Chapter fourty one

940 75 1
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗



   IGIYAR RAYUWA😭


                   🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, charity, honor and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

     'Yar mutan Adamawa

Page➡️7️⃣9️⃣▶️8️⃣0️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Cikin natsuwa ta fara girkin don ita a ganinta ba wani abu me wahala suka bata ba kasancewarta me son girki, babban abunda ke damunta rashin tarbiyar Afreen tana ga se ta seta yarinyar ta kiyayeta a gidan ta rasa dalilin tarewarta a gidan tun last week, ga mamanta da kullum tana hanya, a fili ta furta "Au na manta ita da gidan pendonta!!" Tana ta sake sake tana girkin amma duk sadda ta tuna da musharraf se taji wani farin ciki wadda hakan ke kasa boyuwa a fuskanta bayan ta gama ta jera musu a dining ta shige d'akinsu tayi wanka da karamin towel ta fito d'aure a kirjinta tare da zama gaban dressing mirror ta fara shafa mai.

Tana cikin shafawa taji wayanta na ringing special ringing tone da ta sa don special man d'inta yasa ta gane me kiran seda ta ja ajinta tukun ta d'aga suka fara hira tana ci gaba da abinda take, tambayarta yayi me taje tayi nan ta gayamishi amma bata ce ga wacce ta sa ta ba, be ce komai ba don Amrah ta riga ta sanar mishi, sossai ya yabawa zuciya irin ta khairi da wata ce da se ta aibata pendonshi a gabanshi amma se ta dinga rufa musu asiri, hirar ta ne ya d'auke mishi hankali, inda take sanar dashi wai zasu koma gidan hajiya ruqayyah In ji ta achan za'ayi musu gyara na wata guda da ya saura, inda yake tambayarta karfe nawa zasu tafi tace mishi da dare driver ze kaisu.

Hakan ne ya hana musharraf kiran Afreen yaci mutuncinta, Ai ko da daren khairi da nuriyyah suka tafi da manyan akwatunansu, dada kam bata da abin cewa se godiya ga wannan bayin Allahn duk abinda tayi niyyan fad'a ko yi akansu kan ta aikata momma ta rigata, tunda tazo gidan bata komai se ci da kwanciya da kuma yawan zama da su Amrah a garden ko chan bayan boys quarters, shiyasa a duk sallollinta na farilla se ta sa mutanen nan a adu'a harda hajiya ruqayyah da ta d'auki nauyin kayan d'akin khairi gabad'aya ga na gyaran amare da zata musu.

A chan gidan kuwa hajiya ruqayyah part guda ta ware musu me komai da komai me d'akuna uku ta gayyato babbar me gyaran jikin nan Hajiya Jameela idrees daga chad don tayi mugun kwarewa a harkar se hajiya yasmeen Ahmad daga sudan duk dakuna d'ai d'ai ta saukesu se su khairi suka sauka a d'aya.

A ranar da suka zo a ranar aka fara musu abinda ya kawosu don manyan fridge d'in part din a cike suke da guzurin su hajiya yasmeen, da magungunan sanyi da infection suka fara, se gyaran fata wasa wasa kan sati biyu ya zagayo su khairi sunyi wani mugun chanzawa ga kamshi da ya mugun kama jikinsu ga wani d'an kiban da sukayi sukayi fresh dasu kaman d'anyen tomatos 🍅.

Toh su ci me kyau su sha me kyau ko abinda suke ci ma daban da wadda en gidan suke ci, su kwanta a Ac azo a dirje musu jiki da dilka a turarasu sama da kasa ko fita basa yi, yayinda soyayyarsu da musharraf kuwa ba'a magana kaman zasu kashe juna da love, har mamaki nuriyyah ke yi ba don ta san muryan hammanta ba da se ta karyata khairi akan irin soyayyar da suke zubawa.

Randa suka cika sati biyu a gidan a ranar momma ta fita takaba hakan yasa suka tarkata gabad'aya gidan zuwa gidansu harda hanan matar haidar da hafsa da suka saje suka zama kawaye matar haidar kam ma kusan da ita ake cinyewa da shanye kayan gyaran amaren, sossai momma tayi farin cikin ganinsu haka suna samun kulawa fiye da zatonta, ko su maryam da suma aka had'asu zuwa gidan uncle Ahamad don gyaran baza su nuna musu komai ba har ake wani kananan maganganu akan kaisu gidan hajiya ruqayyah da tayi, ta rasa me ke damun Rabi'ah wallahi har gwara zulai da dama ta san halinta ne.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Donde viven las historias. Descúbrelo ahora