🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Page➡️4️⃣8️⃣▶️4️⃣9️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗Ba irin rarrashin da Amrah bata mata ba amma ta kasa dena kuka gani take ta rasa aikin nan, aikin da dashi take taimakon kanta da en uwanta, aikin da ta sha wahala kan ta sameshi, rufin asirinsu kenan aikin nan, a hankali momma ta kira sunanta "ummulkhairi" d'agowa tayi tana kallonta ba tare da ta amsa ba tana jira taji ance ki tattara ya naki ya naki ki tafi kin gama aiki damu se ji tayi momma tace "Ashe baki yarda da kaddara ba?" Da sauri khairi tace "wallahi momma na yarda da kaddara me kyau ko marar kyau, ai bazan ta'ba zama cikakkiyar musulma ba se na kasance me yarda da kaddara"...................
Momma tace "good, toh me yasa kike kuka haka? Imani yana da hakika, hakikaninsa kuwa shine kaddara, Allah yana cewa a cikin suratul qamar "mun hallici komai da qaddara" ya kuma cewa a suratul A'ala "shine wadda yayi hallita, kuma shine ya daidaita ta, kuma shine wadda ya qaddara abubuwa, kuma ya shiryar dasu" ya kuma cewa a suratul Furqan "kuma ya hallici ko wani abu, kuma ya qaddara shi, qaddarawa" kiyi hakuri kiyi shiru da kukan nan dan Allah, ko basu ta'ba tashi bane se yau?"...............
Share hawayen fuskanta khairi tayi tace "na gode da tunatarwanki momma hakika na yarda da qaddara, da ban yarda dashi ba da ban kawo nan a rayuwata ba, na yarda qaddara ce ta sa na tankawa hauwa har idi yazo ya tadda mu ya d'auki hukunci, na yarda qaddarar abinda ke jikina yasa na murd'ewa Maman hauwa hannu har hakan ya fusatata ya kuma tunzurata ga ja mana sharri a idon duniya, qaddara shi ya d'auke min Abbana a sadda ban yi zato ba, ban ta'ba tsammanin zan iya rayuwa ba shi ba seda qaddara ya nuna min komai me yiwuwa ne...................
Qaddara shi ya rabani da d'an uwa na wadda muka rayu ciki d'aya mahaifa d'aya na watanni tara, muka fito duniya a tare muka kuma rayu a tare na shekaru 17, muka yi jimamin rashin mahaifinmu tare me makon ya barmu muyi wahalan rayuwa tare a wuri d'aya se ya d'auke mana shi, ya kaishi inda bamu sani ba" kuka ne yaci karfin ta, hannunta momma ta rike tana kallonta cike da tausayawa tabbas tun randa ta fara ganin khairi ta san tana cike da damuwa na wani abin...................
Wadda bata san ko menene ba, haka kawai take jin tsantsar tausayinta, za kuwa ta so jin wacece khairi, maganan khairin ne ya katse mata tunani inda take cewa "Ina kewarsu, Ina kewarsu sossai kuma Ina ganin ni ce sanadiyar komai da ya faru damu a rayuwa, na rasa yadda zanyi, na rasa wadda zan tunkara da damuwata, na rasa wadda zan kwanta a jikinshi inyi kuka iya yina be d'aga hankalinshi ba, Dada baza ta Jura ba, In har ta san ina cikin damuwa itama hankalinta baze ta'ba kwanciya ba, nayi iya kokarina don ganin na boye abinda ke ci na a rai amma abun na shirin fin karfina"...................
Momma tace "zaki iya ummulkhairi, dukda ban san wacece ke ba, na tabbatar bakiyi sanadiyar mahaifinki ba sbd yanayinki da tarbiyarki be nuna hakan ba, In ba zaki damu ba Ina so ki bani labarin rayuwanki, Ina son zama miki gini wadda zaki dafa ki tsaya har ki kai ga cimma nasara a rayuwanki" khairi tace "toh momma zan fad'a miki wacece ni, amma yanzu azahar yayi bari In munyi sallah" Da toh momma ta amsa kan ta mike ta haura, miemie ta zo ganganta ta dafa kafad'arta tare da bubbugawa kan ta wuce itama, Amrah ce ta taimaka mata ta mike sukayi d'akin khairin....................
Anan sukayi sallah tare, bayan sun idar sukayi adu'o'i suka shaafa Amrah tace "bari In debo miki abinci kici kan momma ta sauko" abincin taje ta d'ibo mata, bata wani ci mai yawa ba ta ture, da Amrah suka fito yayi daidai da saukowar momma, miemie, da nuriyyah, zama sukayi, momma a two seater, Miemie a kasa kan rug, don bata cika son zaman saman ba haka Allah yayi ta, se nuri da ta zauna a one seater..................