Chapter fourty five

846 80 15
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗



              IGIYAR RAYUWA😭




                                            🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

              'Yar mutan Adamawa

Page➡️8️⃣7️⃣▶️8️⃣8️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Two weeks later

Rayuwa yaci gaba da tafiya wa khairi a birkice sbd bata san laifinta ba ake hukuntata hakan kuwa yafi komai mata ciwo musamman In ta tuna irin soyayyarsu me kashe zuciya da irin kulawar da yayi alkawarin nuna mata bayan aurensu amma gashi yanzu kwana goma sha biyu da samun Lafiyanshi.

Sunyi kwana biyu a gida tare da su momma kan ya shirya da niyyar komawa Abuja inda yace ze barta nan, nan fah momma da bata gane mishi ba kwata kwata a kwanankin tace be isa ba kaman yadda suka tsara da matarshi da little zasu tafi a sata a makaranta achan haka khairin ma results dinsu na fita ze nemar mata admission a chan.

A haka be so ba suka taho Abujan a maimakon jirgin da yayi niyyar bi ya fasa suka tafi a mota, tunda suka je a kwana goman da sukayi zatayi girki ta jera a dining amma ko kallon arean dining din baya yi, haka ze wuce sama dama d'akin kasa ya bata ya kuma ce kar ta kuskura ta hau mishi samanshi ko da bakin wasa.

Da little kad'ai yake d'an sakewa har ya ja ta saman wani lokacin har kwana takeyi amma khairi bata ta'ba hawa ba, yaron dake gyara mishi tun kan zuwanta shi ya ci gaba da gyara mishi abun na damunta ba kad'an kad'an ba amma ba yadda ta iya be bata fuskan tambayanshi laifinta ba bare ta kare kanta.

Kaman yau Bayan ta gama shirya little da sabon uniform d'inta na Hempstead da aka maida ta ta fara daga primary one, janta tayi zuwa kan dining tare da zuba mata irish and egg se tea da tayi musu ta fara ci ita kuma ta koma kitchen ta had'a mata lunchbox dinta, ta fito dashi ta ajiye a gefen jakanta dake d'aure saman dining se surutu take zuba mata amma da kyar take amsawa sbd yanzu magana ma na neman gagaranta, takun saukowanshi ta fara ji ko bata juyo ba kamshinshi da ya bule parlorn ya tabbatar mata da ya had'u yadda ya saba cikin suit dinshi na office.

A hankali ta juyo ta kalleshi aiko a shirye yake cikin 3 pieces suit d'inshi brown da farin shirt se brown necktie hannunshi rike da black brief case dinshi fuskan nan a matukar had'e kaman kullum tun dawowarsu maroon lips dinshi a cikin bakinshi yana d'an tsotsa ya karasa dining din gaban 'yarshi ya tsuguna yayinda ko matan bata ishe shi kallo ba.

Little tace "good morning paapi" yana d'an sake fuska yace "morning sweetheart how was your night?" Tace "fantastic paapi, mom tace kullum In zanyi bacci se nayi alwala In kuma yi adu'a shed'an baze zo kusa da ni ba and she's right I'm always sleeping good with no dreams and shetan around me".

Satan kallon khairi yayi se yaga kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta kallon seconds yayi mata ya fahimci raman da ya bayyana a jikinta fatanta da yayi wani irin kyau da yalki sbd gyaran da aka mata na buki se d'aukar ido yake lumshe ido yayi yana tuna laifinta ya gama yanke shawaran abinda ze yi kuma In shaa Allahu ze sanar da ita a yau ba se gobe ba, kallon little yayi yace "that's good but she's not your mom, your real mom is already gone".

Da sauri khairi ta kalleshi hawaye na cika idonta little tace "but paapi yhu told me that she's my mom and haka granny ta fad'amin that's why muke rayuwa gida d'aya a tare but meyasa yanzu zaka ce she's not?" Had'e rai yayi yace "na riga na fad'amiki am off to work" hanyar waje yayi khairi tabi bayanshi da sauri har seda suka fito kofan parlorn kan ta sha gabanshi dayake gidan ba daga kana fita bane zaka hango masu gadi, drivers da me bawa flowers ruwa kofan main parlorn a corner yake.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now