Chapter twenty eight

902 79 6
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





               IGIYAR RAYUWA😭






                                           🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

                 'Yar mutan Adamawa

*wannan page d'in naki ne Sadiya (Maman khalil) ina jin daad'in comments dinki sossai, irin sossai d'innan plz keep it up dear, Allah ya bar kauna*

Page➡️5️⃣4️⃣▶️5️⃣5️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Dube dube Amrah ta fara bayan fitanta Chan ta hange ta zaune kan wani dakali daga bayan d'akin ta zabga tagumi, karasawa tayi ta zare tagumin hakan yasa khairi d'agowa tana kallonta..........

Murmushi sukayiwa juna kan khairi ta d'an matsa Amrah ta zauna, bayan ta zauna tace "family sun cika d'akin" khairi tace "Ai kam duk ban san su ba gwara su Anty salima" Amrah tace "eh su da iyayensu ne, bari nayi miki bayani dalla dalla kan ki shigo daga ciki" hararanta khairi tayi tace "Toh wa ya gaya miki zan amince balle har in shigo daga cikin?" Amrah na dariya tace "har se an fad'a!! Lallai ni kam har na hango wani boyayyen sirri" waro ido khairi tayi tace "wani sirri?" Amrah ta fashe da dariya tana cewa "na san baza ki ki bane kawai amma ba wani sirri" a tsarge khairi ke kallon Amrah kar de har ta har'bo jirginta............

Ganin tana shirin tona asirin kanta yasa tayi saurin cewa "uhm Ina jinki suwaye da waye a d'akin?" Amrah tace "Duk waennan family da kika gani Alhaji Mahmoud dukku shine tushensu da shi da matarshi hajja marwa wadda yanzu duk sun rigamu gidan gaskiya, Allah ya bashi 'ya'ya guda biyu rak a duniya kuma duk maza da kakanmu ta wurin uwa da kakanmu ta wurin uba, Alhaji Adam wadda shine mahaifin Abbanmu se Alhaji Abubakar wadda shi ya haifi su momma.......................

Alhaji Abubakar da Alhaji Adam sun taso kaman en biyu sabida ba wani tazara bane tsakaninsu sannan komansu d'aya, da yake mahaifinsu sana'ar saida dabbobi yake hakan yasa suma suka tsunduma sana'ar mahaifin nasu inda sukayi shura a ciki har ya kai ga sunyi suna a dukku da ma gombe gabad'aya, a yawace yawancen da sukeyi na safarar dabbobi ne suka had'u da Aslamiyya da kanwarta shuwa a garin chad suma ya da kanwa ne iyayensu sun mutu sakamakon harin da aka kaiwa kauyensu...................

A wurin saida sauran dabbobinsu don tseratar da rayuwansu suka gamu inda Adam ya nemi su zo su koma tare don sossai ya tausaya musu jin labarinsu, tare suka dawo Nigeria inda hajja marwa ta tarbe su hannu biyu take basu kulawa sossai jin labarinsu haka Alhj Mahmoud ma duk wani kulawan da uba ze bawa d'anshi yana basu daidai gwargwado a lokacin Aslamiyya na da shekaru sha bakwai yayinda shuwa ke da shekaru sha biyu a duniya......................

Inda Adam ke da 26, Abubakar kuma 24 wasa wasa soyayya me tsanani ya shiga tsakanin Adam da Aslamiyya sossai Alhj mahmoud yaji daadin haka ba'a 'bata dogon lokaci ba akayi musu aure, anan cikin dukku suka gina gidan irin na zamani babban gida ne me part uku, Adam a d'aya Abubakar a d'aya In yayi aure se na tsakiyar na iyayensu, da kyar suka shawo kan Alhj mahmoud ya yarda suka koma gidan gabad'aya...................

Alhj mahmoud yaga ranar haihuwa sossai don a lokacin ba abinda yakeyi na aiki haka hajja marwa en aiki baja Baja, a hk suka ci gaba da rayuwa cikin tsantsar kwanciyan hankali don basu da wani damuwa, har Allah ya azurta Adam da samun d'a na farko, Alhaji Nasir shine wadda kika gani daga daman ya musharraf sanye da fararen kayan nan In kin lura duk ya fi su tsufa, bayan shekara biyu da haihuwarshi suka sake samun wani d'a namijin shine Alhj Ahmad shima yana nan ciki da sky blue shadda...............

Bayan haihuwan Ahmad ne hankalinsu Alhj mahmoud ya fara tashi akan rashin auren Abubakar yayi mishi magana ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, amma amsan d'aya ne a kara mishi lokaci, ba irin lokacin da bai d'ibar mai ba amma ba mata, da ya gaji kawai se ya had'a aurenshi da marwa a lokacin ta gama secondary anan cikin dukku.....................

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now