Chapter sixteen

810 82 3
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





                  IGIYAR RAYUWA😭




                                            🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

            'Yar mutan Adamawa

*An kar'bo daga baban musa Allah ya yarda dashi yace: manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace "mumini ga mumini kaman gini ne saashi yana karfafa saashi" Bukhari ya rawaito*

Page➡️3️⃣0️⃣▶️3️⃣1️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Kusan mintuna 20 da gama wayansu yaji an turo kofa an shigo ko be d'ago ba ya san haidar ne, yana nan yadda yake d'azu a kwance rigingine banbancin kawai yanzu akwai taba a hannunshi yana zuka, haidar Abokinshi tun na yaranta Haka iyayensu mata da mazan abokanaine sanadin mahaifinshi momma ta san mahaifiyar haidar sede zumuncin iyayensu maza ya gama ta'bar'barewa ne sadda mahaifinshi ya shayar da su ruwan mamaki da har abada baza su manta ba, sati guda musharraf ya ba haidar banbancinsu kuwa haidar su biyu kawai iyayensu suka haifa daga shi se kanwanrshi Hafsa sa'ar miemie ita ma de tana jerin masu son Musharraf amma har ita be bata fuska ba duk kuwa yadda suke da yayanta.............

Haidar na da mata d'aya Islam da 'ya'yansu biyu Abdallah da Abubakar wadda ya ci sunan musharraf suna kiranshi Mu'allim, haidar sojan ruwa ne in an turashi aiki se yayi 5months,6 ko ma shekara kan ya waiwayo gida.............

Yana karasowa ya sa hannu ya fisge taban yana hararan musharraf yace "har yaushe? Baka san ba kyau ga lafiyarka ba? Me ya sa baza ka maida qur'ani abokin debe kawarka ba se taba abinda da kafi tsana" harara musharraf ya banka mishi yana cewa............

"Kaga kar ka fara daga zuwa? Ai ba gidanka na je nake sha ba a cikin gidana nake, d'an iskan banza kawai" yana maganan ne yana kokarin fisge taban shi daga hannun haidar da gudu haidar yayi kofa ya tsaya tare da danne taban a jikin gini a take ya mutu..........

"Me yasa zaka kashe min kayana? Ai naga ba haramun bane daga kai har momma kun sani gaba da maganan taban nan don ma na dena shan sauran kayan maye!!!" Kallonshi haidar ke yi cike da tausayawa ya san adu'a da tsantsar tsayawa ta mahaifiyarshi ya sa ya dena shan kayan maye da har so yayi ya zama addicted to drug Allah ya takaita musu............

A hankali yace "toh Lafiyar jikinka fah?" Tsaki musharraf yaja yana zama a bakin gadon yace "Afuwan doctor Haidar bazan kara ba" dariya haidar yayi ganin yadda musharraf din yayi magana kaman da gaske shi din doctor ne, girgiza kai kawai yayi tare da karasawa ya zauna ganganshi yace "naga kaman kana cikin damuwa lafiya kuwa?"...........

Ajiyar zuciya musharraf ya sauke a sanyaye yace "ba lafiya ba haidar wai fah aure momma ke son nayi nan da wata biyar kuma tsakaninta da Allah wannan karon, wallahi Ina cikin damuwa bayan duk abinda surrayah tayi min na kuma yarda da wata mace?............

Har na bata amanar kaina, 'yata, dukiyata da family na? Never haidar an shaa ni sau d'aya na kuma warke" haidar ya dube shi da damuwa "Musharraf se aka ce ma duk mata halinsu d'aya? Ka gwada ka gani in shaa Allahu Allah baze kara had'aka da irin surayyah ba, kuma na tabbatar kaima kanka kana da bukata, a yadda na sanka musharraf baza ka ta'ba zama har karshen rayuwanka ba mace ba sede In harkar zina zaka fad'a wadda bama fata, sannan ka dubi little tana da bukatar uwa kusa da ita ka kara duba lamarin ni de Ina bin bayan momma ko dole ne se mun maka d'an iska In ka ga dama ka tasata a gaba ka ta kallo kaman hoto"...........

Murmushi ne ya kubcewa musharraf haidar d'an iska ne komai seriousness dinka se ya kawo maka barkwanci kaman ba soja ba, "ni de ban shirya wani aure yanzu ba in ba so kuke mu koma gidan jiya ba" girgiza kai kawai haidar yayi sanin halin abokin nashi In ya kafe twankarashi se Allah se kuma momma.............

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now