Chapter twenty

880 79 2
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





              IGIYAR RAYUWA😭




                                           🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

            'Yar mutan Adamawa

*~~dedicated to MU KARU DA JUNA group, a gaskiya Ina jin daad'in comments d'inku, bani da abinda zan biyaku dashi tabbas ba don ku ba da na jima da dena rubutu, but yhu always support me kune karfin gwiwana thank yhu so very much for the care and support Allah ya bar kauna~~~*

Page➡️3️⃣8️⃣▶️3️⃣9️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Wata kyakyawar yarinya da baza ta wuce sa'ansu nabeel bace ta gani tsaye cikin shigan kananan kaya Jeans da pink tshirt, kanta kitson kalba masu kyau an sa mata beats, murmushi ta sakarwa khairin hakan ya sa khairin ma sakar mata murmushi............

"Hey cutie I'm fatima Abubakar Mahmoud but yhu can call me zahra or little, yhu are beautiful" murmushi kawai khairi tayi mata kan tayi magana taji ance "little wanene a kofan?" Matsawa little tayi khairi ta shiga tana karewa parlorn kallo, a kan three seater idonta ya fara sauka, kwance yake rigingine yana kallon sama, fuskanshi ta kalla idonshi lumshe fuskanshi jajazur musamman kumatu da kan hanci, kuma se gyaran murya yakeyi kaman me tsananin mura, kau da kai tayi tana sauke idonta akan momma dake zaune kan one seater tray d'aure akan cinyanta Da wani roba me kyau da tsabta tana yanka fruits...................

Murmushi ta sakarwa khairi dukda bata sheda ta ba da fara'a tace "sannu da zuwa lale" khairi tace "yauwa" tare da sulalewa kasa ta zauna tana karawa da "Ina yini?" Momma tace "Lafiya klau ya gidan naku?" Khairi tace "lafiya" se kuma tayi shiru, atishawar musharraf yafi biyar kan su gama d'an maganan nan hakan yasa hankalinta komawa kanshi a ranta tace bade taimakona da sukayin nan bane ya ja mishi mura haka don taga irunsu basuyi kama da masu shiga ruwa ba.................

Maganan momma ne ya katse ta daga tunanin da ta fad'a inda tace "sede kuma ban sheda ki ba" khairi tace "sabuwar me aikin da Maami ta turo daga Chan gidan su Hamma haidar" don haka taji hafsa na cewa, momma tace "ohh Ohk na gane dama ke ce? But kinyi karama da aiyukan nan zaki iya kuwa?" Cikin ladabi khairi tace "zan iya In shaa Allah hajiya" little dake zaune kasa kusa da khairi ta zura mata ido tace "momma baki tambayi name d'inta ba tana da kyau"................

Momma tace "aiko little, ya sunanki?" Khairi tace "ummulkhairi" momma tace "masha Allah, toh kinji little sunanta Anty ummulkhairi" little ta turo baki gaba tana kad'a kai tace "uhm uhm ni de cutie zan dinga kiranta Anty ummulkhairi yayi yawa" dariya momma da khairi sukayi, kai a kasa khairi tace "yaushe zan fara aikin hajiya? Kuma Ina rokon alfarmar Ina zuwa da safe in koma da yamma"..................

Momma tace "ki dinga kirana momma ohk? Sannan zuwa da dawowan nan ze yiwu? Dukda tsohuwar me aikinmu ma haka takeyi amma abubuwa dayawa se ni ce me yi shiyasa nake son samun wacce zata zauna da mu anan" little tayi tsulum tace "Ayyah ki dinga kwana cutie plz plz plzzzzz" khairi na murmushi tace "kiyi hakuri hajiya hakan baze yiwu ba sbd mahaifiyata na da lalurar ido bata gani kannena kuma sa'annin little pretty ne"......................

Little ta daka tsalle "yeeeeeeeyyyyy cutie am I that pretty???" Kai khairi ta gyad'a mata tana murmushi little zatayi magana kenan suka ji muryanshi da ke shake sbd muran da yakeyi yace "zahra!!!" A tare suka juyo se idonta ya fad'a cikin nashi saurin kau da kai tayi tana lumshe ido ta rasa wani irin abu ne wannan da in suka had'a ido kad'ai se taji wani iri daga yatsan kafanta har kanta ga bugawar zuciya da take fama dashi In har suka kasance cikin inuwa d'aya................

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now