Chapter nineteen

769 77 2
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗






IGIYAR RAYUWA😭





🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad: Gureenjo

'Yar mutan Adamawa

Page➡️3️⃣6️⃣▶️3️⃣7️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Har kofan gida drivern ya kaita tayi mishi godiya sossai kan ta fice, da sallama ta shiga gidan hakan yasa Dada da ta zuba tagumi sauke nannauyar ajiyar zuciya tana zaune ne kan turmi dukda sanyin da garin ya d'auka ta tabbatar damuwar da mahaifiyarta ta shiga baze fad'u ba a hankali ta kira sunanta "ummulkhairi".......................

A raunane ta amsa sbd tuno abinda ya so faruwa da ita awanni kad'an da suka wuce tabbas da ya farun da bata san wani hali zasu shiga ba ita da waennan en uwa nata, hawayen fuskanta ta share tare da gyaran murya jin dadan ta fara magana cikin sanyi "khairi me ya ajiyeki a waje haka kin san ba magriba kukeyi a waje ba yanzu fah goma saura".................

Bata jira Cewar khairin ba ta kara da "lafiyanki ko? Ba wani abinda ya sameki? Wallahi tun fitanki gabana ke ta aikin fad'uwa" murmushi khairi tayi hawaye na kuma zuba mata ta karasa gaban dadan tana Jan er kujerar tsugunonsu ta zauna kan tace "lafiyata kalau dada kin ga ma albishirinki?" Dada tace "goro" khairi tace "Dada na samu aiki, matar ce ma ta riqeni ganin hadari se da ruwa ya tsaya tukun ta had'ani da drivern ta ya dawo dani gobe ma in shaa Allahu shi ze zo ya d'auke ni"...............

Ta karasa with so much excitement in her voice, ta boyewa mahaifiyarta ibtila'in da yaso afka mata, farin ciki sossai ya bayyana a fuskan dada a fili tace "Alhamdulillah, Alhamdulillah ya Allah ka ci gaba da rufamana asiri duniya da lahira ba don halinmu ba" cikin murmushi khairi tace "Ameen mamanmu, Ina su nabeel ne ban ji su ba" Dada tace "suna ciki sallah sukeyi tun d'azu suke jiran dawowarki da kyar na sasu yin magrib kin sansu da kafiya Toh isha dinma se yanzu suke mika ta".......................

Khairi ta gyd'a Kai ta kuma cewa "Allah ya sa ba abinda kuka ci don hajiya ta had'oni da abinci don naki ci a chan gidantan harda abu a leda ta ban kinga ko bud'ewa banyi ba" cikin jin daadi ba wai don abincin ba se don jin daadin khairi ta samu uwar d'aki me mutunci don a wannan zamani me mutuncin ne kawai ze iya maka haka, dada tace "aaa harda d'awainiya Toh Allah ya saka, ai ko an gode dama ba wani abinda muka d'aura".............

Khairi tana cikin bud'e coolers din su nabeel suka fito da gudu suna cewa "oyoyo Adda" fasa bud'e flask din khairi tayi tare da taran kannenta cikin murmushi tace "oyoyo chutu'ben dada" (chutu'be means en biyu da fulatanci) rungumesu tayi tana jin kewar kannenta bayan ta sakesu tace "Dada ya kamata mu koma ciki wajen nan akwai sauro ga sanyi".............

Komawa ciki sukayi Allah ya sa akwai wutan nepa tarwal a gidan bayan d'auke ruwa suka dawo dashi, plates khairi ta d'auko musu da serving spoon ta zo ta bud'e coolern fried rice ne had'add'e da pepper chicken se cowslow a gefe da yaji kwai, a lokacin In kaga fuskan waennan familyn zaka tabbatar suna cikin farin ciki saka musu tayi yadda ze ishe su sukayi bismillah suka fara ci a natse.................

Har suka gama ci ba wadda yayi magana a cikinsu daad'in abincin kam ya wuce misali, bayan sun koshi suka ajiye saura a kitchen kan nabeela ta dawo ma khairi ta bud'e ledan aiko designers abaya ne masu kyau guda biyu se turaruka arabian perfumes guda biyu, se kud'in da haidar ya basu 10 thousand...................

cikin jin dad'in karamcin maami da haidar khairin ta d'aurawa Dada kayan akan kafa tatta'bawa dada tayi tana sharara musu adu'a kan ta mayarwa khairi kayan khairi tace "Dada baza ki dau d'aya ba?" Dada tace "a'a ernan rabani ni kam Ina ni Ina kayanku na zamani balle ni da ya kamata in d'au nauyinku bayan kushewar mahaifinku se kece ke d'awainiya dani ni Ina nan bani da anfanin komai"..................

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now