Chapter fourty four

865 74 7
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





               IGIYAR RAYUWA😭



                                              🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

                  'Yar mutan Adamawa

Page➡️8️⃣5️⃣▶️8️⃣6️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Washegari bayan sunyi sallahn asuba inna ta shigo suka bude shafin hirar indo da dada, ta bata labarin lokacin da aka aurar da indon ita bata sani ba tayi aure anan cikin gombe zuwa billiri kawai tayi ta samu an aurar da kanwarta tayi bakin ciki sossai gashi iyayensu su biyu suka haifa, a lokacin ta haifi 'ya'yanta duka uku Muddasir, Muzzammil, da ruqayyah, bayan auren indon da shekara biyu Allah ya kar'bi ran iyayensu sanadin gobara yanzu en uwa ne kawai a 'billiri 'ya'yan muddasir bakwai yayinda muzzammil ke da shida dukkanninsu mata bibbiyu suke da se 'ya'yan ruqayyah biyu.

Misalin karfe takwas part d'in inna ya cika da jikokinta a lokacin ta saka dada da khairi sunyi wanka da breakfast duk wadda ya shigo zatayimishi bayanin dada da khairi kuma se aka ci sa'an basu da wulakanci kwata kwata familyn da murna suke taran su en matan suka ja khairi zuwa cikin gida duk da yadda take suku suku sbd bata san halin da musharraf yake ciki ba.

Suna zaune a d'akin en matan da ke part d'in uncle muddasir da suke cewa dad shima sun gaisa da khairi a lokacin da suke shigowa be santa ba kuma yaran basu fad'a mishi wacece ba, hira sukeyi amma gabad'aya hankalinta baya tare dasu su shidda ne en matan duk kuma sa'annin ta ne hafsat da taci sunan inna, Asiya, fatima, firdausi, Asma'au se hauwa, hira sukeyi kaman ba 'yan kishiyoyi kuma ubbanninsu daban daban ba hakan ya tabbatarwa khairi tarbiya da had'in kan dake gidan ganin taki sakewa se kawai suka koma hiran su ya sa su ci gaba da hiransu su ya su akan waliman da zasuyi na kammala secondary, wani karamin yaro ne ya shigo da gudu yana cewa "Adda Asma'u wai kizo inji Anty Ruqayyah" kan Asma'u ta mike khairi ta mike hauwa tace "har mun gama hiran kenan?" Khairi tace "A'a In na dawo zamu ci gaba, fita zamu yi da Maami" Firdausi tace "Toh se kun dawo" sauran ma suka ce se ta dawo da asma'u suka fice zuwa part d'in inna tana kara yi mata bayanin yaran gidan amma jinta kawai khairi ke yi bata fahimta.

Suna shiga ta duka har kasa ta gaida Maami cikin fara'a ta amsa tana tambayarta ya bakunta murmushi kawai tayi tana kallon hafsan maamin da suka rungume juna da Asma'u tana saketa itama tayi hugging dinta tana cewa "welcome to the family sis" murmushi kawai khairi tayi tare da zama kusa da inna, Maami ta kalli khairi tace "kinga nace zanzo 8 gashi har 8 ya wuce, tashi muje na cewa hajiya fatima Ina zuwa" mikewa khairi tayi da sauri dama da hijab a jikinta inna tace "er kusun uwa daad'i miji".

Kai ta dukar tana cewa "dada mun tafi" dada tace "ki gaisheshi da jiki ki kuma gaida mommanku" bata amsa ba sbd masifar inna se ma ficewa da tayi Maami ta bi bayanta tana cewa "se mun dawo" bayan fitansu Asma'u tace "yanzu inna khairi na da aure?" Inna tace "Eh mana ita kuma aka gayamiki kaman waenchan dalotayen yayyunkun nan ne da zasu ce se sun gama makarantar jami'a kan suyi aure, Toh da aurenta jiya da safe aka d'aura mata aure".

Asma'u tace "Kai inna tambaya fah d'aya na miki amma kin ban amsa uku, Toh me yasa ba'a kaita gidanta ba ta Kwana a gidan nan?" Hararanta inna tayi tace "ban sani ba" Hafsa tace "kyale innan nan muje zan fad'a miki" fita sukayi hafsa na mata bayanin abinda yasa ba'a kaita ba.

Da sallama hajiya ruqayyah ta tura d'akin asibitin khairi na biye da ita a baya momma ce kad'ai a d'akin tana zaune kan kujera shi kuma yana kwance sambal akan gado daga shi se dongon wando baki, fatanshi yayi fari sossai fuskanshi fayau idonshi a lumshe kaman me bacci amma sam ba baccin yake ba duniyar tunani ya fad'a me yayiwa ubangiji da ya tsinci kanshi a wannan rayuwa, da sauri kuma yayi istigfari ko ya yayi da idonshi hoton da aka turomishi yaki barin idonshi sam.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang