Chapter fifteen

820 84 2
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗






IGIYAR RAYUWA😭




🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gureen

Wattpad:- Gureenjo

'Yar mutan Adamawa

Page➡️2️⃣8️⃣▶️2️⃣9️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Washegari

Misalin karfe 10 na safe jirginshi yayi landing a birnin gombe, bayan ya gama checking ya janyo brown medium size trolley d'inshi tafiya yake cikin izza da tsantsar takama daga nesa In ka hangeshi zaka san lallai gayen ma'abocin gym ne don yadda kayan da yasaka suka mugun fidda yanayin jikinshi................

sanye yake da farin long sleeve shirt masu buttons da black crazy jeans amma ba irin crazy me munin nan ba, rigan sossai ya kamashi ya 'balle buttons biyu na sama, kanshi da ya sha gyara se kyalli yake daga nesa, tun fitowanshi ya sheda motar mommanshi sede ya tamke fuskan nan tamau sbd ba ita bace yake hange...................

Da gudu zahra ta taho ta rumgume shi dukawa yayi ya d'aga ta sama yana juyi da ita duk hankalin en matan wurin ya karkata gareshi wasu na kallonshi da tsantsan burgewa wasu kuma na kallonshi da tsantsar so dariyan da yakeyiwa ershi ya mugun tafiya dasu, yana sauke zahra ya kama hannunta suka karaso jikin motan yana karewa Afreen dake tsaye jikin motan kallo...................

Sanye take da long sleeve peach color shirt me buttons kaman na maza ta kama kasan ta d'aureshi a cikinta har fari kal din vest dinta na bayyana, se straight skirt brown me tsagu har cinya se turban brown, seda ya kare mata kallo daga sama har kasa kan yaja tsiririn tsaki ya bud'e gaba ya shige ko sannu da zuwanta be amsa ba...................

A ranshi yake tunanin yanzu wannan ce ze aura? Gsky ya cire ta lissafi Allah yayishi me tsananin kishi shi kallon tsirara ma yake mata don ba maraba a fili ya saki tsaki, tunda suka gaisa da drivern momma be kara magana ba har suka isa gida ko gaisuwan Afreen d'in be amsa ba haka duk surutun da zahra keyi be tanka ta ba dama ta saba....................

Ana parking be jira komai ba ya sauka ya nufi main parlor yana ganin yadda Afreen ta bishi da ido kaman zata cinye shi, da gudu zahra ta zo ta rike hannunshi suka karasa tare, tare da barin Afreen da dakon akwati. "Salamu alaikum my momma I miss y............" maganan ne ya makale ganin Maryam, salima da Zainab baje a parlorn ko wacce taci ado kaman masu zuwa gasan kyau...............

Ba laifi dukkansu kuma kyawawa ne farare sossai irin farin gomben nan, amma duk cikinsu ba wacce ke da ki'ba ko dirin kirki, Zainab sanye da riga me had'e da wando na atampha ta cakara d'auri a gaban goshi tana zaune kan two seater hannunta rike da waya kirar iPhone X, se salima dake kwance kan doguwar kujera sanye da wando jeans pink da pink shirt d'an karami ba d'ankwali kanta se gashinta da ta raba gida biyu ta kamasu da manyan ribbons................

Se Maryam da yayiwa lakabi da er rawan kai ko ya ce mata kaza kanki da motsi tsaye gaban tv hannunta rike da remote tana chanza channel sanye take da straight gown da yabi jikinta ya fidda karamin shape dinta black hannunshi na vest, fuskanta kam mad'au yaji makeup kaman ba gobe se gashinta da tayi parking tsakiyar ka yana lilo....................

Ganinshi ya sasu tasowa da gudu kowacce na niyyar rungume shi, ganin da gaske fah suke yasa shi daka musu tsawa "what nonsense!!!!!" Birki ko wacce ta ja tana shagwa'be fuska, Zainab tace "sannu da zuwa sweet bro" a nyamutse yake kallonsu d'aya bayan d'aya akan salima ya tsaida idanunshi don a ganinshi ta fi su hankali yace "Ina momma?" A yangance cikin murmushi ganin duk cikinsu ita yayi wa magana tace "tana upstairs hamma" ba tare da ya tanka ba ya haura hannunshi rike da na zahra ya san ba me mishi wannan abu se momma yanzu ita momma cikin waennan taga matar aure?..................

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now