🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Page➡️4️⃣2️⃣▶️4️⃣3️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗"Mamana ta rasu" cikin tausayawa khairi tace "sorry pretty Allah yaji kanta" murmushi kawai little tayi, tana shafa cikinta tare da yin puppy face murmushi khairi tayi tace "Ohk mu je ki ci abinci" suna bud'e kofa ana bud'e na d'akin momma had'a ido sukayi da wata buduruwa da bata sani ba, wani kallon banza ta watsa mata a d'age tace "who the hell are yhu?" Kai a khairi ta kawar tace "house help" waro ido tayi tace "and yhu have the guts na hawan upstairs baki san maids basa hawa nan ba".............
Little tace "o'o Anty salima I invited her here, and momma ta sani" harara saliman ta watsa wa khairi kan ta wuce ta sauka, suma sauka sukayi ran khairi ba daadi tana tunanin su waye waennan en matan gwara ma salima ta d'anyi kama da mutanen gidan amma banda maryam kuma bata ji little ta kira sunansu a cikin mutanen gidan ba...........
Little na ganin Amrah zaune parlor tana cin abinci tace "Anty Amrah see the cutie I was telling you about" kallon khairi Amrah tayi tana murmushi tace "hi cutie" murmushi khairi tayi tana tabbatarwa kanta Lallai tayi sa'an gidan aiki don duk yaran momma bayan musharraf suna da tsananin kirki haka momman ma, Amrah na sa spoonful na abinci a bakinta tace "yhu cooked?" Kai khairi ta gyad'a waro ido Amrah tayi cikin sauri ta had'iye abincin tace "wow you cooked well Amma kinyi catering school a abroad ko?"...........
Dariya khairi da little sukayi yayinda salima ta ta'be baki ta ci gaba da danna wayan da takeyi, a fili tace "I don't think ko airport maid din nan ta ta'ba zuwa" Shiru Amrah tayi, little ta kuma rike hannun khairi tana kallonta, khairi na murmushi tace "thanks, bari In sakowa little" tare da nufan kitchen, Amrah tace "yana dining na fitar"............
Chan khairi taje ta sakowa little ta dawo parlorn a kasa kan rug ta zauna little ma tayi irin zamanta, a baki ta dinga bata har ta ce ta koshi Amrah na zaune gefe ta gama cin abincin tana kallo...........
Bayan ta gama bata ta had'a plate din Amrah da wadda little taci tayi kitchen ta had'a da kwanukan safe ta fara wankewa, biyota little tayi tana taya ta da surutu har ta gama ta share da towel me tsabta ta ajiyesu mazauninsu...........
D'akin da aka bata taje tayi alwala tayi sallahn azahar kan ta kwanta, wani bacci bacci take ji har ta fara lumshe ido taji an shigo, d'ago kai tayi se taga maryam ce tsaye tana yatsina tace "am not interested da abinda kika dafa, I want jollof na couscous with vegetable" bata jira Cewar khairi ba ta fice...........
Mikewa khairi tayi ta fito, kitchen ta shiga ta fara had'a mata dayake daidai na mutum d'aya ne in less than 30mins ta gama ta zuba a plate ta kawo mata parlorn a kan center table ta ajiye tare da jawo mata gabanta..........
Turo kofa taji anyi ko bata juya ba bugawar zuciyarta da kamshin turarenshi ya sanar da ita waye ne ya shigo runtse ido tayi don har ga Allah ita bata son encountering dashi, sallama kawai yayi maryam ta amsa, ya nufi dining.........
Kujera yaja ya zauna tare da fiddo waya ya fara dannawa ran nan a had'e har ta juya ta nufi d'akinta taji maryam tace "ruwan fah ko ni zan kawo wa kaina?" Fridge din dake gefen dining taje ta d'auki drinks d'aya da ruwa ta koma kitchen ta sa a tray ta d'aura cup tana fitowa taga maryam ta koma kan dining tana ta zuba duk da bata jin me take fad'a amma ta san da musharraf takeyi bayan ko d'ago kai be yi ba tun zaman ta balle ya tanka..............
![](https://img.wattpad.com/cover/229264706-288-k522983.jpg)