Chapter Twenty one

858 79 2
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗🎗





                IGIYAR RAYUWA😭





                                             🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

              'Yar mutan Adamawa

Page➡️4️⃣0️⃣▶️4️⃣1️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Friday

Haka kawai khairi ta tsinci kanta cikin farin ciki da ta rasa dalili har take alaqanta hakan da aikin da zata fara ne wadda ta tabbatar da yardar Allah shine rufin asirinsu, da wuri ta tashi tayi musu breakfast tana sauke breakfast ta d'aura jollof don ya zama na rana tunda bata nan, tayiwa su nabeel wanka ta shirya su cikin uniform d'insu seda ta sa musu breakfast d'insu kan ta shiga wanka tana fitowa jollof d'inta yayi ta kwashe musu a karamin cooler d'insu ta kai d'aki ta ajiye................

Cikin A shape gown material ta shirya tana sa kayan tana tunanin d'an uwa don shi ya d'inka mata, sossai gown din ya mata kyau, ponytail style tayi parking gashinta da ta manta when last ya ga kitso black silky hijab da iya karshi cinya ta saka ta zura black robber silifas d'inta, wani paper bag ta samu ta zuba d'an abinda zata iya nema In taje Chan, fiskanta fayau ba komai ko d'igon baki d'aya baza ka gani ba haka jikinta ma................

Cikin sauri ganin bakwai da rabi tayiwa dada sallama, dada tace "Allah ya tsare ya kiyaye, ya kuma bada sa'a ki ci gaba da kula dan Allah, ki kuma rike mutuncinki kiji tsoron Allah a duk inda kike, sannan ki gujewa 'bacin ranki don kin san sakamako" a sanyaye khairi tace "In shaa Allah" ta kama hannun kannenta suka fice, napep ta tara musu don bata son suyi latti seda suka biya ta ajiye su kan ya wuce da ita GRA.................

Yana ajiyeta ta biyashi kud'in shi ta nufi gate din gidan gabanta na fad'uwa a kai a kai, knocking tayi malam d'ahe ya bud'e a mutunce suka gaisa inda yake tambayarta wurin wa ta zo ta sanar dashi itace sabuwar me aikin gidan, maraba yayi mata tare da bata hanya ta wuce, taku takeyi cikin salon tafiyanta da kaman tana tausayin kasa ta nufi main entrance na gidan a bakin kofa ta tsaya tare da knocking..................

Wata bakar buduruwa ta gani da ta san zata girme mata da shekaru masu yawa duk da baza ta haife ta ba, murmushi buduruwar ta sake mata Tace "sannu" da sauri khairi tace "Ina kwana" nuri tace "lafiya wurin momma kika zo?" Khairi tace "a'a ni ce sabuwar me aikin gidan" khairi ta d'auka zata ga nuri ta chanza fuska se taga ta fad'ad'a fara'arta Tace "Ohk sannu da zuwa bismillah"...............

Shiga khairi tayi cikin jin daad'i don bata ga alamun wulakanci a gida ba kwata kwata, a kasa ta samu wuri ta zauna tana gaida miemie da Maryam dake parlorn cikin fara'a miemie ta amsa ta yayinda ko kallo bata ishi maryam ba, nuri na kallon miemie tace "je ki kira mata momma" Miemie ta mike ta haura stairs ba jimawa se gata da momma, cikin fara'a tayiwa khairi sannu da zuwa khairi ta gaida ta, ta amsa tana tambayarta gida da mamanta, amsawa khairi tayi da "suna Lafiya Alhamdulillah" momma tana nuna khairi tace "ga fa sabuwar me aikinmu ummulkhairi sunanta"...................

Miemie ta d'aga mata hannu da murmushi itama ta mayar mata da murmushi, nuri tace "momma ina kika samu me aiki kyakyawa er fulani haka?" Momma tace "hajiya rukayya ce ta turomin ita wlh" Miemie tace "and she looks cool and innocent" momma na murmushi tace "ai itace little ke ta baku labari" wara ido miemie tayi tace "dama itace cutie? Ashe da gaskiyan little masha Allah"................

Maryam dake kallonsu da haushi da kuma mamaki ta ja tsaki, tare da mikewa ta haye sama da kallo suka bita kan miemie ta ta'be baki, momma tace "tashi ummu muje In nuna miki d'akin da zaki dinga ajiye abubuwanki" mikewa khairi tayi ta bi momma d'akin kasa dake daura da kitchen ta nuna mata ita kuma ta shige, tiles ne shimfid'e a kasan d'akin se babban katifa guda d'aya dake manne jikin inda window yake daga Chan gefe sallaya ce shimfid'e, se fanka dake ta aikin juyawa shikenan se toilet...............

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now