🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
*this page goes to yhu sweet sis haneefa Muhammad Gurin, thanks for the support and care, yhu are such an angel dear I love yhu so much😘*
Page➡️2️⃣2️⃣▶️2️⃣3️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗Ganin yayi ta kiranta bata d'aga ba yasa yayi reporting a office be da lafiya ya tafi, tarkata komanshi yayi ya fice, ranshi a matukar 'bace wannan fushin da mommanshi tayi da shi duk baba yayi blaming sbd da be zo ba da hakan be faru ba, haushinshi yake ji har kashinshi............
Yau be taho da driver ba so da kanshi ya ja motan ya jefa ta titi, har ya isa gida ranshi tafasa takeyi ji yake kaman yayi tsuntsuwa ya ganshi gombe..........
***
Ita kam momma tunda sukayi haka da Musharraf ta ajiye wayan a parlorn ta haura sama, wanka tayi ta fito da alwala tare da gabatar da walaha, tana idarwa ta shafa mai tare da shiryawa cikin wata dakkakkiyar lace black and red tare da feshe jikinta da turarukanta masu sanyin kamshi..............
Saukowa tayi hankalinta gabad'aya se ya koma ga Musharraf ta sanshi sarai In har tayi fushi da shi toh be da natsuwa sam, seda ta shiga wanka tukun ta tuna da wayan da ta bari a parlor ta san yayi ta kira, tana shirin d'aga wayan ta duba kenan se mai aikinsu hanne ta shigo da sallama...........
Zama momma tayi tana amsa sallaman har kasa hanne ta du'ka ta gaida momman, momma tace "hanne me yasa yanzu baki son zuwa da wuri yanzu past 9 fah duk wanke wanken safe na tare kin san girkin safen ma kanki yake Ina yi ne kawai amma In Musharraf ya sani kema kin san sauran"..............
Hanne kanta a kasa tace "hajiya kiyi hakuri kwanan nan duk shirye shiryen buki na akeyi yau ne ma ake kawo lefe" cikin mamaki momma tace "shine ba sanarwa hanne? Yanzu yaushe ne d'aurin auren?" Hanne tace "nan da sati biyu kuma a kaltungo zamu zauna".........
Kai momma ta gyad'a tare da yi mata adu'an zaman lafiya, hanne ta mike ta wuce tana amsawa a zuciyarta, bayan wucewanta ne momma ta shiga tunanin inda zasu samu wata mai aiki me amana da gaskiya irin hanne ko ma fiye da ita............
"Yaaa salaam" ta furta tana me kara kallon fuskan wayanta 20 miss calls na Musharraf shi da baya kiran mutum fiye da sau biyu!!! Danna kiranshi tayi amma a kashe tayi ta nemanshi bata samu ba Haka ta zauna jugum cikin tunanin wani hali yake, ita ba da gaske take mishi ba ai ko maza sun kare ta gama zama da mutum irin Mahmoud amma da gaske ta yafe mishi duk laifin da yayi mata...........
******
A yau suke da nufin barin taraba state jakukkunan kayansu guda uku suka fitar sulaimi da khairi se kuka sukeyi haka dada da ummi 'maman sulaimi' ma zaman shekaru dayawa rana d'aya ace za'a rabu da ciwo kuma zaman amana sukayi...........
Haka suna ji suna gani suka rabu baba ne ya kira musu napep shata har roadblock inda ake hawa motocin tafiya, ba su kara minti biyu ba suka wuce, sienna suka samu se suka kama back seat gabad'aya wato guda uku, khairi, dada da Abul suka zauna a sit, Abul ya d'auki nabeel inda Khairi ta d'auki nabeela................
Awanni kusan 7 ya kaisu gombe daga cikin jalingo sbd rashin hanya sam hanyar ba kyau, tunda suka hau motan drivern yake saka wa'azi na malamai daban daban akan marayu, cin hakkinsu da hukuncin masu cin kud'i da gadonsu, sossai jama'ar motan suka natsu suka ji har suka isa.................
![](https://img.wattpad.com/cover/229264706-288-k522983.jpg)