Chapter thirty two

912 78 1
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗






                  IGIYAR RAYUWA😭





                                               🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

               'Yar mutan Adamawa

Page➡️6️⃣1️⃣▶️6️⃣2️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

In kika ce tashin hankali kin rage a abinda na shiga ko ince muka shiga gabad'aya family, mamaji kaman baze rayu ba ko da suka yi niyyar tsinewa Mahmoud Bappa da diddi ne sukayi tsayin daka wajen hanasu inda suka nuna musu ko basu tsine mishi ba abinda de ya shukan nan shi ze gir'ba sun amince baza su tsinemai ba amma kar ya sake tako kafanshi inda suke har abada In kuwa yazo to tabbas tsinuwa ce tsakaninsu, ba yadda su hamma nasir basuyi ba ganin an ku'buto da musharraf amma abin yaci tura abinda yaso haukatar dani kenan..................

Dadda da ta tashi yimin fad'a har kaman zata bugeni akan yadda na boye rayuwar aurena, se kuma suka d'aurawa kansu laifin suna rayuwa with that guiltiness, khairi In nace miki na zauna na natsu karya nake yi, tunda aka kai musharraf prison ban kara bacci da dare ba, kullum a tsaye nake a gaban ubangiji abinci se anyi da gaske nake ci su miemie kam ma ko kallonsu bana yi dukda basu san me ake ciki ba wacce ta fahimta ma nuriyyah ce haka In Ina kuka zata zo ta sani a gaba muyi tare...................

Da nasiha da adu'o'i da komai aka samu na d'an sake har muke zuwa prison ziyartar musharraf randa na fara zuwa halin da na tadda musharraf ya kusa yin ajalina, a buge ba yadda yake rungume shi nayi ina kuka kaman raina ze fita hakan yasa shima fara hawaye, inda da kyar na samu yayi min magana ya tabbatar min tunda abin ya faru kuka ma be samu yi ba se yanzu, a sanyaye na ce "musharraf me ya kaika fara shaye shaye da hankali da iliminka?" A yanayi na marar hankali yace "Toh me kike so inyi momma? Anan fa zan kare rayuwana sanadiyar sharrin mahaifina, na san yaushe zan mutu? Na san iyakar shekarun da zanyi a duniya? Momma dan Allah ki barni kawai abin nan yana rage min damuwa kaman yadda na ciki suka fad'a"......................

Ina girgiza kai nace "Inaa musharraf ka fawallawa Allah lamuranka shine kad'ai me iya rage maka damuwa ba shaye shaye ba, musharraf ba tarbiyarka ba kenan amma ban ga laifinka ba duk na mahaifinka ne" yana kallona da idonshi da suka rine da kayan maye yace "Ina rokon ki abu biyu a duniya momma, ki kularmin da little sossai momma ki kuma kwantar da hankalinki wurin tarbiyar su nuri kar laifin ubansu ya shafesu, sannan abu na biyu shine dan girman Allah karki komawa auren mahmoud don Allah" Ina gyad'a kai nace "naji musharraf naji, zanyi duk abinda kace" ya kuma cewa "sannan alfarma nake so kiyi min na komawa gidana na nan garin da zama, ki kula da su little a wurin ki ci gaba da sana'anki"...............

Nan ma kai na gyad'a mishi yana baya baya yace "and kiyi hakuri ganina ze dinga d'aga miki hankali hakan yasa na yanke shawaran bazan kara fitowa ba daga yau, am sorry" Ina ta kiranshi amma ko waiwayowa be yi ba ya wuce su hamma ne suka kama ni muka tafi, haka na dinga zama da kewan d'ana da kyar na samu na shawo kan su diddi suka barni na dawo cikin gombe da zama, anan na ci gaba da business Ina ci gaba da kula da su miemie, a lokacin ne kuma su hajjiya ruqayya suka dawo gombe, sossai ita da mijinta sukayi mana jaje, se kuma daga lokacin kawancenmu yayi karfi....................

Kullum In naje prison musharraf baya fita haka kuma bana kin zuwa ko letter in bayar akai mishi, sannan mahaifinshi ban kara ganinshi ba, kowani karshen wata se su hamma nasir da Ahmad se sun turo mana kayan abinci da kuma kud'i haka taheer ma, a lokacin ma anyi auren Rabi'ah har ta haifi afreen................

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin