Chapter fourty three

923 75 12
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗




IGIYAR RAYUWA😭



🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

'Yar mutan Adamawa

Page➡️8️⃣3️⃣▶️8️⃣4️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Gida haidar ya nufa dashi ganin yadda jikinshi ke rawa hawaye kuma yaki dena gangara daga fuskanshi, be ta'ba tunanin shi rago ne ba se yau ya kasa zuciyarshi ya kasa aminta da abinda ya gani sede ga sheda, suna isowa ya fad'a d'akinshi tare da datsewa don be son kallon fuskan kowa daga bakin kofan ya tsuguna tare da cire hulanshi ya tusa hannu cikin gashin kanshi duk jijiyoyin jikinshi a tashe yau ba don yayiwa momma alkawarin baze kara shan abun maye ba da ya sha giya, tuna akwai taba a d'akin yasa ya nufi wardrobe ya d'auko tare da cire babbar riganshi ya jefar anan ya zube ya kunna taban se kuma ya kasa sha, jefarwa yayinda karfi yana me naushin iska toilet ya fad'a ya sakarwa kanshi shower ba tare da ya cire kayan jikinshi ba.

Ya kusan minti talatin tsaye a wurin zuciyarshi be yi sanyi ba ji yake kaman an saka zuciyar a tukubar tsire tsabar Azaban zafin da yake mishi, why? Why? Why khair yake ta nanatawa da kyar ya samu yayi wanka zazzafan zazza'bi na rufeshi sbd abinda ya dami zuciyarshi da kuma ruwan sanyin da ya zubawa kanshi na about 30 minutes, a bayin ya kwa'be kayanshi tare da fitowa d'aure da towel ya zube kan gado yana lullu'buwa jikinshi kaman wuta.

Cikin tashin hankali haidar ke ta zarya a kofan d'akin don bugawar duniya musharraf ya ki bud'e mishi about 2hours kenan da shigowarsu tare ya barshi don yana tunanin yana son samun space in ya ware se ya dawo yaji abinda ke faruwa, amma har anyi hotuna mutane duk sun watse an koma gombe don shiryawa dinner yanzu a gidan daga momma se su dadda da su uncle Ahmad, momma ma ta shirya zata wuce kenan ita da hajiya ruqayyah.

Da sauri haidar ya fita ya tare ta yana cewa "momma, maami akwai matsala" Da mamaki suke kallonshi a tare sukace "matsalan me? Ina musharraf?" Shiru yayi na mintuna kan ya fad'a musu abinda ke faruwa momma da tun d'azu take fad'an kin zuwan musharraf a d'auki hotuna kuma tayi ta kiran layinshi be d'aga ba, a rude tayi d'akin suka rufa mata baya itama maganan duniya musharraf be bud'e ba.

Su bappa ta kira a lokacin har hawaye ya fara zarya idanunta me musharraf ya gani haka? Da spare key din part d'in mamaji yazo lokacin duk waenda suka saura a gidan sun cika kofan, bud'ewa uncle Ahmad da ya kar'bi key din yayi a tare suka fad'a d'akin cikin wani hali suka samu musharraf da yasa momma kusan fad'uwa yana kwance ne kawai shi da gawa ba maraba kuka ta saka tana sulalewa kasa, dadda ce ta kamata haidar ya karasa da gudu ya ta'ba pulse dinshi yaji yana har'bawa a hankali ajiyar zuciya ya sauke yana cewa "he's alive we just need a doctor" uncle nasir yace "saka mishi kaya Aliyu se mu wuce cikin gombe kawai" nan suka fita dadda na rike da momma da ta kasa dena kuka se kace an ce mata musharraf din ya mutu.

Cikin lokaci kankani sukayi asibiti dashi inda suka bar mamaji, diddi da dadda a gidan, uncle Ahmad, uncle nasir, hajiya ruqayyah, bappa, momma se haidar ne suka wuce dashi, cikin hanzari akayi emergency dashi Doctor Aslam da wasu doctors din suka fad'a d'akin, sunanan zaune kusan hour uku a lokacin har magrib ya gabato doctors basu fito ba, uncle Ahmad ne ya d'aga waya ya kira marwan kai tsaye yace mishi "a fasa dinner din nan musharraf na asibiti ba lafiya" cikin damuwa yake tambayar me ya sameshi uncle Ahmad ya sanar dashi doctors basu fito ba har yanzu.

Abunka da gidan buki nan take maganan ya bazu ba dinner amma ance za'a kai amare gidansu a daren sbd musharraf ba lafiya shiyasa ba za ayi dinner ba, mutane dayawa sunji haushin hakan amma ya suka iya, khairi kwance a d'aki dada na zaune gefenta tana mata er nasiha da kad'an kad'an akan zaman aure don su se gobe zasu wuce Abuja a tsarin da sukayi tun farko don a Abuja aka shirya duk wani kayan d'akinta sbd musharraf be da wani gida anan part d'inshi kuma yayi karami amma In sun zo nan zasu dinga sauka.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now