ma har kasa suka duka suka gaisheshi ya amsa da fara'a haka dada ma, bayan sun gama gaisuwan ne suka mike suka zauna saman cushions.

hira suka fara khairi de se kallon dada takeyi tana mamaki dada ta dawo wata hajiya tashi d'aya ko leshin jikinta ma abin kallo ne se ta fito a marar shekarunta anan ne ma take ji wai next week zasu tafi Spain akwai abinda ze kai Abban ze tafi da ita a gwada mata aikin ido, sossai khairi ta nuna jin daad'inta tayi ta wa Abba godiya yana dariya yace "me na godiya ummulkhair bayan matata nayiwa" murmushi tayi tana dukar da kai, sallama musharraf ya musu ya fice akan se da dare ze dawo ya d'aukesu, har wurin mota khairi ta raka shi suna 'yar hiransu na masoya.

A d'akin Nasreen ta yada zango inda nan ta samu Afreen suka shiga hira suna tuna abubuwan da aka yi tayi lokacin bukin su marwa, kan ta shiga seda ta leka little a d'akin nabeela ta gansu suna wasa da kayyayakin wasan nabeelan d'akin kawai abin kallo ne an shiryashi gwanin sha'awa.

Bata ga Abul ba seda suka zo cin abinci daga gani da alamu yanzu ya tashi daga bacci "eyeee jin daad'i se yanzu ka tashi?" Murmushi yayi yace "to 'yar uwa me mutum ze yi yanzu bayan baccin ba karatu ba komai gashi Abba ya hanani d'inki" murmushi tayi kan tayi magana Abba yace "Eh ba wani d'inkin da zakayi da raina da lafiya na ga kud'i, zaman rashin karatun ma na this year ne kawai next year zakayi waec da neco In had'aka da 'yan uwanka a Nile" murmushi kawai Abul ke ta bugawa cikin jin daad'i wai yau shine ze je Nile university hmm Allah kenan, se kuma tunanin Abbanshi ya fad'o mishi adu'a kawai ya mishi ya ci gaba da cin abincinshi.

Bayan sun gama cin abinci d'akin dada khairi ta shiga ta fad'a gadonta se bacci dayake fashin sallah take se la'asar lis ta farka ta shiga ta wanko fuskanta da bakinta a bakin gado taga dada zaune bayan fitowanta tana murmushi tace "dada kinyi ta shigowa Ina bacci ko?" Dada tace "Ai ko de wannan baccin naki kaman ba na lafiyannan ba har yanzu yana nan khairi? A gidanki wa ke miki aiki?" Tura baki tayi tace "na dena fa dada, yanzu dinma don baya nan ne amma ai matsalan hamma dayawa yake In yana tare dani" dada tace "hmm to an ji me miji, ba de haka kike sake baki kiyi ta surutun miji da kawaye ba kam?" Bubbuga kafa ta fara "haba haba dada se kace wata sakarya, wannan ma fah don kene" hmming dada tayi inda suke ci gaba da hiransu na tsakanin 'ya da uwa inda har dada ta tambayeta jikinta baya tashi ko, tace tunda suka tashi ranar kamu da dare basu sake tashi ba.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Donde viven las historias. Descúbrelo ahora