Chapter four

1K 94 3
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





IGIYAR RAYUWA😭



🎗🎗🎗🎗🎗

Story & Written by: fateemah Muhammad Gurin

'Yar mutan Adamawa

Page➡️7️⃣▶️8️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

A kullum mahaifiya itace jigo a kan ko wani hali d'a ze shiga tana tsayama d'a akan ko wani kaddara ze fuskanceshi tabbas ya yarda da kalman nan na 'behind every successful man their must be a woman' in ba don mahaifiyarshi ba be ta'ba tunani ko zato ze zo inda yake yanzu ba, ta tsaya tsayin daka akanshi da rayuwanshi, ya ginu ne bisa kalaman nan guda uku "hakuri, kaddara, jarabawa" ya ga jarabawa iya jarabawa amma da ya kasance me hakuri da yarda da kaddara se hakan ya zame mishi nasara a rayuwa..

Maganan momma ne ya dake shi da kalaman da ba sabo bane a gareshi ya saba jinsu kullum In har yana tare da ita ko ze yi waya da ita "babu hutu da kwanciyar hankali ga bawa a wannan rayuwa ta duniya sai yayi imani da kaddarar Allah, wato ya sakankance cewa duk abinda Allah ya qaddara mai aukuwa ne kuma abinda be so faruwansa ba to haqiqa ba zai faru ba, Allah ya rantse cewa hakuri Alheri ne ga masu yinsa a inda yake cewa 'kuma Lallai idan kukayi hakuri toh babu shakkah shine mafi alheri ga masu hakuri' Musharraf ka sani masu haquri ne kawai ake cikawa ladar su ba da lissafi ba, toh kai me yasa bazakayi haquri ka rungumi kaddaranka da jarabawar da Allah ya saukar maka a rayuwa ba? Shekaru Akallah 4 ba wasa bane sam kaki bari komai ya wuce a rayuwanka? Ya ci ace yanzu ka manta da duk wani rayuwan mu na baya, ka samu mace ta gari ka aura itace zata zama fitila me haske rayuwanka da ta jima cikin duhu, Ina maka adu'a a kullum randa na gaji kuwa sede kaji an d'aura maka aure na gaji da wannan halin naka" karyewa muryanta yayi alamun kuka na shirin kubce mata, idonshi dake runtse ya bud'e sunyi ja kaman an zuba mishi yaji yana jin tsananin ciwo da zafi a zuciyarshi cikin sanyin murya yace "kiyi hakuri momma" karamin murmushi tayi daga 'bangarenta tace "nayi Musharraf" ajiyar zuciya ya sauke shi de bayan mahaifiyarshi da 'yan uwanshi da suke ciki d'aya  se 'yarshi ba macen ko namijin da ze kara yarda dashi a duniyannan kuma har yanzu ta'bon zuciyarshi d'anye ne sam be shirya wani aure yanzu ba ko nan gaba sbd ya gama sarewa da al'amarin mata, "Allah ya maka albarka ya za'ba maka mata ta gari" a sanyaye yace "Ameen Ina su Miemie?" Tace "sun shiga school Amrah nada lectures so ta raka ta" "uhm" kawai yace sun d'an ta'ba hira tukun sukayi sallama yana jinshi wasai..........

