Chapter fourty

996 78 0
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗




                IGIYAR RAYUWA😭




                                               🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, charity, honor and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

               'Yar mutan Adamawa

Page➡️7️⃣7️⃣▶️7️⃣8️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Tunda ya d'auki hanya ko juyawa be yi ba balle ya ga hawayen da yayi cha'ba cha'ba a fuskanta duk tunaninshi ya tafi ga mata masu kaiwa maza kansu a wannan zamani, mazan yanzu ba kai ka fara cewa kana sonsu ba ma ya aka kare bare, mazan yanzu da basu san darajar mace ba? Ya tabbatar d'ai d'ai ne za'a samu masu bin koyarwan manzo a zamantakewar aure he just take a glance at her a lokacin da ya sha kwanan gidansu waro ido yayi a d'an rud'e yace "qalbee!! What happened to yhu subhanallah are yhu sick? Ko nayi miki wani laifi ne?" Ya karasa yana danna horn na shiga gida.

Me makon tayi shiru se ta fashe da kuka harda shesheka, Amrah dake baya murmushi kawai ta sake ta san ba wani abu bane kishi ne kawai ke d'awainiya da ita, kuma da alamu ze lalla'ba kayanshi da farko ma damuwa tayi da auren hammanta da khairi sbd sanin halinshi amma yanzu zuciyarta fes ashe hamma an iya soyayya harda wani qalbee😅

Yana parking ta fice daga motan khairi ma shirin fita take taji ya riko hannunta cikin damuwa yace "menene ummu?" Cikin kuka tace "ba kai bane ka saurari wasu" waro ido yayi shikam ma be gane inda maganan ta dosa ba hakan yasa yace "ban fahimta ba" tura baki ta kuma yi cike da rigima tace "har hoto fah ka bari ta d'aukeka, har fa cewa take ko da malam se ta mallakeka, amma tana knocking glass ka bud'e" dariya ya saki cikin dariya yace "jealousy jealousy, dama duk kukan na kishi na ne? Alhamdulillah" kukan shugwa'ba ta kara sawa da sauri ya bar dariyan da yake yace "sorry, am sorry sweetheart bazan kara sauraren kowacce mace ba bayan ke da muharramaina In shaa Allah kinji?" Kai ta d'aga yace "oya fulfill your promise" rufe fuskanta tayi da kyawawan yatsunta hakan yasa ya kurawa yatsun ido na mintuna kan yasa hannu ya sauke ya rike su cikin hannunshi yace "wallahi qalbee kina sa ni surutu dayawa In yi ta magana ki ki cewa komai".

Yanzu dinma shiru tayi ya sake cewa "shikenan tunda baza ki min magana ba you can go" ya fad'a yana sake mata hannu ganin kaman ranshi ya baci yasa tace "Ohk sorry, zanyi magana" Shiru shima yayi tace "mi yid'i ma ha nder nberd'e am" tana karasawa ta fice da sauri tana murmushi, murmushi me sauti ya sake yana shafa kanshi zuwa kirjinshi a kan lips dinshi ya furta 'Alhamdulillah' ashe ze sake farin ciki a rayuwanshi? Cikin farin ciki ya fice ya shiga d'akinshi gobe da safe ze wuce hakan yasa ya d'an shirya abinda ze bukata.

Tana shiga parlorn ta samu duk ahalin gidan zaune su nabeel ne kad'ai basa nan suna islamiyya, har kasa ta duka tayiwa su momma da dada sannu da gida kan ta shige d'aki don yin wanka, a ranar da yamma suna zazzaune a parlor ana hira yayinda momma da hamma ke kallon news khairi kuma na tsaye daga wurin dining tana taya me aikinsu shirya abincin dare, su little suna game a waya amma basu sa volume ba, nuriyyah, Amrah da Miemie kam kowacce chatting take yayinda dada ke zaune shiru tana azkar.

Sanarwa aka farayi a tv wadda ya sa su maida hankalinsu gabad'aya akai "Abun al'ajabi wani hawan Allah ne wadda ada aka sanshi farin sani sbd yadda aka dama dashi sossai a siyasar kasarnan inda mukamin da ya rike daga karshe shine mukamin senator ba kowa bane se senator mahmoud Adam, ya mika kanshi ga hukuma akan abubuwan da yayi marasa kyau har gwara da alummah ma akan iyalanshi inda yace 'ya cutar dasu mafi munin cutarwa wadda baze fad'u ba amma yana rokonsu yafiya yayi hakan ne watakil ko zasu yarda da gaske ya tuba yabi Allah su taimaka In sunji labarin mutuwarshi su yafemishi haka iyayenshi su sashi a adu'ar su dan Allah duk san duniya ne da son zuciya se sharrin shaid'an ya ja mishi abinda ya aikata a garesu, yaci amanar aure yayi shaye shaye yayi cin hanci ba kad'an ba yayi zinace zinace.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now