🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad gurin
'Yar mutan Adamawa
Page➡️9️⃣▶️🔟
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗Wata kyakyawar yarinyace da baza ta wuce shekara hud'u ba an mata d'inkin atampha doguwar riga me kyau kaman ba yarinya ba, gashinta ya zubo har kumatunta ta gaba kasancewar kitson chuku da na gaba da aka mata an kawata shi da beets masu kyau, se tsalle take tana cewa "yes yes Anty Amrah, Anty Amrah" Kallon inda take kallo nayi se naga kyawawan 'yan mata na kokuwa a tsakiyar parlorn akan wani pink t-shirt dake hannun marar tsawon kuma tsiririyar wadda bazata wuce 17yrs ba wacce naji yarinyar tana kira da Anty Amrah se kokarin boyewa take yi a bayanta inda d'ayar da ta kasance doguwa kuma tafi Amrahn ki'ba bazata wuce 18 and half ba, ta samu nasarar fisgewa ihu yarinyar ta saka "yeeeeeeeeeaaahhh Anty miemie!!! Anty Miemie!!" Ci gaba sukayi da kokawarsu akan rigan yayinda yarinyar take ta tsalle tana kiran duk wadda rigan yazo hannunshi, kaman daga sama sukaji ance "Amrah, miemie wai wani irin banzan hali ne wannan? Wai se yaushe zaku girma ne?" Kanta na maida idanuna wow wata kyakyawar mata na gani da baza ta wuce shekaru 49 ba daga kallo d'aya na gane fulanin gombe ce sbd farinsu da ya nuna sossai a jikinta sanye take da atamphar holland riga da zani ta yafa gyale akan d'ankwalin dake kanta kafanta sanye da flat shoe, shagwa'be fuska yarinyar chan tayi tace "ohh no granny you spoiled the fun" zaro ido momma tayi tace "kaniyarki ne zarah, ku kuma sakarkaru daku a gaban 'yarku kuke wannan iskancin dama?" Shagwa'be fuska Amrah tayi wadda itace karama tace "momma ai Miemie ce da neman fad'a sabuwar rigar da Adda nuri ta sayo jiya na d'auka zan saka yau shine fah wai ta rigani se na bata" miemie tayi saurin cewa "karya takeyi momma na fa riga ta d'auka kuma anjima kad'an nake son sawa sbd Ina da lectures don taga na d'auka shine wai se na bata" momma tace "rufemin baki miemie ba kece babba ba? To maza bar mata rigan ita kuma nuriyyahn zata zo ta sameni zata saya muku abu guda d'aya baza ta ce na waye ba kuma baza ta ce ga wadda taba kyauta ba ta barni da raba fad'a" turo baki Miemie tayi tana kallon Amrah inda Amrah tayi mata gwalo a harzuke tace "momma ba kin ganta ba!!!" Momma tace "Auta kika sake mata gwalo se na kwace rigan na bata" sum sum sum Amrah ta haura stairs inda miemie tabi bayanta don zuwa shiryawa ten take da lectures, kasancewarta d'alibar jami'a na gombe state university inda Amrah ke gombe high school sss3, nurriyah kuma tana service d'inta a nan cikin gomben, zarah kuma tana nursery two itama Gombe high school take, kallon zarah momma tayi tace "Hey little zo kiji" ganin yadda zarahn ke tura baki yasa ta kirata, tana bubbuga kafa ta karaso ta kwanta akan cinyar momman, momma tayi murmushi kan tace "I have some good news" zarah tace "what is it?" Momma tace "your paapi is coming 2morrow" wani irin tsalle zarah ta daka tana ihun murna da gudu ta haura stairs don sanar da Aunties d'inta murmushi kawai momma tayi tare da maida hankalinta kan katon plasman dake aiki a parlorn ganin Bollywood ke aiki yasa ta d'auki remote don mayarwa sunnah tv..
parlor ne madaidaici a saman anyi furnishing dinshi da royals cushion masu tsananin kyau da tsada komai milk da gold ne a parlorn gefe karamin kitchen ne da basu anfani dashi amma akwai komai na bukata Chan gefen kitchen d'in kuma toilet ne babba me kyau, se wani corridor da a ciki d'akunan baccinsu yake, seda zarah ta isa kofar d'akinsu Amrah taja birki don tunowa da yadda suke nuna rashin jin daad'insu In aka ce Paapi d'inta ze zo, fasa shiga tayi ta juya zuwa room d'inta dake facing na su miemie yayinda na momma ke gefenta na nuriyyah kuma na gangan nasu miemie karshen corridor din kuma console ne had'add'e purple an jera wasu turarukan wuta masu kyau daga kasanshi socket ne wadda burner ke jone a jikinshi a kuma kunne yana fitar da hayaki me kamshi kad'an kad'an kasancewar a low aka saka ta, tana shiga ta fad'a kan gadonta tare da jawo wayanta iphone 6plus ta fara game (baki na rike tare da cewa shagali 'ya'yan masu akwai) ........