Chapter six

905 89 2
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





                IGIYAR RAYUWA😭





                                               🎗🎗🎗🎗🎗

Story & written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

      'Yar mutan Adamawa

Page➡️1️⃣1️⃣▶️1️⃣2️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Sun shigo gombe after 5 dukda a kishingid'e yake idonshi a lumshe amma chanjin iska da nishad'in da yake ji a cikin ranshi ya tabbatar mishi da sun shigo mahaifanshi tabbas a ko yaushe gida daban ne, a hankali ya bud'e idonshi tare da mikewa ya zauna da kyau yana kallon window sassanyan murmushi ne ya bayyana a fuskanshi har dimple d'inshi na gefen dama ya bayyana wadda ya sani kusa yar da biro na ashe yana dariya!! Murmushin ba karamin kyau yayi mishi ba sede kash ba kasafai yakeyi ba, yana ta kallon cikin garinsu har suka isa GRA layin shiru ba kaman cikin gari da suka baro ba, horn da driver d'inshi ya danna ne yasa shi maido da idanunshi kan ash ion get d'insu da sauri mai gadinsu ya fito yana ganin motan maigidansu ne yayi saurin komawa ya tura get din zuwa karshe inda motarsu ta kutsa zuwa katuwar haraban gidan dake d'auke da flowers masu kyau daga jikin gini inda sukayi har baya wurin boysquaters inda nan ne masu aikinsu suke wasu harda iyalai kuma shi ke ciyar dasu, Chan karshe garden ne mai kyau wadda ruwa ke bulbula yana kuma gudana, qasan haraban shimfid'e yake da interlocks masu kyau daga gefe madaidaicin part ne me parlor da d'aki d'aya se kitchen da store wadda ya kasance nashi yayinda parking lot ke facing part d'inshi cikinshi motoci ne guda uku na different companies, main house d'in kuma duplex ne da ya gaji da had'uwa steps uku daga kasa kan ka haura kan varender din dake shimfid'e da white tiles zuwa babban parlor dake a kasa wadda komanshi ke In Ash and milk se kitchen, store da toilets guda biyu se d'aki guda d'aya. Motansu na tsayuwa tsakar gidan Zarah ta fito da gudu tayi kanshi be gama fita ba ta rungume shi karamin murmushi yayi kan ya duka yasa hannu ya d'aga ta yana juyata se dariya takeyi ajiyeta yayi yasa hannu a sit din bayan ya d'auko brief case dinshi d'ayan hannun kuma ya riqe hannun 'yar shi cikin tsiririyar muryanta tace "I missed you paapi" yace "missed yhu too my little" nan ta fara zuba mishi surutu kananan murmushi kawai yake sakewa ba tare da ya amsa mata ba har suka shiga cikin parlorn ya so ya fara zuwa part dinshi yayi wanka amma baze iya ba se yaga momma d'inshi da ta kasance farin cikin rayuwanshi da sallama ya shiga parlorn inda momma dake zaune cikin shiga na alfarma ta mike fuskanta d'auke da murmushi tana welcoming nashi ajiye briefcase dinshi yayi tare da karasawa ya rungume ta tana murmushi ta ture shi tana cewa "kayya Musharraf se kace a india?" Murmushi yayi sossai tukun ya langwa'bar da kanshi gefe cikin shagwa'ba da yayi mugun kar'banshi yace "eww momma nayi missing naku ne fah" tace "muma munyi missing dinka sossai son" seda ta zauna tukun shima ya zauna a kasa tare da d'aura kanshi akan kafanta rigimar zarah ne ya ankarar dasu wanzuwar ta awurin duk ido suka maida kanta ta turo baki gaba tana bubbuga kafa a kasa cikin shagwa'ba tace "Paapi don kaga granny shine ka manta dani koo??" Yace "ohh sorry sweetheart zo abunki" karasawa tayi ta zauna daga kasa tare da kwanciya akan kafanshi, da yake ya riga ya d'aga kanshi daga kafan momma hakan yasa shi kallonta fuskanta fal murmushi a hankali yace "mun same ku lafiya momma?" Tace "lafiya klau Musharraf ya wurin aikin naku?" Yace "Alhamdulillah momma, Ina yaran nan?" Momma tace "nuri bata dawo daga wajen aiki ba yayinda Amrah ta raka miemie school tana da 4-6" d'an 'bata fuska yayi tukun yace "but duka motocin gidan nan suna waje why?" Momma tace "hmmm sun je sun karasar da man duka rankatakab yadda ba yadda za'ayi a fita dashi filling station Ina ta son in kira azo a sa tun safe se in sha'afa" 'bata fuska yayi sossai tukun yace "haba momma ya za'ayi a bar motocin gida duka ba mai fisabilillahi in wani urgent abu ya taso fa?" Murmushi tayi kawai sanin d'an nata yanzu wannan abu ya jawa duk 'yan matatan ta fad'a sam ta manta ne sbd hidiman dawowanshi amma da ko ita bazata so yazo ya same su haka ba, d'an shiru yayi don da gaske ranshi ya 'baci, kallon fuskan zarah yayi se yaga tayi bacci d'aga ta yayi ya sata a kafad'anshi tare da mikewa momma tace "kawota kaje dining abincinka na jiranka" yace "no momma lemme freshen up, zan tafi da ita In zan fito masjid se in tasota ta shigo" Kai momma ta gyad'a ya d'auki briefcase d'inshi ya fice, a tsakiyar gidan ya gamu da nuri murmushi shimfid'e a fuskanta tace "ya Musharraf san da zuwa, ya hanya?" Ba tare da ya saki fuska ba yace "yauwa Alhamdulillah" ya wuce ta yayi gaba abunshi da kallo ta bishi har ya shige part d'inshi baki ta ta'be, ta san yafi sake mata akan su Miemie amma bata san wa ya ta'bo shi ba daga dawowarshi ya fara cin ran nan nashi har ga Allah tausayi yake bata har ranta sbd ta san duk wani obstacles da ya shiga a rayuwanshi duk da wayonta ba har chan ba lokacin, da tunanin ta fad'a parlor bakinta d'auke da sallama. nayi mamakin ganinta me duhun fata a cikinsu, chocolate color ce ba kaman su da suke farare tas tas ba...

