🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Page➡️5️⃣5️⃣▶️5️⃣6️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗Da kyar khairi ta sake bayan wasu lokuta amma ta kasa cin abinci sbd wani fitinanniyar kunyarshi da take ji abinka da fulani, shi kam ko a jikinshi se ma yawan satan kallonta da yake, da ya gaji ma kwanciya yayi abinshi yana facing inda take zaune tare da lumshe ido, a jikinta take jin ana kallonta amma ta rasa waye ne ta kalleshi yafi sau abinda yafi se taga idonshi a lumshe....................
Tana cikin sake saken yadda zata tambayi momma labarin rayuwanta da kuma kaddaran musharraf taji an turo kofan, murmushi me kyau ta saki tana mikewa tace "sannu da zuwa mamie" mamien haidar ce tazo tana matukar ganin daraja da girman matan, mamie ma na murmushi tace "yauwa sannu ummulkhairi" gaisawa sukayi cikin mutumci, su Amrah ma suka gaisheta ta amsa musu tana tambayansu school, kusa da momma taje ta zauna suka fara irin gaisuwarsu ta kawaye..................
Nuri ce ta shigo da sallama ganin mamie yasa ta duka har kasa ta gaida ta, amsawa tayi fuska d'auke da fara'a tace "ya service?" Nuri tace "Alhamdulillah mamie mun kusa kammalawa" mamie tace "toh Allah ya bada sa'a daughter" tace "Ameen" tana kallon momma tace "momma inaga ni kam zan koma gida" momma tace "Ohk ku tafi da khairi ma sbd abincin dare" khairi na mikewa tace "toh momma, se kun dawo Allah ya kara sauki" momma tace "Ameen" sallama tayiwa mamie.....................
Suka fice tana satan kallon gadon har lokacin idonshi a lumshe yake, bayan nuri ta bi tana mishi adu'ar samun lafiya, yinin ranan gabad'aya haka tayishi cikin wani yanayi da bata san na menene ba, a chan asibiti kuma bayan fitansu khairi momma ta mike tana cewa hajiya ruqayya "zo muyi wani magana" mikewa hajjiya ruqayyah tayi ta bita..............
Mota suka je bayan sun zauna hajjiya ruqayyah tace "menene aminiya da baza ki bari mu koma gida ba?" Momma tace "hmm Ina so inga komai ya tafi yadda nake so ne ruqayyah, matsalolin musharraf kara yawa suke bazan ta'ba iya barinshi ya kara wattani uku zuwa hud'u nan gaba ba mata ba sbd lafiyanshi" hajjiya ruqayyah tace "me ya faru?" Nan momma ta bata labarin duk abinda doctor ya fad'a, seda ta sauke ajiyar zuciya tukun tace "Ina mishi sha'awar auren ummulkhairi"........................
Waro ido hajja tayi tace "'yar aikin da na turamiki?" Momma tace "ita fa ko kina ga tana da wani aibu?" Hajjiya ruqayyah tace "a'a sam se hankali da tarbiyya da na lura tana da shi kawai de gani nake kaman musharraf be so mace me wayewa ba taya za'a yi yaso wadda ko primary bata dashi, dukda tana kyau da diri kam".................
Murmushi momma tayi tana tuna abinda ta gani d'azu tace "ze so ta ne, tana da hankalin da nake tunani ita ce kad'ai zata iya fiddashi daga halin da yake ciki gabad'aya, sannan tayi karatu zuwa ss2 In kinji turancinta ma zaki rantse private school tayi" hajjiya ruqayyah zatayi magana kenan momma ta fara bata labarin khairi tun daga na iyayenta har ita kanta, wlh se da hajjiya ruqayyah tayi hawaye.................
Cikin tausayawa tace "khaih duniya!! Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah mun gode da ni'imarka garemu" don wallahi labarin khairi imani ya kara mata, cikin tausayawa tace "ai ko na sami 'ya aminiya, na d'aukewa mahaifiyarta nauyin duk abinda uwa zatayiwa erta a bukin, sannan me ze hana In an tashi biyawa Amrah kud'in waec da zatayi nan da two weeks musharraf ya biyamata, don kin san yanzu karatu shine gatan kowa a duniyan nan"..................