Chapter fourty Eight

980 81 7
                                    

🎗🎗🎗🎗🎗



IGIYAR RAYUWA😭



🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

'Yar mutan Adamawa

Page➡️9️⃣2️⃣▶️9️⃣3️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

'Balle murfin motar tayi da sauri tayi d'ayan 'bangaren titin wani matashin saurayi dake tsaye a gaban wani mota dayake traffic ya tsaidasu, be ankara ba kawai se ji yayi an rungumeshi ta baya ko daga Ina, ko ya take, ko a wani hali take In har taga d'an uwanta ba ta gaba ba zata ganeshi.

Tana rungumeshi ta saki kuka da sauri musharraf ya dawo driver sit ya ja motan zuwa gefen hanya kan ya samu ya tsallaka zuwa bangaren da suke yana bawa mutanen da ta tara hakuri, har a lokacin taki sakeshi balle yaga waye se kiciniyar kwacewa yakeyi amma ta rike shi gam, seda musharraf yazo ya janye ta dukda haka taki sakin hannun d'an uwanta, wani babban mutum ne ya bud'e motar da d'an uwa ke tsaye a jiki ya fito dama traffic ne ya tsaidasu a natse yace "lafiya kuwa bayin Allah?" Abulkhairi da ya sawa khairi ido yana ta kallo ne ya juyo yace "Abba nima ban sani ba Haka kawai wannan tazo ta kamani tana kuka" mutumin ze yi magana kenan khairi data ke rike da hannun abulkhairi da d'ayan hannunta, musharraf ya rike d'ayan tace "Dan uwa!!!! Ni ce baka sani ba?" Se ta rushe da kuka.

Mutumin ya kalli musharraf da yayi wani iri sbd ganin yadda matarshi ke kuka yace "bawan Allah mu tsallaka se muyi magana don naga an kusa sake mu" tana rike da Abulkhairi dake ta mata wani irin kallo suka tsallaka mutumin yace "suna na Alhj Abdulrashid hameed ni babban d'an siyasa ne kuma d'an kasuwa, wannan d'ana ne sunanshi "Abdallah" dan Allah ko zaku iya min bayani yadda zan gane ku?".

Khairi tace "wallahi wannan sunanshi ba Abdallah ba, sunanshi Abulkhairi d'an uwa na ne, my twin brother that was lost decades ago, baka ga kaman mu ba?" Ajiyar zuciya mutumin ya sauke kan yace "Toh Alhamdulillah ga kama kam, maganan nan ba na kan titi bane in ba matsala ku bini gidana se muyi maganan cikin natsuwa" har musharraf yace "Toh Alhaji" Khairi tace "a'a baze yiwu ba sede ka bamu address zamu zo da dare sbd yarinyarmu ta taso school tuntuni gashi ba kowa a gidan" cike da wani irin so musharraf ke kallonta duk yadda ta matsu, duk yadda take marmarin ganin d'an uwanta amma sbd baza ta iya barin 'yarshi ita kad'ai ba ta hakura zasu koma gida se daga baya taje wajen d'an uwanta.

Ajiyar zuciya ya sauke kamin ya kalli Abdallah tabbas ba abinda ya banbanta shi da khairi sede kawai don ita mace ta fishi kyau, amma Toh ya akayi be ganeta ba? Kallon khairi yayi kallon d'aya ya gane tashin hankalin da take ciki kawai bata son nunawa ne amma damuwa ya bayyana sossai a fuskanta, maida dubanshi yayi wurin Alhj Abdulrashid yace "ba komai Alhj ka bamu address din after isha prayer zamu zo In shaa Allah" Address din ya basu suka mishi sallama akan se ya gansu idon khairi na kan Abdallah suka wuce shima kur ya mata da ido yana kallo.

Musharraf ne yaja motan hannunshi na cikin nata ba wadda ya iya cewa kowa komai a cikinsu har suka isa gida suka samu little kuwa ta dawo har ta ci abinci ta chanza kaya tana baccinta, samansu suka haura sukayi wanka a tare suka chanza kaya duk ta kasa magana suka kuma gangarowa abincin da tayi tun kan ta fita lectures tuwon semo da miyan d'anyen ku'bewa ta saka musu da zafinshi jau kaman yanzu aka sauke sbd yanayin warmern da ta saka.

Sbd yana bata yana ci hakan yasa ta ci sossai amma ba wai don tana da apatite ba, suna gamawa ana kiran magrib ya mike yayi mata pec tare da cewa "se na dawo" Kai kawai ta gyad'a mishi ya fice ita kuma ta tada little dake kwance kan kujera tace "tashi pretty magrib yayi" tashi tayi tana kaikaya ido tace "yaushe kuka dawo mommy?" Murmushi khairi tayi tace "kina shan baccinki muka dawo, oya an shiga sallah a masallaci tashi kiyi sallah In kin idar ki tabbatar kinyi bitar karatunki Ohk?" Tace "Ohk mommy" ta mike ta shige d'akinta inda khairi ta haura sama.

IGIYAR RAYUWA 🎗🎗Where stories live. Discover now