Chapter thirty Eight

950 83 9
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





               IGIYAR RAYUWA😭





                                              🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

Page➡️7️⃣3️⃣▶️7️⃣4️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Bayan kaman 40mins doctor Aslam ya fito yana kallon musharraf yace "muje office" bin bayanshi yayi zuwa office Bayan sun zauna yace "dr ya jikin nata?" Doctor yace "da sauki sossai tana bacci ne yanzu haka sbd alluran da aka mata" fuskanshi d'auke da damuwa yace "Amma ba yadda za'ayi a cire mata ciwon gabd'aya Ina nufin next month kar tayi haka?" Doctor Aslam yace "itama sistern ka ce?" Dayake Doctor Aslam ya san en gidansu gabad'aya, har ze ce er aiki se yaji bakinshi ya furta "wacce zan aura" murmushi dr yayi yace "masha Allah, ciwon mara na period pain ba yadda zamu yi mu cire mata se Allahn da ya d'aura mata, wasu matan suna denawa ne daga sun yi aure wasu kuma har se sun haihu yayinda wasu har abada, yanzu de mun yi mata allurai da karin ruwa ruwan na karewa zaku iya tafiya".

Godiya ya mishi tare da amsan bill d'insu ya fita, biya yaje yayi kan ya dawo d'akin da aka kwantar da ita dayake sun san en gidansu duk amenity ake kwantar da su hakan yasa da ya shigo da khairi aka bata amenity, a bakin gadon ya zauna yana kallon fuskanta da yayi fayau farinta ya fito sossai, baccinta ya mishi kyau sossai musamman yadda idonta da bakinta suka bud'e kad'an.

Seda ya gama morewa kallonta kan ya koma kan plastic chair ya kishingid'a tare da lumshe ido yana tuna randa sonta ya fara shiga zuciyarshi, be san taya ba be san ta Ina ba kuma be san yadda akayi ya karya alkawarin da ya d'aukarwa kanshi da zuciyarshi na hana kanshi son wata 'ya mace ba, be san yadda akayi ta kakkarya duk wani takunkumi da kwado da ya sawa zuciyarshi ba ta shige tun kallo na biyu da ya mata randa ake shirin keta mata haddi, tunda kuwa yaji labarinta se yaji kaman ninka mishi sonta da tausayinta akayi yana sonta har be san iya adadi ba.

Yana kaunarta da dukkan zuciyarshi, babban abinda yasa ta zama numfashinshi kuwa shine yadda take matukar son little tabbas duk wadda yaso little to shi ya so, abinda ya hanashi bud'e mata zuciyarshi kuwa shine yana tsoron sabarwa kanshi rayuwa da ita da soyayyar ta tazo tayi betraying d'inshi irin surrayah, gwara ya zauna be d'and'ani zakin soyayyarta ba zuwa ya gama yarda da ita 💯% karan wayanshi ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya fad'a a hankali ya bud'e idonshi dake lumshe ya sauke su akanta gashinta me taushin bala'i dake baje akan pillown da take don tuni tayi wulli da ribbon da kuma gyalen ta, wayanshi ya zaro daga pocket d'inshi yana kallon caller id d'in ganin "first love" yasa shi d'auka tare da karawa a kunne yace "hello" momma daga 'bangarenta tace "lafiya son naga baku iso ba har yanzu" idonshi na kanta yace "yarinyar nan ce ba lafiya tana FMC" momma tace "subhanallah me ke damunta haka?" Yace "period pain, ku taho yanzu am on my way too sbd flight d'ina 1 ne and yanzu 12".

Da Toh kawai momma ta amsa tana kashe wayan, mikewa yayi ya karasa bakin gadon yasa hannu ya mayar mata da gashin goshinta dake yawo a fuskanta, cameran wayanshi ya shiga yayi mata pics sossai kan yayi pecking goshinta ya juya kenan yaji an riko hannunshi a hankali ya juyo se yaga duk cikin bacci ne sabule hannunshi yayi ya juya ya fice cikin takunshin nan me sace zuciyar mata.

A parking lot yayi parking tare da fita straight wurin su momma dake shirin fita asibiti ya tsaya da ita da Amrah ganinsu ne yasa drivern tsayar da motan tare da sauke glass, momma tace "har ka dawo?" Kai ya gyad'a mata tace "Toh Allah ya tsare ya bada sa'a, a de dinga kiyayewa zamu yi waya kan ka tashi don na san ba asibitin zaka koma ba" kwa'be fuska yayi ya ki magana se kallonta da yakeyi.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now