***

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun" Da Abul ke ta nanatawa ne ya dawo da ummulkhairi daga suman tsayen da tayi, idonta ta kai inda dogarayen suke tare da polisawan da suka sama Abbanta ankwa, wayam taga wurin ba kowa alamun sun tafi dashi tana daskare a wurin wani irin kuka ta fashe dashi tana d'aura hannu akai a rud'e tayi hanyar kofa da gudu riketa Abul yayi hawaye na gangaro mishi fisfisgewa ta fara tana cewa "Abba! Abba!! Abbaaaaa!!!! D'an uwa sakeni sakeni kana ga zasu tafi da Abbanmu Wlh karya ce karya sukeyi Abba baze ta'ba aikata zina ba a rayuwanshi balle yayi wa wata 'ya mace fin karfi wacce irin shafin kaddara ce ta bud'e mana waiii hande 'yan boni(yau mun shiga uku)" ta karasa da wani irin kuka tana d'aura kanta kan kafad'an d'an uwanta shima hawaye kawai yakeyi yana tuna hukuncin fyad'e tabbas ya san Abbansu bazai aikata mummunan aikin nan ba amma ya san duniya da sharrin mutane ze sa a d'aureshi a matsayin mai laifi toh ma wacece yarinyar? Me shedansu? duk be sani ba, idonshi ne ya sauka akan Dada dake shirin fad'uwa da sauri ya saki khairi a guje yaje ya tare mahaifiyar tasu tare da d'aura kanta kan kafanshi yasa hannunshi kasan hancinta a firgice yace "er uwa dada.... dadaa bata numfashi" a guje khairi tayi wurin randa tare da d'ibo ruwa tazo ta zuba mata a fuska numfashi taja me karfi tare da sauke ajiyar zuciya se kuka tana maimaita "Allahuma Ajjirna fi musibatin, innalillahi wainna ilaihi rajiun" suma yaran kar'ba sukayi don su d'an samu natsuwa Ai kuwa maganan Allah se ga d'an natsuwa ya saukar musu khairi ta taya Abul suka d'aga Dada zuwa kan taburma suna ajiyeta Baban sulaimi na sallama a rude ya shigo yake tambayarsu wani labari ne yake ji a wajen nan khairi kam ta kasa magana se sabon kuka da ta 'barke dashi Abul ne ya samu ya mishi bayani, nan yace "Toh ai zama be kama mu ba, tashi maza Abulkhairi muje gidan sarkin muji wani chargi office aka kaishi" mikewa Abul yayi yana cewa "er uwa ki bar kukan nan haka ki kula da Dada" Kai ta gyad'a mishi suka fice inda Dada ke adu'ar Allah ya sa a samu nasara, bangaren Abba kuwa shock ya hana shi fahimtar me akeyi sam be san ya akayi tafiyar ba har suka iso Jalingo devision aka jefa shi cikin cell cikin hantara da bakar magana had'e da zagi, sam hankalinshi yaki dawowa jikinshi balle har yayi analyzing abunda yaji sunce, shi 'umar sanda' yayiwa wata fyad'e? Da sauri ya furta Auzubillahi minnashaid'anir rajeem wani irin dariya polisawa da masu laifi da suke cikin cell d'in suka fashe dashi na tsantsar shakiyanci wani yace "Da kake jin daadi a kan 'yar mutane baka San shed'an ba se da akayi ram dakai toh waye shed'an din anan In ba kai ba?" Suka kara shekewa da dariya hawaye ne ya silalowa malam Umar yana karanta duk adu'ar da tazo bakinshi don samun sauki daga mahaliccinshi.

