Chapter twenty six

930 70 0
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗🎗





IGIYAR RAYUWA😭





🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

'Yar mutan Adamawa

Page➡️5️⃣0️⃣▶️5️⃣1️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Bayan fitansu bata koma cikin gidan ba se kawai ta wuce part d'in musharraf da sallama ta tura kofan, lumshe idanunta tayi tana shakan kamshinshi da ya amsa mata sallaman, ita kam Allah ya gani ba karamin so take yiwa turaren nan nashi ba, ba abinda ke tashi a parlorn se sanyin Ac had'e da na turarukan wuta da room freshener chakud'e da kamshinshi se ya had'u ya bada wani scent me daad'i na daban, karewa parlorn kallo tayi ba wani tarkace don sam ba cikan komai, daga set din kujerunshi se tv me had'e da stand se center table............................

Wucewa tayi cikin d'akin nan ma kamshin yake se ta dinga ji kaman yana kusa, nan ma ba wani tarkace se set na had'add'en Italian bed, a kan gadon ta hangi little kwance tana bacci kusa da ita taje ta zauna, duk da ita take kallo amma tunaninta da hankalinta sam baya jikinta, tunani take me mahaifinsu yayi musu me muni haka suka tsaneshi?...................

Tayi ta kokarin had'a bakin zaren cikin maganganunsu amma ta kasa, khaih ita kam a duniya bata ga me Abbanta ze mata da zata tsaneshi hakan nan ba, tsanan yayi yawa, ganin ta kasa gane komai se kawai tayiwa musharraf din adu'ar samun lafiya, tare da kutsawa tunanin abinda ya kutso kai rayuwanta, auren musharraf....................

Ita daga farko ma baza ta iya auren mutumin da ba soyayya tsakaninsu ba, ta tsani wulakanci taga kuma alamun shi kuma tambarinshi kenan, she can't just marry someone so mean like him, while personally she thinks he is rude, filthy and a complete scoundrel, ita gaskiya she wants to marry someone that will take good care of her family and her, love her and cherish her in front of everyone, amma zata iya watsawa momma kasa a ido kuwa? She saws so much hope a idanunta sadda take mata maganan auren d'an ta, and she's very sure in har suna wuri d'aya da momma baza ta ta'ba bari ya wulakantata ba...................

And she knows momma will take good care of her family wadda ita kanta baza ta iya ba sbd rashin kud'i, ita yanzu da wa zatayi shawara? Bazata iya cewa Amrah bata son d'an uwanta ba, sannan baza ta iya tunkaran dada da maganan nan ba sbd tana da tabbacin cewa she will be the first oppose to the marriage, don burinsu ita da Abba shine su aura mata ita da nabeela wadda suke so kuma yake sonsu tsakani da Allah ba don kud'i ko wani abu nashi ba................

In har shi musulmi ne kuma me wadatar zuci, mutum ta karshe kuma itace Maman hamdeeya wacce Haka kawai take jin bazata iya wannan zance da ita ba sbd wani zuciyar na fad'a mata zata iya gayawa mijinta shi kuma ya bata gur'batacciyar shawara sbd son da yake mata, baza ta so hakan ba sam wallahi................

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon little tace "wacce macece ta iya jurar zama da kai ASSIDDIQ har ta baka kyautar this beautiful damsel?" Shiru tayi don bata da me bata amsa, sulalewa tayi ta kwanta akan gadon tana lumshe ido tace "I've to know who are yhu before going into this"......................

**********

Ganin har bayan la'asar doctors din basu fito ba, kuma ruwa ya tsagaita yasa momma tace "muje muyi sallah" katse zaman jugum din sukayi da mikewa suka fice masallacin da ke cikin asibitin anan sukayi sallahn la'asar tukun suka dawo, agogo momma ta duba akallah awansu biyu kenan a ciki ba wadda ya fito, adu'a kawai ta dinga yi a ranta na Allah yasa yana lafiya....................

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now