🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)Story and written by: fateemah Muhammad gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
Page➡️7️⃣1️⃣▶️7️⃣2️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗"What!!!" Exclaimed musharraf with a mouth open agape, kallonshi momma tayi da alamun gargad'i hakan yasa yaja bakinshi ya yi shiru, cikin sanyin murya momma tace "ko sbd me yasa mamaji?" Mamaji yace "duk cikin zuriyarmu bamu da wata ko wani me aljannu baza mu fara daga kanta ya zamana gaado ba, don mu yarda da aurensu ba danginta Ba komai bane sbd ko iyayenku a haka muka auro su".
Kai dadda ta dukar cike da kunya shap ta manta da su a ya aka auresu take kokarin aibanta wasu sbd rashin dangi, murmushi momma tayi me cike da manufa tace "Ai ko inde haka ne marwan baze iya auren Nuriyyah ba" da mamaki suke kallonta bappa ne ya iya cewa "ko sabi da me fatima?" Kai tsaye tace "sbd itama aljannun ne da ita, am sorry to say mamaji masu aljannun ba mutane bane? Ko akwai wadda ya ke d'aurawa bawa bayan Allah? Tuni ne kawai nake muku na san kun sani Allah ne ke qadarta wa bawa abu a yadda yaso, na boye muku nuriyyah na da aljannu ne sbd kwanciyar hankalinku.
Sbd In har kuka san dalilin samuwarsu a jikinta zaku ci gaba da d'aurawa kanku laifin komai ne" dadda tace "innalillahi wainna ilaihi rajiun, menene dalilin samuwarsun?" Musharraf yace "duk wani banzan aiki na ubanmu wadda ya shafi sihiri zuwa wurin boka don cin za'be, sun za'be ta ne sbd yafi sonta akan duk mu 'ya'yanshi a rayuwanshi" salati en parlorn suka d'auka dadda kam fashewa da kuka tayi tana Allah wadai da d'a irin mahmoud.
Mamaji ma shi kad'ai ya san halin da yake ciki, Bappa ne ya dinga musu nasiha cikin ilimi da fasaha ya nuna musu kar su karaya suce zasu tsine mai su ci gaba da adu'a shine ze taimaka mishi koda Hakki ze tashi kamashi ze zo mishi da sauki, da kyar mamaji ya nitsar da kanshi tare da mai da kwallan idonshi yace "tun yaushe take fama da su? Kun yi magani?" Momma tace "tun shekara d'aya da rabi da ya wuce, Musharraf ya taka rawan gani sossai akan maganninta I cannot ask the better for them bcos he's the best brother ever, ya tsaya sossai duk inda yaji wani malami ya kaita har abin yayi sauki ba kaman da da zatayi sati bata san waye kanta ba hallitarta duk se ya sauya ni kad'ai na san irin tashin hankalin da na shiga mah......" kuka ne ya kwacewa momma tuna irin wahalan da nuriyyah ta sha a tsakankanin kan tayi sauki.
Duk parlorn nuriyyah suka zuba wa ido cike da tausayawa hakan ya sata fashewa da kuka, duk yadda mamaji yayi kokarin maida hawayen idonshi hakan ya gagara se da suka zubo, bappa ma seda yayi hawaye yana godiya ga Allah da kaddarar ta, yana mata adu'ar samun aljannah sbd hakan don tayi matukar kokari wurin cinye jarrabawarta.
Musharraf da idonshi ke kan khairi ganin zata fara wani kukan yasa ya had'e rai ya zaro mata ido tare da girgiza kai, baki ta turo tana dukar da kanta a lokaci d'aya tana kokarin mayar da hawayen tunda yace baya so su zubo, maganan mamaji ne ya katse musu tunanukan da suka fad'a da kuma kukan da wasu daga cikin en matan ke yi, "Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka bani irin wannan d'a, Fatima, Musharraf, nuriyyah bani da bakin baku hakuri amma Ina neman wa kaina da matata yafiyar ku, sbd duk mu ne silar komai da bamu nemi Abubakar da maganan son had'a fatima da mahmoud ba da hakan be faru ba don Allah Ku yafe mana kar hakkinku ya hana mu kwanciyar kabari".
Momma tace "Wallahi ni ban rike ku ba mamaji na d'auke shi matsayin kaddara, da IGIYAR RAYUWA na baya kulle da na mahmoud da hakan bata faru ba, so ni kam na yafe muku" Nuriyyah tace "mamaji baka min komai ba ni kam wallahi na yafewa kowa amma banda Abba" Shiru duk sukayi suna jiran jin ta bakin musharraf amma gayen nan yayi shiru abinshi kaman be san dashi ake yi ba, kuma yaki kallon bangaren momma.
