Chapter thirty

985 77 3
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





               IGIYAR RAYUWA😭





                                               🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

               'Yar mutan Adamawa

Page➡️5️⃣7️⃣▶️5️⃣8️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Ba irin tambayar da su dadda basu min ba ganin irin karewar da nayi kaman kud'in guxuri amma na ki fad'a musu shi ne ma yace musu Ai basu ga yadda nayi jiki ba farkon auren kawai yanzu cikin nan ne, ba yadda suka iya haka suka bar zancen ba wai don sun yarda ba, har kunyan shiga mutane nake ji don duk wadda ya ganni se ya tanka..................

A haka aka gama buki muka koma Abuja zama nake na hakuri da juriya har na haifi musharraf wadda tsananin rabo ne ya ajiye cikin, na shaa wahala sossai lokacin sbd nayi labour ba me taimakona da kyar na fito tsakar gidan, mai gadi na ganina yaje da gudu ya kira mahmoud seda ya 'bata lokaci sossai kan ya fito se juyi nake kaman bazan rayu ba, da ya fi to d'inma a kaina ya tsaya yana min kallon banza ganin zan iya mutuwa su dadda su tuhumeshi yasa ya d'aukeni ya wurga mota tare da figar motar zuwa asibiti......................

Naquda me wahala nayi kan na haifo shi a lokacin ya kira gida ya sanar musu inda mamaji ya bashi umarnin maza ya biyamin kud'in flight in koma gida kar ya yarda yace mota zanbi, ba don ya so ba Se don ba yadda ya iya haka ya biya yazo ya bani ticket a wulakance ko fuskan musharraf be gani ba, da kanshi ya kaini airport wai baya so inje inyi missing flight in ja mishi asara, bayan mun isa airport kan na fita a motar nace "baka mishi hud'uba ba" wata uwar harara ya zabga min a zafafe yace "baki da uba ne? Ke kar ki yarda, don't you dare try me a airport nan, bayan duk asaran kud'i da nayi da wadda zanyi dole In kun je gida se kin nemi kakaba min banzan d'ankin nan to wallahi ki kiyayi biyan bashi na".................

A hankali nace "ni de d'ana ba banza bane" waro ido yayi kan yayi wani yunkuri na fita daga motan da sauri, kwafa yayi tare da juya motarshi ya fice, trolley na naja rungume da d'a na da tambaya har na gane yadda ake komai a airport se kuma karance karance a haka har na shiga jirgi na zauna a sit d'ina da karanbani na d'aura belt don ban ta'ba ba................

A jirgin na taune dabinon dake jaka na na saka mishi a baki tare da zuba mishi ruwan zamzam, hud'uba nayi mishi da sunan baba na, don na gane baki da uban nan da yace min yana nufin kar In saka mishi sunan babanshi, bayan na isa hamma Nasir da matarshi Anty Aisha suka zo suka d'aukeni bamu ma shiga cikin gari ba muka wuce dukku, Anty Aisha rungume da musharraf, ni kuma Ina rike da marwan lokacin yana da kwana hamsin a duniya.....................

Bayan mun isa naga suna ta fiddo kayayyaki daga motansu anan na gane  sun yi min duk wani necessary sayyaya daga gombe, sossai su mamaji sukayi murnan ganin musharraf se tabarakallah masha Allah suke cewa, a part din dadda (mahaifiyar mahmoud) na sauka, ranan suna suka tambayeshi sunan yaro yace yana jin kunyan fad'a a tambayeni tsabar iya lauyanci, ba kunya nace "Da sunan bappa ya mishi hud'uba" don bazan bari mamaji ya sa sunanshi ba In je In shiga uku na ni kad'ai, sossai kuwa sukayi farin ciki da sunan, ranan suna mamaji ya bada shanu aka yanka, bappa kuma ya yanka mishi raguna biyu basu ma bi ta kan mahmoud ba da be zo ba be kuma kawo kudin rago ba sun ajiye hakan as kunya bayan kuma yi d'inne bazeyi ba............

Bayan kwana arba'in sossai nayi kyau nayi bulbulbul har bana so ace yau zan koma Abuja duk da sossai dadda ta fahimci be damu da ni da musharraf ba gashi tunda nazo bata ta'ba gani nayi waya da shi ba, randa na cika kwana arba'in na tafi gombe sati biyu kwarara nayi, sati na farko gidan yaya Nasir, kwana biyu gidan yaya Ahmad shima lokacin matarshi na da tsohon cikin sufyan..............

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now