Gidan sarki su Abul suka fara zuwa inda suka ga tsantasr wulakanci kafin aka fad'a musu police station din da aka kaishi ba 'bata lokaci suka fara tafiya tunda Nisan dake tsakani ba har chan bane, sun isa inda suka nemi ganawa da wadda case d'in ke hannunshi inda aka had'a su da police d'in bayan dogon wulakanci kai tsaye yace ya riga yayi filling case d'in za'a shiga court dashi on Monday su nemi lawyer kawai shine, sun nemi ganinshi ma an hana haka suka taho damuwa fal fuskan Abul tunani yakeyi ta inda ze fara tunda shine namiji babba a gidan shi ze d'auki duk wani nauyi yanzu a shekaranshi ta 17 ta Ina ze fara? Ya san 'yan uwan iyayenshi ba taimakonsu zasuyi ba sema dariya da karin wulakanci da tunanin nan suka isa gida a inda suka bar su khairi anan suka dawo suka samesu zaman akallah awa biyu zama suma sukayi inda khairi ke tambayar "ya akayi D'an uwa? Ba shi bane ko?" Hannu Abul yasa ya share hawayen fuskanshi yace "se adu'a kawai za'a shiga court ran Monday sunce mu nemi lawyer kawai" kuka Dada ta sa dama khairi kam hawayenta tun tuni basu tsaya ba, d'an nasiha baban sulaimi ya musu akan jarabawarshi kenan su ta mishi adu'a ze fito ne in shaa Allahu se da yaga sun d'an natsu tukun yace "yanzu ya kukega za'ayi da batun lauyan ni ba karfi gareni ba balle ince zan taimaka da wani abin" khairi tace "ba komai baba yanzu ma kayi mana abunda baza mu ta'ba mantawa da kai ba, ka riqe mu kaman en uwanka wadda 'yan uwanmun na jini suka kasa" hawaye ta share ta ci gaba da yake khairi nada zurfin tunani se ta kawo wani shawara "me ze hana mu sayar da gonan Abba muyi hayan lawyer?" Abul yace "baze yiwu ba er uwa gonan fa kenan da muke da se gidan nan muka sayar Ina zamu samu kudin abubuwan bukata?" Dada tace "sayarwan shine kawai mafita Allah ze dube mu, kai kana nan kana tunanin abubuwan bukata ina muka samu kwanciyar hankalin anfani da abubuwan bukatan bayan mahaifinka na tsare" Baban sulaimi yace "tabbas shawaran khairi shine abun anfani da, bari zanje In nemo mai saya Allah yasa kar su mana sayen wulakanci don sunga muna kan kafa" Ameen suka amsa gabad'ayansu ya mike har ya kai kofa ya juyo yace "Abulkhairi zo muje ayi komai a gabanka" mikewa Abul yayi ya bi shi daidai lokacin nabeel ya fito yana hamma da kaikaya ido yazo ya fad'i kan kafan khairi yana cewa "Adda khairi velo mi nanata(yunwa nakeji)" se lokacin ta tuna bata d'aura abun karyawa ba mikewa tayi tana cewa "wad'u munyal ha mi defa jotta d'o(yi hakuri bari inyi girki yanzun nan)" kitchen ta shige tana jin fitowan nabeela tana tambayar Dada me yasa yau ba'a tashe su sunje makaranta ba Dada ta ce mata, Abba ne baida lafiya karsu damu zasuje gobe, suka ci gaba da ma Dada tambayoyin 'yan jarida tun tana amsa musu har ta gaji ta kyale su. Farin shinkafa kawai khairi ta dafa ta soya musu mai ta had'awa nabeel da nabeelah se ta sawa Dada tare da d'aukawa ta fito musu dashi nabeelah ce ta kar'bi nasu suka zauna suka fara ci inda Khairi tayiwa Dada bismillah hannu Dada ta sa ta fara ci duk jiki a sanyaye jin bata ji khairi naci ba yasa tace "ummulkhairi me yasa bakya cin abinci?" Khairi da ta buga tagumi damuwa ya nuna sossai a fuskanta bata ma san dada nayi ba, seda Dada ta kara cewa "khairi! Khairi!!" A firgice tace "na'am dada kina bukatar wani abu ne?" Dada tace "ki sa hannu muci abinci, zamanki da yunwa bashine ze sa a sake mahaifinku ba adu'a shine kawai magani" Kai khairi ta gyad'a tare da sa hannu asanyaye ta fara ci bata wani ci sossai ba ta mike tare da d'age kwanon don dada ta dad'e da cire hannu ita dinma karfin hali ne kawai sbd kar yaranta su karasa karaya amma ita kad'ai ta san abunda takeji, su nabeel tayiwa wanka suna ta mata surutu ta kasa amsa musu har ta shirya su, nabeel ya fice wasa yayinda nabeelah ta zauna tana taya khairin lallice kwanonin da suka 'bata, suna gamawa khairi takai kitchen daga kitchen d'in ta fara jiyo kukan nabeel da sauri ta fita tana tambayrshi me ke faruwa yace "Adda ba kinga su Aisha ba naje muyi wasa wai uhm uhm mamanta ta hanata wasa damu wai Abbanmu yayiwa hauwa fyad'e kar wtkl nima halinshi nayi, Adda khairi me fyad'e?" Dafe gini khairi tayi jin wani irin hajijiya da ya d'auke ta juya ido ta fara don hana hawayen idonta zuba amma inaa kaman an bud'e fanfo maimaita innalillahi kawai takeyi don maganganun yaron sun girgizata yanzu har 'yan unguwan nan sun yarda Abbansu zai aikata fyad'e kuma da hauwa? Wait hauwa fah? Zamewa tayi ta zauna dirshan tare da sake kuka mai sauti........






#vote
#share
#comment



'Yar mutan Adamawa

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now