Chapter twenty three

831 83 0
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗





                 IGIYAR RAYUWA😭





                                              🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

             'Yar mutan Adamawa

*wipe away the tears of the orphans in order to attain the pleasure of the most merciful and a house in paradise*

Page➡️4️⃣4️⃣▶️4️⃣5️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Washegari

Karfe bakwai da rabi dai dai yayiwa khairi a GRA, duk gidan ba wadda ya tashi bacci kasancewar weekend ne, d'akin da aka sauketa ciki ta shiga ta ajiye bag dinta, tare da komawa kitchen ta fara dube dube duk tunaninta ya tafi kan ko me zasu ci da safen? Tana d'aura hannunta kan kitchen island se taji paper an d'aura karamin robbern tumeric a kai d'auka tayi ta bud'e se taga an sa "kiyi pepper soup na kifi, za'aci da bread se kiyi tea but na soya beans" gyad'a kai tayi kaman a wurin aka bata umarni tare da fara aikin.................

Cikin lokaci kankani ta gama tare da shiryawa a dining ta koma kitchen ta wanke duk abinda ta 'bata, tana share kitchen din taji zuciyarta ya buga gabanta ya fara fad'uwa da sauri ta juya se kuwa idonta ya fad'a cikin nashi da sauri tayi kasa da kai tare da cewa "Ina kwana?" Kaman baze amsa ba se kuma yace "Lafiya" tare da ci gaba da tsayuwarshi.............

Juyawa tayi ta ci gaba da goge kan gas se kuma taga kaman hakan be kyautu ba se ta juyo tace cikin tsiririyar muryarta "ranka ya dade akwai abinda kake bukata ne?" Juya idonshi yayi tare da ta'be baki yace "just coffee" Kai ta gyad'a ya juya ya fita, coffeen ta had'a mishi tare da sa cup din kan karamin tray fari ta fita dashi a kan one seater ta Ganshi zaune se lokacin ta samu zarafin kallonshi da kyau sbd kanshi dake kan waya...............

Sanye yake da jallabiya coffee color me guntun hannu da ya matukar amsar fatan jikinshi, duk da be yi wanka ba amma kamshin shi duk ya cika parlorn, ganin ze d'ago yasa tayi saurin karasowa ta janyo center table ta ajiye mishi, ko kallonta be yi ba har ta juya ta fice, komawa tayi bakin aikinta Bayan ta gama goge gogen ta fice varender ta fara wanke mop din da tayi anfani dashi bata hankara ba taji an rungume ta, juyowa tayi ta d'aga ta sama "morning cutie" khairi na murmushi tace "morning pretty, ya kk?" Little tace "lafiya klau cutie Ina friends d'ina?" Khairi tace "sun je islamiyya, ke bakya zuwa ne?" Little tace "a gida malam ke zuwa ya mana da Anty miemie da Anty Amrah, ko wani weekend da yamma" kai khairi ta gyad'a tace "wa ya miki wanka?"...............

Little tace "momma tare muka sauko ma she's at the sitting room" khairi ta ajiyeta a kasa tare da kama hannunta suka fito, cikin ladabi ta gaida momma nan ta shaida mata ayyukan dake gabansu yau, da kai kawai khairi ta amsa, se misalin karfe goma su Amrah suka fita da, gabad'ayansu har little, da su salima.............

Ba sune suka dawo ba se azahar sayyaya kam sossai sukayi, a lokacin khairi ta jima da gama abincin rana har tayi donuts, naman ta ma yana wuta, da gudu little tayi kitchen da leda a hannunta "oyoyo cutie" khairi na murmushi tace "oyoyo kun dawo?" Little tace "yes cutie gashi na sayo miki tsarabar chocolate" khairi tace "aiko na gode" bata fiddo daga leda ba kawai lekawa tayi murmushi shimfid'e a fuskanta, bata kai ga magana ba taji momma na kiranta.................

Fitowa sukayi inda momma ta bata umarnin tattare kayayyakin kitchen ta kaisu wurin zamansu d'iban sayayyan ta fara da kad'an kad'an har ta gama, yau kam bata gama aikinta da wuri ba sam sbd ayyukan da suka mata yawa se bayan magrib ta gama goge kitchen a gurguje ta koma d'akin da yanzu ya zama nata duk da ba kwana takeyi a cikinshi ba, ta d'auko bag dinta ta fito...............

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Donde viven las historias. Descúbrelo ahora