**
Abul be jima da kwanciya ba bacci ya kwashe shi a lokacin baban sulaimi ya shigo inda yace "Ina Abulkhairi yazo ya kaiwa babanku abinci a chargi office don na tambaya aka ce kaiwa ake yi" ajiyar zuciya khairi ta sauke kenan tun safe be ci komai ba? Tana jin Dada na amsawa baban sulaimin da "ya shige d'aki ba da jimawa ba, ummulkhairi tashi ki dubo shi" a sanyaye ummulkhairi ta tashi ta nufi d'akin nashi da sallama ta shiga ganin yana bacci yasa ta fitowa ta dubi baba tace "baba bacci yakeyi, mi andi o somi Un, ha mi wara mi yarana mo (na san duk a gajiye yake bari na zo na kai mishi)" kai Baban sulaimi ya gyad'a ya san dole ya gaji shi da be saba da irin wahalan nan ba duk da su ba masu hali bane amma babansu be bari suyi aikin wahala sam ko yayane gwara d'an d'inkin da yakeyi ma shima don Sana'a ne, duban khairi yayi ya san tana son zuwa taga mahaifinta ne baze hana ta ba se yace "toh bari na turo Ummu sulaimi ta raka ki" Kai khairi ta gyad'a shi kuma ya fice yana tausaya musu ya san In case ya fara daga wurin sarki toh se inda karfinshi ya kare ganin an kwatowa me hakki hakkinshi yana adu'ar gaskiya tayi halinta kar bayin Allahn nan su wahala akan abunda yake da tabbacin ba malam Umar bane ya aikata tuna abunda umman sulaimi ta fad'a mishi yayi shigowanshi Wai an hana su nabeel wasa a waje yau da maganganu se abin ya bashi mamaki ya kuma tokare mishi kirji a yadda malam Umar yake me kyautatawa mutane da makwabta shine don Allah ya jarabceshi 'yan unguwa zasu takurawa iyalanshi? Lallai ka guji duniya da mutanen cikinta da tunanin nan ya karasa cikin gidanshi inda ya samu sulaimi zaune ta zabga tagumi yanzu dawowanta makaranta ko uniform bata cire ba take jin abunda ke faruwa dama tana so In ta cire uniform se ta shiga taji me ya hana su Abul zuwa makaranta yau dayake makarantansu d'aya kuma yau bata jira su ba dama tare suke tafiya amma yau babanta yace ta wuce kawai sbd be da kud'in napep da ze bata kuma be so ya d'aurawa malam Umar d'awainiya bayan ga na yaranshi shiyasa tun da sassafe ta fice, seda babanta ya mata magana sau biyu kan ta dawo daga duniyan tunanin da ta fad'a yace "tashi sulaimi je ki raka khairi chargi office ta kaiwa Abbanku abinci" Da Toh ta amsa tana mikewa a sad'ad'e ta karasa d'aki ta shirya cikin doguwar rigan atampha tana cikin sa hijab taji sallaman khairi wani hawaye ne ya cika idonta tana jin tausayin kawartata da sauri ta share ta fito ta samesu da ummanta tana kara mata nasiha da kyar take iya kakalo murmushi tana ganin sulaimi ta mike