Chapter fourty nine

963 76 5
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗



                  IGIYAR RAYUWA😭



                                              🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

                  'Yar mutan Adamawa

Page➡️9️⃣4️⃣▶️9️⃣5️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Har suka shigo gida uffan be ce mata ba kuma be sake fuska ba hakan yasa suna shiga d'aki tayi narai narai da fuska tare da kwanciya a gadon bayanshi ta zagaye cikinshi da hannunta duk biyu cikin taushin murya tace "am so sorry dear, plz Kayi hakuri bazan kara ba" lumshe ido yayi yana tunanin anya son yarinyar nan baze yi ajalinshi ba? Juyota yayi ya rike tafin hannunta yace "ni zan rokeki qalbee baki san yadda hawayenki suke da tsada da daraja ba? Zubar dasu kaman wani babban asara ne a gareni plz ki dauri ki dena irin wannan kukan it really hurt here wallahi" ya karasa yana nuna setin zuciyarshi.

Dukar da kai tayi tabbas maganganunshi sun shigeta kuma da yardar Allah bazata sake kuka a gabanshi ba tunda yana damunshi, tsintar muryarshi tayi yana cewa "baza kiyiwa assiddiq d'inki wannan alfarmar ba?" Dayake haka In ta bushi iska take kiranshi kuma sunan na mishi daad'i sossai kasancewar ba wadda ke kiranshi ko da Abubakar d'inshi ne bayan 'yan office d'insu.

Zagaye hannunta tayi ta wuyarshi ta kara tsai tayi brushing lips d'insu kan tace "In shaa Allahu bazan kara kuka haka ba baby" murmushi yayi yana cewa "Ohk baby amma fah kin tada wani fitinar" kashe mishi ido tayi tana jefanshi da wani irin murmushi da shi kad'ai ya san ma'anarshi bata hankara ba se ji kawai tayi ya rabata da kasa zuwa gado, a hankali na fita na ja musu kofa.

Washegari kuwa suka koma gidan Alhj Abdulrashid inda anan ya roki sanin su wanene su, ba tare da wani damuwa ba Abul ya zayyane mishi labarinsu wadda seda sukayi hawaye musamman Afreen da Nasreen da suka kasance masu raunin zuciya, irin kallon da musharraf ke wullo mata ne ya hanata kuka a wannan karon da ta tuna labarinta for the first time in history, bayan Abul ya gama ta basu labarin bayan barin Abul gidan har kawo yau, jinjina kai Abul yakeyi cike da farin ciki wai yau 'yar uwarshi ce tayi aure a garin Abuja tana jin daad'inta cike da soyayyar mijinta gashi tayi wani irin mugun kyau ta kara haske.

Nan musharraf ya roki alfarmar Abul yayi zamanshi dasu Abba In sun tashi komawa Gombe se su tafi gabad'aya suyiwa dada surprise, tambaya Abul yayi "yaushe ne tafiyankun hamma?" Musharraf yace "nan da three months" dukda Abul be so ba sbd kewan dadanshi da kannenshi da yakeji amma ba yadda ya iya musamman da yaji Abba na cewa "hakan shine daidai sbd ko ni zan samu nayi scheduling duk wani aiki nawa" haka suka tsayar kan kowannensu ya wuce abinda ze yi Afreen da Nasreen duk Nile university suke karatu amma different courses.

Bayan wata uku

Khairi ta samu nasarar kare exams d'in first semester cikin nasara don Allah yayita me kwakwalwa hakan yasa exams d'in be yi mata wahala ba, ta 'bangare d'aya kuma soyayyarsu da musharraf se kara gaba yake yi basu ta'ba ji sun gunduri juna ba, dukda zaman yau da kullum ana samun sa'bani amma daga d'aya ya hau d'aya ze sauka se wadda ya hau d'in ya sauko da kanshi tukun su fahimci juna, haka zumuncinsu da su Abba ya kara tsanani In ka gansu kaman wasu family yawanci 'yan matan suna gidan khairi hakan yasa Abul ma nan yake tarewa In Abba ya samu sarari da kanshi yake zuwa ya tattara su amma baze hana a washegari khairi ta gansu ba, little ma ta kare term d'inta itama ta saba sossai dasu Anty Nasreen d'inta, dukda khairi ta lura da take taken Afreen na son musharraf hakan be sa ta chanza mata ko a fuska ba don ta yarda da kanta ta tabbatar ita kad'ai ce a birnin zuciyar mijinta dukda shi musharraf d'in ba kowa ke ganin fuska a wurinshi ba halin shin nan na nan yadda yake treating su Amrah haka yake yiwa su Nasreen.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now