Chapter seven

926 84 3
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





                 IGIYAR  RAYUWA😭




                                             🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

              'Yar mutan Adamawa

Page➡️1️⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Cikin yanayin shi na Izza da kuzari ya shimfid'e zarah a gadonshi ya nufi wardrobe d'inshi yana cire kayan jikinshi seda ya saura daga shi se boxers tukun ya janyo light green towel ya yafa a kafad'arshi ya shige bayinshi dake manne da d'akin a gurguje yayi wanka ya fito sbd magrib daya gabato cikin light brown jallabiya a hankali ya haura gadon yana Dan bubbuga fuskan zarah kaman me tada wata babba, bud'e lumsassun idanunta tayi ta zubawa mahaifin nata murmushi ta sakar mishi tana mika, yana kallonta ya furta "Alhamdulillahillazi ahyana ba'ada ma amatana......" seda tayi murmushi tukun ta amsa da "wa ilaihin nushur"...................

"Oya wakeup magrib yayi" mikewa tayi yana rike da hannunta suka fito seda ya ga shiganta main house tukun ya fice masallaci da ba wani nisa ne dashi ba.......

Duk da yunwan da yake ji haka ya zauna se da akayi isha tukun ya fito dayake hakan ya kasance al'adarshi, ya d'an tsaya wurin mai gadi da driver d'insu ya tabbatar ba wani abinda ya faru kuma ba'a musu wani cin fuska duk da ya san momma baza ta ta'ba bari ba amma yana da kyau ya tabbatar d'in.......

Da sallama ya tura kofan parlorn, Amrah da Miemie na tsaye hannunsu cikin na juna da alamu fad'a sukeyi suna d'aura ido a kanshi se suka washe baki suka maida hannun kaman irin rike juna kawai sukayi tare da zamewa kasa suka zauna suka natsu idonshi dake kansu ya kawar ya maida kan nuri dake kunshe dariya harara ya sakar mata se ta gimtse baki Momma kam se dariyanta takeyi karasowa yayi ya zauna gefenta yana shafa cikinshi ta gane Sarai yunwa yake ji amma miskilancinshi baxe barshi ya fad'a ba...........

Kallonsu Amrah tayi tace "Auta ku tashi muje muyi dinner ya Musharraf na jin yunwa" d'an baki ya turo jin Momma tace mishi yaya, ba tare da ta kalleshi ba ta nufi dining tana murmushi suma mikewa sukayi suka isa Amrah tayi serving d'insu tana hararan miemie "Ina Little?" Kallon sama Mimie tayi tare da kwala kiran "Zaaarahhh" bata ajiye numfashi ba taji an daka mata tsawa "kee wani irin iskanci ne wannan?? Ko mu sa'anninki ne zaki zauna kina ma mutane ihu a kai come on kije d'akinta ki kirata".............

Sumui sumui ta tashi ta nufi stairs Amrah se dariya take a ranta don itama In ta sake dariyan ya fita fili za ta samu rabonta, tsab ta gama serving d'insu a lokacin zarah da Miemie sun fito zuwa dining d'in kowa yayi bismillah ya fara ci.........

Seda ya tabbatar kowa ya gama ci tukun ya fara aikawa su Miemie mugun kallo suna ganin haka suka san sunyi laifi duk suka dukar da kai yana nuna su ya fara magana "duk kanku Kun sanni kun kuma san abinda zan iya da wadda bazan iya ba, Wlh Wlh yarinya ta kara fita da mota ta karar da mai bata biya filling station ta sha mai ba tazo ta ajiye mota Wlh ranta in yayi dubu ze baci"...........

Be jira yaji amsan su ba ya mike yana cewa "good night Momma am exhausted" momma tace "Allah tashe mu lafiya" Zarah ta shagwa'be fuska tace "am sleeping with yhu paapi" girgiza kai yayi "no In kin bini baza ki barni na huta ba I know yhu" a sanyaye Tace "sleep tight paapi" yace "night sweetheart" su Amrah suka had'a baki wurin cewa "good night ya Musharraf" hannu kawai ya d'aga musu yana ficewa duk suka sauke ajiyar zuciya suka kalli juna tare da fashewa da dariya lokaci d'aya..........

*************

Da kyar Abul ya samu jikin 'yar uwannashi ya lafa abun tausayi don seda ya zubda hawaye, Sulaimi ce ta share hawayen idonta tana duban Abul tace "Abba yace a fara mata anfani da maganin da ya kar'bo a Abbare last week" Dada tace "Ina yace magungunan karfi garesu? Baza su matsa mata ba In ta fara anfani da?" ..............

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now