tace "baba, umma se mun dawo" jerawa sukayi da sulaimi suka fice, da kyar sulaimi ta kakaro magana inda tayi mata jaje murmushi kawai khairi tayi ta san in tace zatayi maganan ba abunda ze hanata sake kuka akan hanya, tafiya suka dinga yi kurma kurma har suka iso jalingo devision da kyar aka barsu suka shiga inda suka tsaya daga baki bakin kofa wani d'an sanda ya tambayesu "wa kuka zo gani?" Tace "Malam Umar sanda" "au kice me babban laifi kukazo gani akwai ershi a nan?" Kai khairi ta gyad'a kanta na tsananin sarawa mutumin ze kara magana sulaimi tace "kayi hakuri Dan Allah abinci muka kawo mishi muna bashi kuma zamu wuce bata jin daadi ne" Kallon khairi yayi tukun ya ta'be baki ya nufi cikin cell yana cewa "toh a de kiyaye don ance kama tudinu tudan abinda kayi shi za'ayi maka ehe" basu tanka shi ba se chan ya fito da Abban ganin fuskanshi kawai yasa khairi fashewa da kuka sulaimi kuwa hawaye ya silalo mata, fuskanshi a kumbure tsaban dukan da akayi mishi duk don ya amsa laifin da ba shi ya aikata ba, da kyar ya samu courage d'in yi mata murmushi yace "yi shiru mamana karki damu jarabawata ce tazo a haka in shaa Allahu kuma zan cinyeta tare da karfafawanku gareni In ku kun kasa d'auka ni da nake ciki tsundum kuma ya zanyi? Uhm" da kyar ya samu khairi tayi shiru tare da mika mishi abincin ze d'auka kenan d'ayan police d'in da tunda suka shigo be yi magana ba yace "dakata!! Bud'e ki ci tukun ki bashi" bud'ewa tayi ta d'iba a spoon tare da kaiwa bakinta da kyar ta ci ta had'iye sbd kuna da ranta keyi Wai yau Abbanta ne anan wurin cikin wannan hali, bayan tayi spoon biyu se ta rufe ta mika mishi kar'ba yyi har sun juya yace "ummul" se ta juyo yace "ki sha maganin da na kar'bo miki daga kauyen Abbare n nan" Kai ta gyad'a mishi kan suka juya suka fice har suka iso gida ummulkhairi na hawaye kukanta ya Karu ne sadda suka shigo layin unguwansu tun daga bakin hanya ake zund'ensu har suka iso depon su idi shaid'an nan kam zaginsu sukayi tayi ba tare da wani shayi ba dukda ummulkhairi bata ga idi shed'an a wurin ba amma tayi mamakin wai yau 'yaranshi ne ke zaginta su da suke girmamata kaman itace ogan nasu ba idi ba, "khaih Allah ya isa mna hauwa Allah kayi mana sakayya" a fili ta furta hakan suna shiga cikin gidansu basu karasa shigewa ba ma khairi kam ta zube a wurin da sauri Abul da ke zaune ya taso yana ambaton "subhanallah kamata sulaimi mu karasa da ita".............






#vote
#share
#comment

'Yar mutan Adamawa

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now